Zan Iya Auran Jikar Yayata?

*_ZAN IYA AURAN JIKAR YAYATA?_*

                         *Tambaya*
Assalamu Alaikum, Allah yasa Malam yana cikin koshin lafiya. Malam Ina neman a warware mun wata matsala ne, Akwai aure tsakanina da jikar yayata? Wato dani da kakar yarinyan mahaifinmu daya.


                            *Amsa*
Wa'alaiku mussalam, Babu aure a tsakaninku mutukar mahaifiyarku daya da kakarta, saboda aya ta (23) a suratun Nisa'i ta haramta auran 'yar 'yar'uwa wacce kuke uwa daya ko uba daya ko kuma shakikai.

'Yar 'yar'uwa a wannan ayar ta hada da Jikarta da jikar jikarta har zuwa can kasa kamar yadda malaman Fiqhu su ka yi karin bayani.

Don neman karin bayani duba babun NIKAH a Fiqhul Muyassar da tafsiran malamai ga aya ta (23) a Suratun Nisa'i.

Allah ne mafi Sani.

19/08/2017

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren *_📖MIFTAHUL ILMI📖_* (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren 🔑 _*MIFTAHUL ILMI*_🔑 a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07Thanks for your comment, please visit our website @ www.haiman.com.ng for more 036073248)* ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)