UKU-BALA'I 57

UKU BALA'I
   NA.
    KAMALA MINNA.

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
  BABI NA HAMSIN DA BAKWAI.
Takure take waje daya sai fama rusar kuka take yi idanuwan nan nata sunyi luhu-luhu kamar wacce aka watsawa barkono zuciyarta take ji tana zafi gami da raɗaɗi wai ita ce Huzaif yayi wa haka mutumin da ta baiwa duk yardarta da kaunar ta ta mika masa duk wata ragama ta rayuwarta ta amince dashi ta yarda dashi amma yau ita ce yake daga hannu yana mari yana kiran ta jahila mahaukaciya kaicon wannan rayuwar.
Kuka ta sake rushewa dashi tana dukan cikin ta kamar wata sabuwar hauka Goggo ce tashigo a daidai wannan lokacin ganin abin da take yi ya sanya ta kurma ihu ta isa gareta tana rirrike ta.
 "Haba Hafsatu kalau kike kuwa me ye haka kikayi?".
 "Goggo ki bar ni kam ki kyale ni wai ni Huzaif zai ciwa mutunci har da duka akan layi akan gaskiya".
 "Kiyi shiru nace miki ki kyale shi wallahi Allah sai ya gane bashi da wayo sai ya shaki bakin ciki kamar yarda ya shaka miki...".
 Abulle ta dago labulan dakin ta shigo fuskarta da wani murmushi wanda yafi kuka ciwo hannu ta harɗe a kirjin ta sai da ta kare musu kallo kafun ta nisa zuciyarta na kara suya.
 "ai in har mutum yace son zuciya zai biyewa to tabbas yana tare da tsintar kan sa cikin takaicin rayuwa Goggo da ma kin dai cewa zaku dauki mataki ai aikin gama ya rigaya ya gama mai yayi saura sai ta zauna a yarda take so ba dai haka ta zabawa rayuwarta ba ita ba wanda ya isa yayi mata magana ta dauke shi mutumin kirki ita sai dai ta zauna tayi son ranta to ai gashi nan ta gani a kwanon ta ba zan yi miki baki ba Hafsat amma za ki ji a jikinki da kuma duniyar rayuwarki ai duk wanda ya dama haka zai sha".
Rushewa da kuka Hafsat ta sake yi tana rike kanta da take jin yana barazanar tarwatse wa ba abin da ke ci mata rai da tura mata bakin ciki sai yarda Huzaif yayi mata sosai zuciyarta take suya da kuna sosai take jin zuciyarta na sake buɗe wani fili mai girman gaske wani irin mahaukacin so taji na kawo mata farmaki a zuciyarta mikewa tayi idanuwanta a runtse sai faman tagaɗi take yi kamar wacce ta kora kayan maye.
Da sauri Goggo Marka ta mike ganin tana kokarin ficewa daga dakin riko ta tayi tana mai cewa.
 "Ina kuma zaki cikin wannan yanayin..".
Bata idar da maganar ta ta ba ta fizge hannunta tana mai duban Goggo bayan ta buɗe idanuwanta hawaye sai ambaliya suke yi.
 Hakan ba karamin kara batawa Abulle rai yayi ba ganin yarda Hafsat din tayi wa Goggo kamar wata tsaranta mikewa tayi cikin tsananin bacin rai lokaci guda ta fidda hannu ta dauke ta da mari ji kake tas! ta sake kifeta da wani barin tayi tangal tangal tana kokarin faduwa dafe da kuncinta.
Duban Abulle ta shiga yi idanuwan ta buɗe sosai zuciyarta take zafi da wani irin raɗaɗi ga wani abu mai girma da taji ya tokare mata makoshi.
 "Banza maras hankali wanda bata san ciwon kan ta ba Allah ya wadaran naka dai ya lalace wallahi ki ko kunya ba kiji ba ko nadama ba za kiyi ba akan abin da kika dauko wa rayuwarki...ko da yake na lura har yanzu ba ki san ke wacece ba shiyasa amma akwai rana na nan zuwa zaki san Annabi ya faku".
Bata tsaya sauraron jin kalaman Abulle ba ta bankaɗe labulan dakin ta ficewarta cikin tsananin tashin hankali mai girman gaske.
Kuka ne ya kwacewa Abulle da baya da baya ta ja ta jingina da bango zuciyarta sai faman kartawa take yi gabadaya al'amarin Hafsat ya bata tsoro yanayin da ta ga tana kallon ta yayi matukar caza mata kwanya ba ta san ya akayi ba bata san har yaushe Hafsat ta zama haka ba tana mata magana amma yanayin kallon da take mata gabadaya ba wani alamun tsoro ko runsunawa a matsayin ta na mahaifiyarta anya kuwa ba laifi tayi wa Allah mai girma ba ya jarabe ta da Hafsat?.
Girgiza kai ta shiga yi ranar da take tsoro kenan a rayuwarta ranar da Hafsat zata so fin karfin ta a duniyar nan ba abin da ke daga mata hankali ya hanata natsuwar rayuwa kamar Hafsat duk cikin 'ya'yanta ita ce kangararriya kuma Allah na gani ba wacce ta zama sanadin komai sai Mahiafiyarta sosai abin ke taba mata zuciya tayi fadan tayi rarrashin amma ina ta nuna bacin ranta sai ma ake nuna tsanar 'yarta take yi kaicon wannan rayuwa.
Dago kai tayi ta dubi Goggo dake zaune bakin gado ta zabga tagumi kallo daya zaka yi mata ka gane kamar abin bai wani ɗaɗata da kasa ba amma akwai alamun sanyi a jikinta musamman yarda ta ga Abulle ta shiga yanayin tashin hankali.
 "Abin da nake ta faman tunasar dake kenan Goggo amma kin kasa gane wa Hafsat mace ce abu kalilan ne zai bata mata rayuwa sangartar da kike nuna mata da wai sunan so ne wallahi BA SO BA NE domin ba in da zai kai ta yanzu mai gari ya waya don Allah Goggo yanzu in wannan abin yafita mai kike zaton zai faru na rantse da Allah ko ruwa gagararmu sha zai yi".
Gyaɗa kai kawai Goggo take yi tana faman turo baki gaba.
 "Ai da rufe ni da duka kikayi shine zan san na bata miki rai ko kuma ni na saka Hafsat dauko mana magana a duniyar nan ai ba wanda ya kai ni bakin ciki kan wannan lamarin kuma ai ba kanta farau ba balle ta zama karau uban kowa yana da nashi kashin a gindin sa don haka ban ga wanda zai takura wa Hafsat ba akan abin da tayi ai ba da gangan tayi ba Yaudaren ɗa namiji ne ta gamu da ita da kuma makircin wadancan mutanen...".
 "Goggo!".
Abulle ta fadi da muryar sauti don maganar tayi matukar tunzura mata zuciya da sauri ta mike ta dubi Goggo ji take yi kamar ta daura hannu akai ta kurma ihu ko ta samu saukin wahalar zuciya da zafin ruhi da take ji.
 "Goggo ni ban ga amfanin daukar hakkin wanda ba su da laifi ba kuma na rantse da Allah in har kika ci gaba da tsanar su Mariya da uwarta wallahi sai hakkin su ya kama ki domin na lura a duniyar nan ba wacce kika tsana kamar ita duk biyayyar da take miki da cin kashin da kike mata ba ta taba daga kai ta dube ki ba tunda ta shigo gidan nan abun dai daya ne matsalar ki take fama da ita kullum ba ta da sauki anya kuwa rayuwa za ta yuwu a haka".
Tana gama fadin haka ta juya da sauri ta fice daga cikin dakin cike da tashin hankali mai girman gaske bata san ya za tayi yanzu ba bata san mai ya dace tayi ba ta san dai Allah kadai ne zai yi mata maganin matsalar ta Allah na gani bata da laifi ta san ƙaddara ce kuma ta ansa da wannan tunanin zucin ta fice daga cikin gidan zuciyarta na harbawa da yarda zata tunkari mijinta da wannan al'amarin domin kuwa ya jima yana cewa Hafsat ta dawo gida amma ba yarda ta iya ta nuna masa yayi hakuri ba wani abu tun yana hakurin har yawan maganganun da ake yi akan Hafsat ya fara tunzura shi to ina ga yanzu yaji wannan bakin labarin.
****
Hafsat kuwa tun da ta fice daga cikin gidan ta dau hanya zuciyarta sai an gizata take yi akan kawai ta tafi gidan su Huzaif domin ba za ta iya zama ba a halin da ake yanzu dole ta je ta same shi duk wacce za a yi sai dai ayi domin kuwa sosai take jin wani mahaukacin son sa na kara nakarkar mata da zuciya yana bubbuɗe mata duk wani sashi na jikin ta yana samun matsugun ni sosai take ta jin ta a tashin hankali wanda tun da take a rayuwarta ba ta taba zaton haka ba yau rana daya gabadaya komai ya kwance mata.
Kuka sosai take yi na zuciya domin hawayen sun ki zubowa tashin hankalin dake kara rikita ta shine yarda mahaifiyarta take kallon ta ta tabbata in kowa zai yi mata uzuri ban da mahaifiyar domin ita kadai ne ta san halin da ta tsinci kanta a ciki a daidai wannan lokacin.
Tafiya sosai tayi wacce akaran kanta ba ta san tayi taba ita dai ta san jefa kafafuwanta kawai take yi a in da taji sun sauka har izuwa lokacin da ta isa inda take zaton gidan su Huzaif ne sosai gaban ta ya shiga faduwa ba ta san mai zata ce ba bata san ya zata kalli mutanan gidan ba shin zuwa zata yi ta ce musu ɗan su yayi mata ciki ko ya ya.
Girgizai kai ta shiga yi zuciyarta na faman harbawa tsoro da fargaba duk suka dire mata lokaci guda numfashi ta ja kafun ta dubi tankameman Get din gidan a hankali ta kai hannu ta shiga kwankwasawa daga can ciki taji motsin ana zare sakata mai gadi ne ya leko ya dube ta sama da kasa ganin ta a hargitse alamun akwai abun da ke damun ta hakan ya sanya shi tambayarta ko lafiya?.
Hawaye ne suka balle mata da sauri ta dauke su sannan ta ce.
 "Don Allah wajan mutannan gidan nan na zo wajan Mahaifiyar Huzaif".
Sake kallon ta yayi sama da kasa kafun ya ce.
 "Ko lafiya kike niman ta?".
Runtse idanu tayi domin ita dai bata san abin da za ta ce da shi ba a halin da take yanzu in zai bar ta tashi kawai ya barta.
Gefe ya ja alamun bata hanya don ya lura tana wani mataki na tashin hankali a hankali ta shiga share fuskarta sannan ta saka kafar cikin gidan tana takawa zuciyarta na kara curewa waje guda tayi tafiya kadan ta ja burki ta tsaya a tsakar gidan tana mai da numfashi tunani kawai take yi ta yarda zata shiga gidan nan ba ta san a wani matsayi zata je ba ita kanta ya gama kulle.
A hankali ta shiga jan kafafuwanta tana mai da numfashi har ta isa babbar kofar da zai sadata da cikin falon Handle din ta rike ta murɗa idanuwanta a runtse gabanta na tsanarta bugu jin kofar ta buɗe ya sanyata tura kanta gaba gadi domin ta sadakar duk abin da zai faru sai dai ya faru.
Zaune suke kowannan su fuskarsa a cure da alamun bacin rai motsin shigowar da akayi ne ya sanya macen dake tafaman sababi ta tsagaita gabadayan su suka juyo suna duban Hafsat da tayi wiki-wiki kamar wacce tayi wa sarki laifi Huzaif da ke zaune can gefe yana ta faman kumbure-kumbure ganin Hafsat da yayi kamar daga sama bai san lokacijln da ya mike ba cikin yanayi na firgici da tashin hankali yana nunata da hannu bakin sa sai rawa yake yi.
 "Ke! Uban me ya kawo ki gidan nan ban ce karki sake kokarin shigowa rayuwa ta b...".
Tun kafun ya idar yaji saukar lafiyayyan mari yayi taga taga kamar zai fadi kasa hannunsa saman kuncin sa runtse idanu yayi kafun ya buɗe su akan mahaifin sa da ke tsaye yana ta faman huci da hannu ya nuna shi bakin sa na rawa magana yake kokarin yi amma ya kasa tari ne ya sarke shi da sauri ya dafe kirjin sa ya koma ya zauna gami da runtse idanu a hankali tarin ya laɓa amma bai buɗe idanuwansa ba zuciyarsa yake ji tana faman zafi bai san abin da ke damun Huzaif ba gabadaya ya rasa gane kan sa sosai yake fuskarta matsala akan ɗa daya tak! da yake dashi.
 "Ya akayi baiwar Allah?".
Maihaifiyar Huzaif ta fadi tana duban Hafsat da izuwa lokacin ta fara dana sanin zuwa gidan su Huzaif idanuwanta su ka kawo ruwa sosai hannu ta saka ta dauke su ta fara kokarin yin magana da sauri Huzaif yayi tsalle ya dire gabanta yana famam tunkuɗata waje ita kuwa ta ki tafiya mahaifiyarsa ce ta iso ta riko hannun Hafsat ta dube ta cikin yanayi na rashin wasa.
 "Na san ɗana zai iya yin komai don ya cutar dake tunda na ganki cikin wannan halin na tabbatar akwai abin da yayi miki ki faɗa min na rantse miki zan bi miki hakkin ki kuma daga kan ki zai gane hakki ba wasa bane da yake ganin daukarsa ba komai bane".
Sosai Hafsat taji wani iri gabanta ne ya shiga faduwa tunanin take yi ta fadi kowa yaji in ta fadi tana da tabbacin zata iya samun abin da take so kuma zata iya rasa wa sannan in taki fadi ta tabbata Huzaif zai yi nasara a akanta.
 Bakin ta na rawa hawaye na mata zuba sosai ta dubi Huzaif girgiza mata kai yake yi yanayin sa lokaci guda ya sauya tsoro sosai ya bayyana a fuskarsa kau da kai tayi jin yarda zuciyarta ke kokarin tausaya masa da yanayin da yake ciki sosai take jin GURBIN SO da ta bashi yana kokarin rinjayar haushin sa da take ji.
 "Uhmm dama...kawai dai".
Sai kuma ta shiga taba cikin ta tana runtse idanu.
Mutuwar tsaye Mahaifiyar Huzaif tayi ta shiga ambaton innalillahi wa inna ilahiri raji'un shi kuwa mahaifinsa da ya buɗe idanu lokacin da ya ji Hafsat ta fara magana ganin abin da take nuna wa ba karamin kaɗa 'yan hancin sa sukayi ba mikewa yayi cikin tsananin bacin rai da kunar zuciya.
 "Ke muje ki kai ni gidanku yanzun nan Hajiya maganar gaskiya Huzaif na lura aure yake so kuma wallahi in har ina numfashi a doron kasar nan wannan lamarin shine na karshe wanda zai dauko mani ya hanani kwanciyar hankali wallahi tallahi kin ji na rantse sai Huzaif ya auri wannan yarinyar ko da kuwa hakan na nufin numfashin sa zai yanke daga lokacin da na saka limami ya daura musu auren".
Yana gama fadin haka ya fizgi hannun Hafsat yayi waje da ita ba Mahaifiyar Huzaif kadai ba hatta shi kasan din mutuwar tsaye yayi domin bai taba zaton hakan ba duban sa tayi fuskarta da murmushi mai tafe da hawaye ta juya cikin sauri tayi sama shi kuwa kwakkwarar motsi kasawa yayi kan sa ya ji yana juya masa lokaci guda yasaka hannayensa duk biyun ya dafe shi gabansa na tsananta faduwa wani firgici yaji shi a ciki musamman akan furucin mahaifinsa wanda ya tabbatar ai iya tabbata....
*KAMALA MINNA*😘😘😘😘
Post a Comment (0)