UKU-BALA'I 60

UKU BALA'I
           NA.
    KAMALA MINNA.

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.
  BABI NA SITTIN.
Tunani kawai take yi akan yarda zata anshi Dr.Karami lokaci guda bayan kuma ta san akwai wani akasa ko da yake ya kamata izuwa wannan lokaci ta saukaka wa kanta domin samun natsuwar zuciyarta.
Amma ta yaya hakan zai kasance ta yaya hakan zata faru bata sani ba bata san yarda zata dauki lamarin ba sosai take jin kamar bata kyautawa Dr.Aqeel ba in tayi duba da yanayin dake tsakaninta dashi.
"So daban kyautatawa daban".
Ta jiyo wani sashi na zuciyarta na dauko mata wani sashi na zancen Dr.Karami da ya faÉ—a mata.
 "Amma ai kyautatawa na haifar da so da kauna ga mutane biyu? Kuma ai kyautatawa na cikin abin da ke haifar da so ga zukatan dangin rai".
Ta fadi tana tura laɓɓanta cikin baki tana cizawa a hankali juyi tayi daga kwance da take ta mai da idanuwanta suna kallon sama sosai take jin zuciyarta da kwanyarta na mikata wani mataki na musamman wanda zata so ace ta rayuwa a cikin sa har gaban abada amma kuma bata zaton haka ganin lamarin take kawai a labarin kanzon kurege ba zai taba tabbata ba.
Numfashi ta ja tana mai da numfashe idanuwanta a hankali ta buÉ—e su ta dago dan yatsen hannunta wanda yake dauke da zoben da Dr.Karami ya sanya mata kallonsa take yi zuciyarta na kara buÉ—ewa da kaunarsa ji take yi duk wani GURBIN SO na zuciyarta Dr.Karami yana kokarin mamayewa cikin yan kwanakin nan sosai take jin ta a wani mataki na farin cikin zuciya wacce ta cika da kauna zallarta.
Zata so ace rayuwar ta mika a haka za ta so ace rayuwar ta cigaba da tafiya a haka amma ina! akwai wani wajan da za a kin tafiyar ta sani ALKALAMIN ƘADDARA zai iya zano mata wani abu mai girman gaske ya dora mata a matsayin JARRABI izuwa wannan lokaci ta rigaya ta saba sosai da sosai bata tunanin akwai kaddarar da zata fado rayuwarta bata yi kokarin ganin ta cinye ta ba.
 Gabanta ne ya doka da sauri ta mike tana ambatar 'Hasbunallahu wa ni'imal wakil Yaa Hayyu Yaa Kayyum'.
Idanuwanta ta zaro sosai hannayenta saman kirjin ta tana jin yarda BUGUN ZUCIYARTA ke kara tsananta.
"ME KE FARUWA?".
Ta fadi tana jan numfashi da sauri ta shiga kokarin mikewa ji tayi duk ilahirin jikinta ya dauki sanyi kamar an doke mata duk wata gaɓa dake jikin ta a hankali ta shiga taka kafafuwanta kanta ko dan kwali babu yalwataccen gashin kanta ya baje sosai har zuwa fuskarta da sauri ta janyeshi zuwa baya ba tare da ta sanya dankwali ba tayi hanyar waje a bakin kofa ta tsaya tana ajiyar zuciya Umma ta gani zaune ta zabga tagumi da sauri ta isa gareta ta taɓa ta amma ba alamaun ta san ta zo wajan.
 "Umma!".
Mariya ta fadi da sauti a muryarta tana mai jinjigata a hankali taja wani dogon numfashi ta dago idanuwanta da suka dan kaÉ—a ta dubi Mariya kafun ta kau da su cikin wani irin yanayi na damuwa.
 "Umma lafiya na ganki haka?".
Murmushi kadan tayi wanda da ka kalle ta zaka gane na dole ne girgiza kai tayi tana cizon laɓɓa.
 "Mariya mahaifin ki shi na tuna wani mafarki mara dadi nayi a yanzu a nan zaune ina gangaÉ—i sosai naji na tsorata".
Ware idanu Mariya tayi jin abin da Umma ta fadi ko dai wani abu na shirin faruwa ne domin itama taji irin yanayin a yanzu zuciyarta ta sake bugawa hannun Umma ta kamo ta danke sosai cikin nata.
 "Anya Umma Abbana ba ya cikin matsala zuciyata sosai take hasashen haka ina tsoro Umma ya kamata ace ko ina yake ya bayyana muna tsananin bukatarsa hakurinmu umma...".
 "Mariya to ya za muyi da Æ™addarar Allah haka ya tsara mana a rayuwa dole hakan sai ta faru fatana dai duk in da yake tsayin shekarun nan Allah ya bayyana mana shi".
Hawaye ne suka kwaranyo wa Mariya a idanu da sauri ta saka bayan hannunta tana shafe su tana mikewa kan kafafuwan ta sosai take ji a zuciyarta mahaifinta duk inda yake baya cikin dadi da farinciki gami da kwanciyar hankali sosai take jin fargaba da tsoro a zuciyarta tana son ganin mahaifinta tana so ta sanya shi a idaniyar ta sosai take kewarsa.
   A kullum sai tayi tunaninsa tana son ta ganshi tana so ya dawo cikin duniyarsu su rayu tare zuciyarta sosai take zafi duk sa'ilin da ta tuna lokacin da mahaifinta ya bar su ciki mawuyacin hali ta sani kaunar da yake nuna musu ba zai sanyashi guje musu ba ta tabbata akwai abin da ya sanyashi barin su ya mika wani wajan tsayin lokaci mai girman gaske...
****
Saukarta kenan daga Napep tana kokarin shiga gidan su Mariya taji anyi mata Horn bata yi zaton da ita ake ba sai da taji ana tayi ba ƙanƙautawa sannan ta juya ta kalli in ta tajiyo horn na tashi ta gefen idanu Dr.Aqeel ne tsaye kafarsa daya a waje daya cikin motar ware idanu tayi gami da juyowa tana duban sa ba tare da ta ce kala ba.
A hankali ya kulle motar ya shiga takowa gareta harÉ—e hannayenta tayi a kirji tana kallonsa Up and Down cikin wani irin yanayi zuciyarta na suffan ta mata tsarin halintarsa na cikakken namiji wanda ya hada duk wani abu da mace ke bukata a wajan namiji sanye yake cikin kananun kaya suit light blue wanda tayi matukar yi masa kyau hannunsa daure da hadadden agogon Rolex mai tsananin kyau....
 Da sauri ta ja numfashi sa'ilin da taji daddar kamshin turarensa ya daki hancinta da sauri ta kau da idanuwanta daga barin kallon sa.
 "Halin dai naki na nan na shan kamshi Baseera".
Duban sa ta sake yi gami da murmushin gefen kumatu.
 "In dai ba mugun hali bane ai da sauki".
Ta fadin tana kallon wani gefe daban.
 Nishin da taji yayi ne mai sauti ya sanyata duban sa da sauri cikin alamun tuhuma yanayinsa ta ga ya sauya gabadaya kamar wanda ba shi da lafiya laÉ“É“ansa ya tura cikin baki yana cizawa.
 "Ban san mai zai ce miki ba Baseera na san kin fahimci halin da nake ciki akan Æ™awarki ina son ta sosai zuciyata take dakon sonta ya kamata izuwa wannan lokaci ace ta bani dama son ta nake yi so zallarsa".
Tunda ya fara magana take kallonsa da mamaki namiji har namiji amma so ya mai dashi wani iri kau da kai tayi zuciyarta na jin haushin yanayin da ta ga yana nunawa AKAN SO.
 "Dr.Aqeel kenan nifa wannan lamarin naku na rasa gane kan sa wallahi abu yaki ci ya ki cinyewa kun saka min Æ™awata a gaba sai faman figarta kuke yi kun hanata sakat! bayan kuma ku kan ku kun sani ba yarda za ayi dukkanku ku aure ta dole sai dai daya a cikin ku".
 "Ni nake son ta Baseera amma ta kasa sanin haka".
 "Su ma sauran ai son ta suke yi ko ya dai kamata ace kun kafa teburin Sulhu a tsakanin ku ku barwa daya in kuma ba za ku iya ba gaskiya dole ku rabu da ita wani ya aureta daban tun da kun kasa hakurar da zuciyarku akan sonta".
girgiza kai yayi yana jin yarda zuciyarsa ke kara buÉ—ewa da son Mariya ya lura har yanzu Baseera bata san SO ba shi yasa bata dauki lamarin nashi da girma ba.
 "Zan kama kafa dake".
"Ban yarda ba".
"Saboda me?".
"Ba zan iya bane gaskiya ba zan takura mata ba".
runtse idanu yayi kafun ya buÉ—e su akan ta da wani rin yanayi kallon ta yake yi sosai da sosai zuciyarsa na mikashi wani mataki mai girman gaske kwanyarsa yake ji ta shiga yawo dashi wani sashi na daban tana buÉ—e masa shafi-shafin wasu lamuraka masu girman.
 "Zan takura miki".
Ya fadi da wani irin yanayi a muryarsa ita kanta sai da taji tsigar jikinta ta mike numfashi ta ja.
 "Zaka iya takura mani amma bana tunanin takurawar taka za tayi amfani".
"Dole tayi amfani ki rubuta ki ajje daga yau ina tare da ke har ranar da BURINA zai cika".
ya fadi muryarsa da zurfi a cikinta dubansa tayi da murmushi a fuskarta.
 "MU ZUBA MU GANI".
Ita ma ta fadi da murya mai sauti da sauri ta juya ta doshi kofar gidan gabanta na dokawa sosai taji a jikinta kallon ta yake yi sosai take jin kafafuwanta kamar za su zubda ita me Dr.Aqeel ke nufi da ita sosai taji wani iri a jikinta sosai take jin kamar wani abu na faru kwanyarta taji tana yamutsewa zuciyarta na matsewa tana mikata wani mataki mai girman gaske.
Tana shiga cikin soron gidan ta jingina da bango tana mai da numfashi idanuwanta a lumshe sai da ta shafe dakiku kafun ta ja kafafuwanta da taji sun yi mata sanyi ta shiga cikin gidan.
  ba kowa a tsakar gidan hakan ya bata damar zarcewa bangaren su Mariya bakinta dauke da Sallama ba ansa ta ba haka ya sanya ta sake yin sallamar nan ma ba a ansata ba labulan dakin ta daga can ta hango Mariya rigingine a gado idanuwanta na kallon saman dakin da sauri ta zare takalman ta ta shiga cikin dakin ba tare da ta sani ba har ta zauna bakin gadon hannunta ta kalla zoben da ta gani ne ya sanyata ware idanu cike da mamaki ga dariya na kokarin kwace mata da sauri ta sanya hannu ta rufe bakinta sai da ta gama karewa zoben kallo sannan ta daka mata duka.
A firgice ta mike tana shirin zurawa a guje ganin Baseera ya sanyata sakin jiki tayi kasa ta zauna tana mai da numfashi gami da dafe kirji.
 "Mtss Allah ya kyauta miki ai wannan sai ki firgita mutum ya zura da gudu".
Dariya Baseera tayi gami da kamo hannun Mariya mai zobe ta kalla sannan ta daga idanuwanta ta kalle ta cikin tuhuma tana mai sakin murmushi hakan da Mariya ta gani ya sanya fizge hannunta ita ma tana dariya.
 "Mariya!!".
Baseera ta fadi da murya mai zurfi kafun ta dafa kafaÉ—arta muryarta tayi kasa sosai.
 "Ya kamata zuwa wannan lokacin ki san matsaya a rayuwarki rayuwa baza ta taba daidai a wannan matakin ba da kike kai a yanzu kuruciyarki zaki duba karki yasar da ita a banza a wofi wajan sanyawa kan ki damuwa don Allah na roke ki Mariya ki san abin yi Umma za ki duba nasan ta fiki shiga tashin hankali akan wannan lamarin sai dai ba zata nuna miki hakan ba".
Cikin rashin fahimta Mariya ke dubanta.
 "wai shin me kike nufi ne?".
"Kin fi kowa sani Mariya akan maganar ki da wadannan mutanan ne ya kamata ki tsaida guda daya gwani kin ga yanzu haka Dr.Aqeel yana kofar gidan nan don na tabbata ya dade da zuwa a nan na tadda shi".
Da sauri ta dafe kirji gami da zaro idanu waje.
 "waje fa kika ce Baseera na shiga uku".
"Ba ki shiga uku ba zabi ne naki".
Shiru Mariya tayi tana runtse idanu kafun ta riko Hannun Baseera.
 "Baseera akwai matsala akwai abin da baki sani ba wanda na boye miki maganar gaskiya ina tsoron yanayin nan da muke ciki kisan a halin yanzu Hafsat na nan dauke da juna biyu kuma Huzaif ne sila...".
Fizge hannunta Baseera tayi ta mike tsaye jikinta har ɓari yake yi idanuwanta a warwaje laɓɓanta sai motsawa suke yi alamun tana son yin magana amma ta kasa numfashi ta ja kafun ta runtse idanu ta buɗe su.
 "me ki ke son ce mani Mariya Huzaif din da na sani Yaa Rabbi!".
dafe kanta tayi gami da komawa ta zauna zuciyarta na matsewa da wani irin yanayi.
 "Garin ya ya hakan ta faru Mariya?".
Girgiza kai ta shiga yi kafun ta ciji laɓɓanta.
 "Baseera Alfarma nake nema gareki".
ta fadi tana kamo hannayenta Baseera da jikin ta ya gama yin la'asar ta sarke da nata tana faman matsewa zuciyarta na bugawa da wani irin yanayi mai girman gaske.
 maganar take ji tana yi mata nauyi maganar da take so ta fadiwa Baseera bata san ya zata dauke ta ba tana tsoron taki amincewa ba tana son wani abu na rashin jin dadi ya gilma a tsakaninsu in taji bukatarta ta dago idanunta tayi da suka kaÉ—a ta dubi Baseera wacce itama izuwa wannan lokacin gabadaya hankalinta ta mai dashi wajan ta idanuwanta na zagayawa a gareta tana jin yarda zuciyoyin su su dukan biyun ke bugawa da sauri sauri....
*Kamala Minna*😘😘😘
Post a Comment (0)