UKU-BALA'I 47

UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI.
Abu kamar wasa Mariya zuciyarta da kwanyarta sai kuwwa suke mata mai sauti akan batutuwan Umma da Baseera sosai take jin lamarin ya fara samun karbuwa a gareta zuciyarta na ta kokarin bata dama tayi abin da suke bukata amma ta rasa ta yarda zata fara domin kuwa wani bangare na zuciyarta sai safa da marwa yake yi wajan yanke hukunci kan lamarin.
Numfashi ta ja kafun tayi shiru tana mai tallaɓe haɓarta kamar daga sama ta jiyo kuwwa daga waje da ihu shiru tayi tana sauraron kafun daga bisa ni tayi hanyar fita tsakar gidan Umma ta hango tsaye tana kallon ikon Allah Goggo Marka ce ta turmushe Hafsat sai faman jibga take yi kamar ta samu jaka daga ita sai dan fatari a kugu zanin ya fadi Mariya da take kallon ikon Allah bata san lokacin da dariya ta kusan kufce mata ba duban Umma tayi cikin yanayi na mamaki abin da tunda take a rayuwarta bata taba gani ba shine yau yake faruwa tabbas in da sauran numfashin ka a duniya kana DA SAURAN KALLO.
"Umma me ke faruwa ne hak...?".
Da sauri Umma ta daga mata hannu ba tare da tayi mata magana ba idanuwanta na kan Goggo Marka da ta zage sai jibgar Hafsat take yi kamar Allah ya aikota sai faman numfashi take ita kuwa Hafsat sai zunduma ihu take yi tana kokarin kwace kanta.
"Umma zata kashe fa bai kama ta ki bar ta tai ta dukan ta b...".
Sake daga mata hannu tayi a karo na biyu ta juyo ta dube ta fuskar ta da yanayin bacin rai sosai da sosai kafun ta hadiye wani yawu mai tauri mai nuna a wuya take.
"Yo meye na ki a ciki ta kashe ta mana wa tayi wa jikarta ce komai tayi mata wallahi ko a jikina".
Nan da nan Mariya tayi rau-rau da idanu tana duban Umma jin abin da tace.
"Haba mana Umma mai yasa zaki ce haka? kina kallo fa irin dukan da take yi mata bai kamata ba...".
"A wajan ki ne kike ganin bai kamata ba Mariya..tun dazu nake jin haniyar su ina zaune a nan daga cikin dakin su ban tanka ba sai da naji Goggo na zunduma mata zagi kamar wata wacce ta kirkiri maguzanci shine fa na tashi domin bata hakuri in laifi Hafsat tayi mata amma sai ta hada dani tana tsine min har da iyayena take anbata har tana cewa in har ni ba shegiya bace na fice na ba su waje".
Umma ta karashe tana dauke hawayen fuskarta da suke ta faman zuba kafun ta sake nisawa cike da bacin rai.
"ko ni shegiya ce wallahi dole in bar su in dai ina da zuciya balle kuma uwa da uba akwai su ban hanaki ba zaki iya zuwa ki cece ta domin 'yar uwarki ce ta jini amma ni kam wallahi a,a haram shan giya gidan liman".
Ta karashe tana karasawa wajan da take wankin kayanta ta cigaba da yi sai faman ajiyar zuciya take da wani irin yanayi na takaici zagin da Goggo tayi mata tun da take a rayuwarta ko kwatankwacinsa ba a taba yi mata ba.
Jikin Mariya yayi sanyi sosai tausayin Hafsat take sannan kuma maganganun da Umma ta faÉ—a mata suna ci mata zuciya sosai taji ranta ya baci tun da taga Umma na hawaye ta tabbata yau an kaita bango numfashi ta ja mai tattare da bacin rai kafun ta dubi Umma wacce take faman dirza kayan wankin kallo daya zakayi mata ka gane sauke haushinta take a jikin kayan da saurin Mariya ta isa gareta ta riko hannunta dago idanuwanta tayi wanda sukayi face-face da hawaye sun kaÉ—a sun yi jajir sosai hannu ta saka ta na goge mata su.
"Haba Umma me yasa kike zubda hawayenki akan Goggo ya kamata ki saba ba yau bane ta saba yi miki haka...".
"Na san ba yau bane amma abin da tayi mani yau na tabbata zai ji ma a zuciyata bai gogu ba duk abin da take yi mani ina hakuri amma yau HAKURINA ya kare ta kai ni bango amma ba komai Allah na nan ai zai yi mani sakayya".
Ta karashe tana rike hannun Mariya da take goge mata hawaye da su juyawa sukayi su duka suna kallon Goggo Marka wacce ta dago a wannan lokacin tana faman sakin numfashi kamar wacce tayi gudun faffalaki.
"Ni zaki tozarta ni zaki ciwa mutunci ni zaki kwancewa zani a kasuwa to wallahi ba ki isa ba kin yi kadan a yau din nan sai kin koma wajan uwarki ba za ki ja min abin kunya ba a gidan nan haka kawai ina zaman zama na zaki dauko mani ALAƘAƘAI ba garai babu dalili ban san hawa ba kawai sai naji sauka ai da sake wallahi ba a gidan nan ba".
Abin da Goggo Marka ta shiga fadi kenan tana faman haki kamar wacce Numfashinta ke gardama sai faman nuna Hafsat take yi wacce ke kwance idanuwanta sun kada sunyi jajir sai zubda ruwan hawaye suke yi tana faman nishi domin ta daku iya dakuwa
Duka ta sake kai mata cikin rashin tsammani ta doke mata baki lokaci guda ya fara zubda jini kafun ta shureta da kafa ta wuce bayan ta tsintsine mata tayi hanyar dakinta sai faman zage-zage take yi.
Su dai su Umma kasake sukayi gabadaya ta rikita su sun rasa mai Hafsat tayi mata har haka ta duke ta duka mai ansa sun duka haka ko barawo akayi wa wannan dukan sai ya san ya daku a hankali Mariya ta kalli Umma tana faman gyada kai kallon ta Umma tayi ta kau da kai don ta san abin da take nufi a hankali Mariya ta ja jiki zuwa in da Hafsat take bakinta sai zubda jini yake yi idanuwanta na zubda hawaye kallonta tayi kafun ta kau da kai jin zuciyar na tunano mata da kiyayyar da Hafsat ke mata tana jin wani iri da bacin rai amma haka ta daure kawai ta dago ta tana mai zare mata dankwalin kanta tana goge mata fuska da jinin dake zuba a jikinta.
"Sannu ko Hafsat me kika yi wa Goggo haka har take dukan ki abin da bai taba faruwa ba?".
Ta tambaye ta tana mikar da ita kan kafafuwanta ita kuma sai faman cizon laɓɓa take yi saboda tsananin ciwo da jikinta ya kama yi lokaci guda.
"Uban ki tayi min hegiya tsohuwar munafuka in baki sake ta kin bar wajan nan ba in na zo wallahi sai na hada dake".
Kamar daga sama suka tsinkayo muryar Goggo Marka na fadin haka da sauri Mariya ta ja baya tana mazurai.
"Shaggu na kurya masu gansa kuka a idanu ina ruwan ki da ita kinibabba me ya shafe ki da abin da tayi min in ban da kuturun kinibibi irin na ruwarki shine zaki zo kina tambayar ta".
Da hanzari ta ja jiki ta bar wajan tana kallon yarda Goggo Marka ke faman watsa mata banzan kallo kafun ta juya wajan Hafsat dake tsaye kikam.
"ke kuma zo ki shige tun kafun nazo wajan nan na karya miki shaggun kafafuwan nan naki bakar munafuka kawai".
Kikam tayi ko motsi ba tayi ba sai faman zunburo baki take yi gaba wanda ya fara tasawa.
"dake fa nake ko ki zo ki shige ko kuma ki fice daga cikin gidan nan".
A hankali ta fara dingisa kafar da tayi mata tsami sosai ta tunkari dakin tana zuwa Goggo Marka ta dungure mata kai tare da hankaÉ—a ta cikin daki kafun ta juyo ta dubi su Umma tana jan katon zaki.
"Tsofaffin munafukai kawai ta Allah ba taku ba".
Murmushin takaici Umma ta saki kafun ta ja hannun Mariya su shiga cikin dakin su rai a matukar bace.
*****
Tafe take kanta a kasa kamar wata maras gaskiya Hijab din ma sakko dashi tayi zuwa fuskarta yarda ba kowa yake gane waye ba hannunta rike da ledar kayan cefanar Cake a hankali take tafiya kamar wacce bata son taba kasa.
Kamar daga sama taji yo Horn din mota da sauri ta dago kai kafun ta shiga ja da baya duk a tunanin ta kan hanya take ake mata horn amma sai ta ga akasin haka motar a tsaye take gefe guda amma sai danna horn ake yi haka da ta gani ya sanyata tunanin ba da ita ake ba da saurin ta shiga waige-waige don ganin da wanda ake amma ba kowa a hanyar sai tsirarun mutane kuma kowa harkar gabansa yake yi koman da kanta kasa tayi ta cigaba da tafiya amma gabanta sai dokawa yake yi domin tunaninta ya bata da ita ake yi hakan ya sanyata kara saurin tafiyar da take yi daidai kwanar da zata shigar da ita kofar gidan su ta ga Motar ta shawo gabanta da gudu cikin tsananin firgici tayi gefe tare da sakin kara mai sautin kayan hannunta duk suka zube kasa don duk a tunanin ta markaÉ—e ta motar za tayi amma sai taga akasin haka buÉ—e idanuwanta tayi da suke runtse ta sauke akan motar ganin ana kokarin buÉ—ewa gabanta ne ya yanke ya fadi ganin waye a cikin motar yake kokarin fitowa haÉ—e fuska ta kare yi ta durkasa kasa tana hada kayanta gabanta sai dokawa yake yi da wani irin yanayi gabadaya jikinta bari yake yi lokaci guda idanuwanta suka kada sukayi jajir duk ta rikice kayan nata ta kasa hada su hannunta karkarwa yake yi kawai.
DaddaÉ—ar kamshin turare ne ya daki hancinta lokaci guda ta ja numfashi mai tsayi gami da runtse idanuwa sosai taji a jikinta kallonta yake yi a hankali taji ana ansar ledar dake hannunta cikin rashin kuzari ta saki ledar ba tare da wata gardama ba a hankali ya shiga tattare kayan ya ajje su gefe idanuwansa gabadaya ya sauke akanta yana kare mata kallo kafun lokaci guda ya ja numfashi mai tsayi zuciyarsa na mika shi wani mataki na daban mai cike da abubuwa muhimmai akan Mariya.
Mika hannu yayi kamar zai kamo nata hannun da sauri ta mike tana ja da baya idanuwanta cikin nashi suka sarke gabanta ya cigaba da bugawa a wani mataki wanda yake rikita mata tunanin gabadaya ta rikice sai faman rawar jiki take yi zuciyarta taji tana mikata wani sashi na daban mai kokarin canza mata duk wani tunaninta memorinta taji yana kokarin goge haddar da tayi runtse idanu tayi jin wani abu mai kama da kibiya mai tsanin haske ya kufto daga fuskar Dr.Karami mai tattare da lallausar murmushi ta tunkarota kafun lokaci guda ta buÉ—e idanun nata haske ya mamaye fuskarta wani numfashi ta ja mai karfi kamar zata shiÉ—e.
"Ban san me zan ce miki ba Mariya amma ki sani zuciyata tana matakin da take kokarin tarwatsewa da son ki na azabtu na wahalu lokaci mai tsayi wanda nayi tsammanin rayuwata ta kare ke nan duk a kan ki son ki Mariya sosai zuciyata ta kasa sarrafa kanta a dalilin sonki komai...komai nawa ya canza sosai da sosai duk dalilinki ki dube ni Mariya ni mai son ki ne so na hakika ki daure don Allah karki baiwa zuciyata kunya".
Wani irin dokawa zuciyarta tayi wanda har sautin ita kanta sai da ta ji ya bayyana idanuwanta a rufe jin ta take yi zuciyarta na mikata wani mataki da bata tajin taje ba sosai taji kamar kan gajimare take yawo maganganun Dr.Karami suka shiga sauti a cikin kwanyarta mai kara zuciyarta da ruhinta taji suna buɗewa da wani irin yanayi suna ansar sakon Dr.Ƙarami gabadaya taji komai nata kamar sabo komai ya goge sabbin abubuwa taji suna shigarta ta ko ina sake damke idanuwanta tayi kafun ta bude su ta sauke akan sa wani irin kwarjini da haifa take hangowa saman fuskarsa suna kara narkar mata da zuciya cikin wani mataki wanda ba zata iya sarrafa kanta ba.
Durkusawa tayi ta kamo hannayen ledan kayanta ta mike sosai kan kafafuwanta da taji suna lauyewa suna kokarin zubda ita kasa kokarin motsawa tayi tana ɗaga kafar guda daya da taji tayi mata nauyi sosai runtse idanu ta sake yi kafun ta tura laɓɓanta duka cikin baki a hankali ta shiga takawa idanuwanta na kara lumshewa gabadaya garin taga yana juya mata ji take yi kamar ba ita ba gani take yi kamar wata MARIYA ce ba ita ba tana ji yana kiran sunanta muryarsa na dakar mata zuciya da kwanya suna kara rikitata amma ta kasa katabus tafiya kawai take yi bugun zuciyarta na kara tsananta sosai a cikin wannan yanayin taji ta cikin soron gidan su lokacin guda ta karasa shiga ta zube tana mai jan wani numfashi mai tsayi dumin hawayen da suka zubo mata ya sanyata buɗe idanu a razane duk a tunanin ta ya biyo ta amma sai ta ga akasin haka bata goge hawayen ba illa wani kuka ta taji ya zo mata tun daga zuciya da ruhi da gangar jiki kukan take yi mara sauti sai faman shassheka take yi kamar wacce numfashin ta zai dauke...
*_KAMALA MINNA_*😘😘😘
Post a Comment (0)