UKU-BALA'I 58

UKU BALA'I
         NA.
        KAMALA MINNA

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
  BABI NA HAMSIN DA TAKWAS
Ba karamin tashin hankali Hafsat tashiga ba lokacin da taji mahaifin Huzaif yana ta faman sababi tun da suka dauko hanya ko hadiyar yawu ba yayi idanuwansa sun kaɗa sun yi jajir kamar jan gauta ita kan ta tayi dana sanin zuwan ta gidan.
 "Ban dan dakikan ci kina 'ya mace har ki zauna namiji ya yaudareki da banzayen kalaman sa ya nemi kashe miki rayuwa a banza a wofi bayan ke kan ki in mai tunani ce ya kamata tun kafin haka ta faru in son ki yake yi tsakani da Allah sai ya fito kuyi aure duk uwar da za kuyi ba wanda zai hana ku amma da yake kan ki a tukunya yake kika saki baki kika aminci da zancen Huzaif wanda ni kaina mahaifin sa Allah na gani ina fargaba akan sa da halayen sa ban san abin da yake damun ku ba 'ya'ya mata a yanzu da yawan ku maza na amfani da ku wajan saka muku son su wanda zai hana ku ganin laifin su sam! wasun ku basa gane SON GASKIYA da SON SHA'AWA".
Kwaɓa yayi gami da dukan sitiyarin motar sai faman jan tsaki yake yi kamar zai tsinke harshen sa.
Numfashi ta ja gami da haɗiye wani abu da taji ya tsaya mata a makoshi lokaci guda zufa ta shiga karyo mata sosai ta tsorata dashi ji take yi kamar tace ya tsaya ta sauka amma ina ta kasa.
Cikin wannan yanayin da kwatancen da take masa suka iso kofar gidan parking yayi sannn ya juyo ya dube ta ganin tayi wiki-wiki da idanu ya sanya shi galla masa harara domin shi dai ba ya ganin laifin maza kamar yarda yake ganin laifin mata domin ba yarda za ayi kina 'ya mace har ki bari namiji ya yaudare ki ba tare da yardar ki ba in har kika nuna masa ba ki yarda ba ai ba dole zai yi miki ba ai so ba hauka bane.
 "Maza ki je kiyi mani sallama da mahaifin ki".
Ware idanu tayi gabanta ya yanke ya fadi ita a rayuwarta har mantawa take yi tana da wani mutum wai mahaifi sosai taji wani irin yanayi a zuciyarta yau rana daya taji takaici rashin baiwa mahaifinta lokacin sa yau ga ranar sa ta zo shin da wani idanu zata je ta dube shi bata je masa da kayan alheri ba sai na akasin sa ta san dai ba zata fara ba don ta san izuwa wannan lokacin labari ya kai kunnansa.
 "Dake fa nake ko ba nan ne gidan naku ba?".
Mahaifin Huzaif ya katse ta da sauri ciki firgici har tana buge koshin ta a jikin motar ta buɗe murfin ta fito sai faman rarraba idanu ta ke yi sosai ta lura da mutanan layin na ta kallonta da wani irin yanayi ita kanta sai ta ji ba dadi ba yarda ta iya haka ta ja kafafuwanta ta nubi cikin gidan kirjinta na dokawa da tashin hankali.
A tsakar gida ta tadda Mariya na wanki kallo ta bi ta shi kafun ta kau da kai ita kan ta Mariyar kallon ta take amma bata ce da ita komai ba sai yanayim tausayi da ya bayyana a gareta sosai ta lura da abin da take zargi din da gaske din dai cikin ne domin gashi nan har ya fito don ita da duk ba ta lura ba.
Hafsat na shiga cikin dakin ta tadda Goggo Marka zaune tallaɓe da haɓa abin duniya duk yabi yayi mata yawa ganin Hafsat ta shigo ya sanya ta mikewa cikin hanzari.
 "Ke kuma ina kika je cikin wannan halin so kike yi jama'a su fuskanci halin da kike ciki ne?".
Kau da kai tayi tare da cizon laɓɓa ba tare da tace da ita komai ba.
 "Dake nake Hafsat kika yi banza dani".
Turo baki tayi tare da cewa.
 "Zuwa nayi gidan su Huzaif na sanar da iyayensa yanzu haka tare da mahaifin sa nake domin yace sai ya zo ya sami mahaifina".
Gaban Goggo Marka ne ya yanke ya fadi lokaci guda idanuwanta sukayo waje ta daura hannu akai.
 "Mun shiga uku in mahaifin ki ya san wannan lamarin ai mun boni".
Dubanta Hafsat ta shiga yi ganin yanayin da ta shiga takaici ya sake kume ta.
 "Yana waje fa yana jira don cewa yayi nayi masa sallama da mahaifina".
Da hanzari Goggo Marka ta figi zanin dake rataye ta yafa tayi waje zuciyarta da wani kudiri da ta dauka cikin kankanin lokaci har tuntube take yi wajan saurin tana fita hango shi tayi jikin motarsa ganin hakan ya sanyata tsayawa tana tunanin kafun ta canza fuska ta isa gareshi sam bai lura da ita ba sai ji yayi an bubbuga masa jikin mota da sauri ya juyo ya dube ta ganin ta ya sanya shi rinsinawa yana gaishe ta mai makon ta amsa sai ma wani wulakantaccen kallo da ta watsa masa.
 "Ina tsinannan ɗan naka ma ci amana Allah ya wadaran ɗa irin naka".
Duban ta ya shiga yi domin jin maganganun nata yake yi kamar ba gaske ba sai da ya sake dubanta sosai yaga yarda take faman kallon sa a wulakance ya bashi tabbacin kila ita ce mahaifiyar Hafsat sosai yaji ɗacin maganar da tayi a ransa amma sai yaki nuna mata tunda a girme ta girmeshi.
 "Ayi hakuri Baba kin san sha'anin 'ya'yan namu na wannan zamanin ka haife su ne baka haifi halin su ba...".
 "Ni rufe mani baki kaji ko ai dole kace haka tun da ɗan ka ya gama da jikata ya cuce ta maganar gaskiya ba zan yarda ba dole kasan abin yi tun kafin wannan abin kunyar ya bazu a jama'a su sani don wallahi ba zan lamun ta ba".
Duban ta yake yi da mamaki yarda ta hakikance tana ta faman zabga masa magana kamar shine yayi wa 'yarta ta ciki ko ya ce jikarta kamar yarda ta fadi ba zai yi mamaki ba lura da yayi ita tsohuwa ce kuma zai yarda da cewa RIKON KAKA bai yi ba don ya tabbata in da a hannun iyayenta wannan yarinyar take hakan ba zai taba faruwa ba in har sun san abin da suke yi.
 "Ayi hakuri Baba ina mahaifin ta yake".
Wani irin dokawa gabanta yayi jin ya ambaci mahaifin Hafsat yake nema nan da nan jikin ta ya shiga rawa da sauri ta dube shi.
 "Baya nan Allah yayi masa rasuwa...kasan abin da za ayi kawai asirinmu a rufe ni da kai da 'ya'yan namu a zubda cikin nan tun kafin kowa ya sani ina ga haka shine mafita garemu...".
 "Zubar wa kuma bayan laifin da aka aikawa ubangiji sannan a sake yin wani laifin anya kuwa kina tausayin jikar nan taki anya kuwa kina son ku rabauta ke da ita to a gaskiya ba za ayi haka dani ba abu daya zan iya yi muku shine na aurawa jikarki ɗana ni nayi wannan alkawarin sannan ba za ayi auren ba har sai ta haife abin da ke cikinta ina ga wannan shi kadai ne mafita a garemu".
Duban sa Goggo ta shiga yi cikin wani irin yanayi na rashin baiwa maganar tasa muhimmanci.
 "In kuwa haka ne sai dai ta koma gidan ku da zama don Allah na gani ba zan zauna da ita a zo ana zunɗena da gulma ta ba".
Mamaki ne ya sake turnuke shi yau ya kara tabbatar da sakaci da rashin alfanun rikon kakan musamman ga 'ya'ya mata yanzu mai gari ya waya anya kuwa iyayen yarinyar nan sun san halin da 'yar su take ciki kuwa? Sosai yaji haushin yarda take maganganun ta don haka ya dube ta.
 "In har ba zaki yarda da abin da nace ba sai dai kowa ya kama gabansa don ba damuwa ta bace jikar ki ce zata shiga cikin gagarin rayuwa ina ma laifina akan kokarin da nayi".
 Yana gama fadin haka ya fada cikin motarsa ya ja ya tafi ya bar Goggo Marka sake da baki sai faman sababin take yi ganin mutane sun fara dawo da hankalin su gareta ya sanyata juyawa ta na fadin.
 "Aifa na kurya masu gansa kuka a idanu an bazo mani".
*****
Abu kamar wasa lamari sai kara rincaɓewa yake yi a wajan Hafsat tun ranar da mahaifin Huzaif ya zo ko kafarsa ba ta sake gani ba sannan ga Goggo Marka ta saka ta gaba a na cikin haka mahaifinta yayi wa gidan tsinke ba karamin kaɗuwa tayi ba ita da Goggo Marka idanuwansa sun kaɗa sun yi jajir kallo daya za kayi masa ya baka tausayin don tashin hankali iyakar karshensa ya shiga cikin sa duban Hafsat yayi.
 "Ni Mahaifin ki ne amma daidai da rana daya ba ki taba bani wannan matsayin nawa ba Hafsat ni na haifeki amma ni da banza duk daya ni da uwarki ba wanda kike gani da gashi rayuwarki kike yi yarda kike so baki da mai kwaɓa ko ma an kwaɓe kin Goggo gani take yi kamar matsa miki ake yi yanzu wa gari ya waya iyee ke ba ki cikin kwanciyar hankali mu iyayenki da mu ka san kina da hakki akanmu mu ma ba mu da kwanciyar hankali yanzu uwarki na can bata da lafiya kuma ba wanda ya zama sanadi sai ke".
 Wasu hawaye masu dumi suka zubo masa kau da kai yayi cikin dauriya.
 "Hafsat tunda kika taso a matsayin ki na 'ya mace mai rauni mai makon ki yi kokarin tsare rayuwarki amma ki ka ki kika nuna ba wanda ya isa dake ke a tunanin ki wannan rawar kai da kike yi shi zai sa an gan ki da mutunci kina tunanin wannnan rayuwar da kika daukarwa kan ki akwai na mijin da zai gan ki da mutunci har yace zai iya zama dake a matsayin matar aure ina! ba wani ɗa namiji da zai auri jahila ko wani namji burin sa ya samarwa 'ya'yansa uwa ta gari ke ba abin kwaikwayo bane ga 'yar uwarki ba abin da ba kuyi mata ba ba abin da ba ku ce mata ba akan neman ilmi da take yi haka kuke jifan ta da mugayen kalamai yanzu wa gari ya waye ke da ita waye yake da nasara a rayuwarsa na tabbata yanzu Mariya duk wani namiji mai hankali mai natsuwa zai so ace ta zama matarsa amma ke fa a yanzu kina tunanin ko wanda yayi miki wannan aikin zai aure ki ne ina! ko ma ya yarda zai aure ki to wallahi ba zai taba ganin ki da mutunci ba ke da banza duk daya zai dauke ku".
Goge hawayen da suka zubo masa yayi gami da girgiza kai.
 "Yanzu kika fara shiga tashin hankalin rayuwa in har kika ce ba zaki sauya ba".
Yana fadin haka yafice zuciyarsa cunkushe da tashin hankali.
Goggo Marka dake can gefe tun dazu tayi wiki-wiki da ita duk abin duniya yabi ya dame ta ta rasa me za tayi maganar tun tana boye wa har an fara ganowa duban Hafsat tayi.
 "Hafsat wai me ya kamata muyi ne yanzu don ni gaskiya na fara tsorata da lamarin ko gidan iyayen naki zaki koma?".
Wani duban rashin fahimta Hafsat tayi mata zuciyarta na zafi me Goggo marka take nufi da wannan maganar ta ta da take fadi girgiza kai tayi cike da kunar rai.
 "Kamar ya na koma gidan iyayena Goggo kina kallon fa abin da Babana yace sannan kuma kice na koma bayan ba a gabansu komai ya same ni ba".
 "To ya kike so in yi ne kowa ya zo kaina zai sauke matsalarsa kamar a kai na ne wannan lamarin ya fara faruwa ni gaskiya na gaji gwanda ki koma gaban iyayenki ko kuma kisan yarda zakiyi ki sami Huzaifa din akan maganar auren ku da mahaifin sa ya zo dashi".
Hawaye ne suka shiga zubo mata cike da takaicin yarda Goggo Marka ke nuna mata ta fara gajiyawa da ganin ta mikewa tayi sai faman tangaɗi take yi ga cikin nata ya bayyana sosai.
 "Ni Goggo kike hantara ni kike cewa kin gaji da ganina kenan dama ba son Allah kike yi mani ba dama kin rabani da iyayena ne don ki bata min rayuwa".
Gyaɗa kai ta shiga yi hawaye na sake balle mata.
 "Shikenan Goggo amma ki sani wallahi ba in da zani domin ba laifin iyaye don haka ba zai je na kara tayar musu da hankali ba a nan zan zauna in ma haihuwar ce sai dai nayi ta a nan sai dai duk abin da zai faru ya faru".
Ta karashe tana galla mata harara cike da takaici Mikewa Goggo Marka ta yi ta iso gareta.
 "Hafsat ni kike fadawa wannan maganar haka?".
 "An fada miki kin cancanta ne shiyasa kuma wallahi takaicin nan tare dake za mu shanye shi".
Mamaki ne ya cikata ganin yarda Hafsat ke mata magana cikin tsawa-tsawa kamar zata kai mata bugu bata gama shan mamaki ba sai da ta ga Hafsat ta tsartar da yawu ta bankaɗe labule ta fice daga cikin dakin.
*Kamala Minna*😘😘😘
Post a Comment (0)