UKU BALA'I.
NA.
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA SITTIN DA DAYA.
Numfashi taja mai zurfi kafun ta tura laɓɓanta cikin baki tana cizawa idanuwanta har zuwa wannan lokaci suna kan Baseera zuciyarta sai kara harɓawa take yi da sauri-sauri fargabarta da tsoronta suna kara daɗuwa sosai take hango rashin yarda da amincewa gami da rigima cikin idanun Baseera wacce tayi mata fakare tana yi mata kallon tuhuma.
'Ya za ta dauki lamarin in na sanar da ita anya kuwa zata yarda har ta aminci da bukatata?'.
Mariya ta fadi haka a ranta tana kara matse hannun Baseera a cikin nata.
"wai me ke faruwa ne?".
Baseera ta fada gabanta ita ma na cigaba da faduwa.
"Baseera ki Auri Dr.Aqeel".
Ta fadi tana runtse idanunta sosai a cikin jikinta take jin wani iri zuciyarta na matsewa da wani irin yanayi da yake mikata wani mataki mai girman gaske.
Dariya Baseera tayi cikin rashin baiwa batun muhimmanci sosai tana kallon Mariya da idanunwanta ke a rufe.
"Ban gane ba Mariya me kike nufi kin san kuwa abin da kike cewa?".
BuÉ—e idanunta tayi sosai wanda suka kaÉ—a sukayi jajir ganin hakan yasanya Baseera nutsuwa tana kallon ta lokaci guda zuciyarta ta buga da wani irin tsoro da ya mamaye duk ilahirin jikinta.
Gyaɗa kai Mariya ta shiga yi kafun ta motsa laɓɓanta.
"Ki taimaka ki auri Dr.Aqeel Baseera".
Ta sake fadi tana kara kusanto Baseera fizge hannunta tayi gami da mikewa kallon Mariya take yi da wani irin yanayi kafun ta ja da baya sosai tana sake yi mata wani kallo mai kama da na tsoro ita kanta Mariya ta tsoro ta da irin kallon da take yi mata mikewa tayi tana takowa in da take ta sake riko hannunta tana sarkewa da nata.
"Ki taimaka Baseera ki aure shi wannan hanyar ce kawai nake hango mana mafita a gareni da kowa ma".
Kallonta take yi sake da baki kwanyarta take ji tana mikata wani mataki mai kokarin kona mata kwanya zuciyarta take ji tana harbawa da sauri-sauri.
"Ki taimaka ki aure shi na san za ku dace kuma za ku so juna".
"Ba zan iya ba Mariya ba za ayi wannan cin amanar dani ba".
Ta fadi tana fizge hannayenta tana kokarin ficewa daga cikin dakin da sauri Mariya ta riko ta sosai ta juyo da ita idanuwanta suka kawo kwalla sosai cikin rawar murya Mariya ta fara magana.
"Karki kawo cin amana a wannan lamarin Baseera ni nace na amince miki kuma na san ba haramun bane don haka don Allah ki anshi bukatata hakan ne zai tabbatar da amincin ƙawancenmu".
"Ki yi hakuri ba zan iya ba Mariya".
"Ki taimaka ki auri Dr.Aqeel Baseera ba za kiyi da na sani ba ni za ki taimakawa".
"Mariya....!".
Da sauri Mariya ta kai hannunta ta rufe mata baki tana girgiza kai hawaye na sauko mata saman fuska.
"ko MATAR MIJINA kika zama Baseera ba zan taba da na sani ba domin na san halin ki kuma na san ba zaki taba abin da zai cutar dani ba Baseera matsayin yar'uwa kike a wajena kina da matsayi mai girma a gareni ki anshi bukatata ki daure karki ce dani a,a".
Runtse idanu Baseera tayi tana jin zuciyarta na mikata wani mataki mai girman gaske gabadaya komai ya cunkushe mata ta rasa wani tunani ma zatayi ba ta taba zato ko tsammanin Mariya wannan bukatar zata nema a gareta ba in da ta san haka ce zata faru ba abin da zai kawo ta wannan gidan amma ina ALKALAMIN KADDARA ya zano mata rubutun da sai ta zo ta karance shi.
'Anya ba cin amana in ta yarda da batun Mariya anya hakan ya dace bata jin son Dr.Aqeel a ranta ba ta jin sun dace a tsakanin ita dashi to in ita ta yarda shi fa a yarda ta ga yana mayan son Mariya an ya kuwa zai dube ta da idanun kirki har ya anshe ta a matsayin matar aure gareshi ina! ba zata yarda taje in da ba a son ta ba ba za ta je in da ba za a ganta da mutunci da kima ba ba zata yarda ta shiga in da za a din ga yi mata kallon kamar dole akayi masa ba'.
Nazarin da ta shiga yi da zuciyarta kenan cikin wani irin yanayi tsoro da fargaba na kara bayyana a gareta.
'Mariya ta cancanci komai fiye da haka za ta so ace sanadin ta ta samu farin ciki za ta so ace ta sanadin ta rayuwarta ta sauya ta dawo mai armashi amma ta ya ya hakan zata kasance bata tunanin auren Dr.Aqeel shine mafita'.
Kamar Mariya ta san nazarin da take yi da zuciyarta dubanta tayi cikin kara narkar da murya da son biyan bukatar ta duk da tana jin wani iri a zuciyarta ta.
"Ki daina shakka ko fargaba akan Dr.Aqeel Baseera zai so ki ba zai taba wufutar dake ba so zai yi miki mai an suna so zallar sa karki sake ki saka wa zuciyarki fargaba ko tsoro".
Hannu ta saka tana dauke hawanyen fuskarta tana mai kokarin zaunar da Baseera amma ta kiya ta kwace kanta.
"Gida zan tafi Mariya kaina ciwo yake yi don Allah rabu dani zan yi tunani".
"Ban yarda ba Baseera ba zan yarda ki fice daga cikin gidan nan ba har sai kin ansa mani bukatata in kuwa har baki an sa ba to na tabbata amincin dake tsakaninmu ba kai ya kawo ba wallahi tallahi Baseera ko mijin da nake aure ki ka zo ki ka nuna kina so wallahi zan yarje miki ki zama MATAR MIJINA".
Da mamaki Baseera ke dubanta fuskarta na sakin wani murmushi wanda yafi kuka ciwo sosai ta kamo hannun Mariya ta saka a nata.
"ki daina kiran amincin dake tsakani na dake kina danganta shi da wannan lamarin ni nace miki ki bari nayi tunani ba yarda za ayi na ansa wannan batun lokaci daya Mariya ba sauki fa lamarin nan gareshi ba duba zakiyi da shi Dr.Aqeel ba shi yace yana so na ba ke yake so kina tunanin in ya ji batun nan zai yarda har ya dube ni da kima da mutunci ya anshe ni amatsayin da kike kokarin daura ni?".
Murmushi ita ma tayi zuciyarta na kara matsewa.
"Alkawari nayi miki zai so ki so da bai taba yi wa wata 'ya mace...".
"Ya isa haka Mariya maganar ta isa haka ki daina danganta KALMAR SO a wannan bahagon tunanin naki mara tushe kece mace ta farko kuma ta karshe da Dr.Aqeel yayi wa son da ba zai sake yi ma wata mace ba a duniyar...".
"Na karya taki Baseera a wannan matakin ni nace miki in har kika aminci da Dr.Aqeel sai yayi miki so fiye da wanda yayi mani a filin duniyar nan ki rubuta wannan ki ajje ni dai BURINA ki amince".
Kanta ta dafe da take jin yana sara mata maganganun Mariya suna kokarin saka mata ciwon kai bata san yarda za tayi da ita ba amma Allah na gani zuciyarta na fargaba kan lamarin nan.
"ki je ki samu yardarsa in har ya amince nima na amince".
Tana gama fadin haka da sauri ta kwace kanta ta fice daga cikin dakin zuciyarta da kwanyarta sai hayaki suke yi kamar za su kama da wuta duniyar take ji tana juya mata kafafuwanta take ji suna kokarin zubda ita ga wani zafi da take ji tun daga kasan ruhinta har zuciyarta komai kallon sa take yi kamar a mafarki ba gaske ba laɓɓanta take turawa cikin baki tana cizawa gami da runtse idanuwa.
Dafe kanta Mariya tayi gami da jan kafafuwanta da take jin su ita ma suna kokarin zubda ita kasa ga wani hayaniya da take ji a kwanyarta zuciyarta take ji tana harbawa da sauri-sauri idanuwanta a runtse ta isa bakin gadon ta zauna tana faman fadin.
"Yaa Hayyu Yaa Kayyum".
Numfashi take fiddawa a hankali zuciyarta na kara mikata wani mataki abin da tayi ne a yanzu take jin wani banbarakwai ji take yi kamar ba gaske ba ji take yi kamar cikin barcinta ne komai ke faruwa girgiza kai ta shiga yi kafun ta buÉ—e idanuwanta wanda suka gajiya da kaÉ—awa sosai zuwa ja murmushi ta saki gami da rufe fuskarta da tafukan hannayenta ta fada kan gadon ta baya.
Tunanin ta yarda zata fuskanci Dr.Aqeel take yi ba ta san ta yarda zai dauki maganar ba in ta je masa da ita bata san duban da zai yi mata ba akan wannan maganar anya ba zai ce ta yaudare shi ba anya ba zai ce ta ci amanarsa ba anya ba zai ce tayi masa BUTULCI ba?
Tunanin da take ta faman yi kenan zuciyarta kuma ta kasu kashi biyu bangare daya na bata kwarin gwuiwar tunkararsa dayan barin kuma yana tsoratar da ita yanayin da za su kwashe da Dr.Aqeel sosai ta ji ko ina na jikinta yana sanya kwanyarta na kara rikicewa da rigimar da zuciyarta ke hango mata za su kwasa da Dr.Aqeel a maganar nan ya kamata tayi wani tunani dole ne ta nemo hanyar da da zata samawar kanta mafita sannan ta samu cikar fatanta da burinta.
*******
Kai kawo kawai take yi tsakiyar dakin gabadaya ta hargitse yarda ka san wacce ta kwato kanta daga gidan mahaukata hannayenta saman kai sai yamutsa sumar kan ta take yi lokaci-lokaci take tsayawa tana jan numfashi tun da ta dawo gida ta rasa gane kanta maganganun Mariya ne kawai ke yi mata safa da marwa gabadaya take jin kwanyarta na kamawa da wuta ga zuciyarta na ta faman kokarin fallewa da gudu daga kirjinta tashin hankalinta na daÉ—uwa ji take yi gabadaya duniyar na sauya mata ji take yi kamar ba ita ba.
Saitin katon Mirrow da ke dakin ta isa ta tsaya tana kallon kanta ta cikinsa l fuskarta take shafawa tana runtse idanu gani take yi kamar ba ita ba gani take yi kamar wata Baseerar aka ajje aka dauke ta ainihin.
'Ta ya ya za ta so Dr.Aqeel bayan sun taba soyayya da ƙawarta aminiyarta ta kut-da-kut anya kuwa zata iya zuciyarta take ji kamar ba zata amince ba ji take yi kamar zaman kishi za su yi da Mariya ji take yi kamar in ta amince Mariya zata dauke a maciyar amana a gareta'.
Zuciyarta ce take ta faman dauko mata wannan maganganun suna kara rikita mata lissafi kofar dakin da taji an taba ne ya sanyata saurin juyawa Yah Tareeq ne ya shigo ganin yanayin da take ya sanya shi saurin isowa gareta yana yi mata kallon tuhuma.
"Me ke damun ki Sister?".
Ya fadi yana kokarin riko hannunta da sauri ta ja da baya dafe da kai ta zauna bakin gado tana mai da numfashi harÉ—e hannaye yayi a kirjinsa yana dubanta cikin wani irin yanayi kafun ya isa kusa da ita ya zauna kan loka din kusa da gadon.
"Tambayarki nake me ke damun ki kin yi mani shiru".
"Yah Tareeq bana jin dadi ne don Allah ka yi shiru bana son surutu".
Da mamaki ya dube ta ganin yanayin da take ciki ya tabbatar masa da gaskiyar abin da tace mikewa yayi yana kokarin fita har ya kai bakin kofa sai kuma ya tsaya gami da juyowa ya dube ta ita ma shi take duba dawowa yayi da baya hakan ya sanyata runtse idanu so take yi ya fita so take yi ta zauna ita kadai zaman kadaici take so kwanyarta take so ta sauke daga hayakin da take yi tana bukatar zaman ita kadai domin samun mafita akan wannan Bahagon lamarin da yake kokarin rikita mata lissafin rayuwa.
Kusa da ita ya zo ya zauna bata ce dashi komai ba har zuwa lokacin idanuwanta a rufe suke tana faman jan numfashi da sauri-sauri.
"Sister wai shin ya maganar nan ta mu ne har yanzu ba ki ce dani komai ba lokaci tafiya yake yi?".
Duban sa tayi ta gefe idanuwanta a zazzare ji take yi kamar ta kwala ihu don haushin abin da yake cewa da ita so yake yi ya sake rikita mata lissafi bayan tashin hankalin da take ciki laɓɓanta ta tura cikin baki ta ciza da karfi har sai da ta dan saki kara ta dube shi sosai sai fama gyaɗa kai take yi.
"Yah Tareeq ka san me nake so da kai?".
Girgiza yayi cikin mutuwa jiki ganin yarda tayi masa maganar.
"Ka taimawa kan ka ka taimaka min ka bar maganar nan don ba zata taba yuwu ba ne Yah Tareeq kayi hakuri ka je ka nemi wata matar amma ba Mariya ba don a halin da ake yanzu bana tunanin za ta iya dubanka har ta anshi tayin ka in har ba so kake yi abubuwa su lalace ba".
Zaro idanu yayi waje sosai gami da mikewa cikin hanzari ya shiga kokarin magana amma Baseera ta dakatar dashi bayan ta mike idanuwanta sun kara kaÉ—awa sun yi jajir.
"Don Allah na roke ka Yah Tareeq wallahi tallahi abi nan ba zai taba yuwuwa ba kawai bata lokacin mu za muyi sannan kuma kayi dakon son da ba zai yi maka amfani ba sai ma matsala da zai ja maka kawai kayi hakuri ka nemi wata ZABIN ALLAH shine kawai mafita".
Tana gama fadin haka ta koma ragwaf! ta zauna dafe kansa yayi da yaji yana juya masa kamar zai zubda shi ya shiga ambaton Allah a hankali ya fara jin saukin zafin zuciyarsa kallon Baseera yayi yanayin da yake ganinta a ciki ya tabbatar masa da abin da take gaya masa da sauri yaja jiki yana hada hanya ya fice daga cikin dakin dagowa tayi ta dube shi bayan taji alamun ficewarsa ta girgiza kai ta koma ta kwanta....
*KAMALA MINNA*😘😘😘😘