MU KYAKYATA SALLAR MU

MU KYAUTATA SALLARMU

Sallah itace ruhin addini kuma itace zuciya da tushin addini,itace gada da take bambamce tsakanin musulmi da kafiri,sallah itace farkon abinda za'a fara yin hisabi acikin aiyukan bawa aranar alqiyama,idan sallah tayi kyau to sauran aiyuka sun kubuta sun tsira.

Annabi SAW Yana cewa:
(Lallai mutum zai iyayin Sallah tsawon shekara Sittin,Amma Allah bai karbi Sallarsa,saboda rashin cikata, baya cika [kyautata] Ruku'insa da Sujadarsa acikin Sallah).
@Daga Abi Hurairata R.A,Albany yace Hadisine Mai Darajar Hasan acikin Saheehut Targhreb 529:

Manzon Allah SAW yaga wani mutum yana Sallah baya cika ruku'insa kuma yana gaggawa acikin Sujadarsa. sai Annabi SAW yace:
(Da wannan mutuman ya mutu yana irin wannan Sallar da yamutu akan Tafarkin da ba na Annabi SAW ba).
@Daga Amru bin Aas R.A,Albany yace Hadisine Hasan.acikin Littafinsa ;
ﺻﻼﺓ ﺍﻟﺘﺮﺍﻭﻳﺢ -ﺍﻟﺼﻔﺤﺔ ﺃﻭ ﺍﻟﺮﻗﻢ 118

Umar Bin Khaddab R.A yana cewa:
"Mutum zai tsofa har yayi furfura acikin musulunci amma Allah bai karbi koda raka'a gudaba na Sallarsa ba, sai akace masa sabodame? sai yace saboda baya ciki Ruku da Sujada acikin Sallarsa"....

Imam Shafi'i da Ahmad da Ishaq suna cewa:
"Duk wanda baya kyautata ruku'insa da Sujadarsa to Sallarsa batacciyace"....



Allah ka bamu ikon kyautata sallar mu.
Post a Comment (0)