UKU-BALA'I 72

UKU BALA'I
   NA.
    KAMALA MINNA.

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.
  BABI NA SABA'IN DA BIYU.
    *BAYAN WANI LOKACI...*
Sosai take kuka ta mike kan kafafuwanta gabadaya take jin jikinta wani iri, ga wani zafi da radadi dake jinsa a duk wata gaɓa ta jikinta nayi mata, bata taba zaton muguntar Huzaif ta kai haka ba, bata taba zaton rashin imanin nasa ya kai haka ba, ta yi zaton zaman na nasu zai sauya tayi zaton zasu fahimci juna, ashe ba haka bane duk inda take zaton Huzaif ya shalle tunaninta da nazarinta.
 A hankali ta shiga dafa bango tana jan kafafuwanta har ta isa kofar toilet ta buÉ—e ta shiga, zuciyarta take ji tana kuna da suya ji take yi kamar zuciyar zata faso son sa na nan har yanzu ba abin da ya ragu, sai ma kara buÉ—ewa da zuciyarta take yi da son sa.
 Ruwa mai dumi ta cika kwarmin wanka da shi sannan ta shiga sosai zafin ke ratsata ta ko ina, sosai take jin zafin na kaiwa duk wani sashi da gurbi da take jin yana ansawa.
 Runtse idanu tayi lokaci guda ta buÉ—e, sosai take jin rashin nadama akan son Huzaif alkawari tayi ko da yana yankar naman jikinta zata zauna dashi har karshen numfashinta, ta gwamma ce ta ji azabar gidan miji da dai ta koma waccan bakin gidan na Goggo Marka, ta koyi rayuwa tun daga irin cin zarafi da cin mutunci da gori da ta ake mata a wannan gidan ta tabbata in ba tayi wasa ba su Assama'u so suke su fidda ita, amma zata jajirce zata nemi gafarar Allah ya yafe mata laifukanta ta sani abubuwan da ta aikata ne yake bibiyarta ba komai ba a duniyar rayuwarta.
 Ta jima kafun ta tsane jikinta ta fito sam ba ta lura da mutum dake tsaye bakin kofa ba yana ta faman sakar mata wani irin kallo, sai da ta zauna bakin gadonta sannan ta lura dashi gabanta taji ya yanke ya fadi runtse idanu tayi tana tuna artabun da suka kwasa a jiya zuwa yau, goshin sa ta kalla kinkimeman bandeji ta gani runtse idanu tayi tana tuna fadawa da Huzaif yayi jikin Mirrow ya fasa masa goshi, sosai ya yanke shi don jiya ta ga ta shin hankali bata taba zaton Huzaif zai rayuwa ba, musamman irin jinin da ta ga ya zubar da irin sambatun da yake yi.
A hankali ya shiga takowa ya iso gareta gefenta ya zauna fuskarta da wani irin yanayi mai cike da alamun nadama idanuwansa sun kada sunyi jajir gabanta ne ya yanke ya fadi sosai take kokwanto akan abin take hangowa cikin idanuwansa tausayi abin ya bata mamaki.
*****
Hajiya Layla ce ta dubi Khairiyya dake zaune ta zabga tagumi LAMARIN DUNIYA gabadaya ya kara hargitsa mata lissafi, komai na duniyar take jin sa wani iri babu dadi, duk da a yanzu bata da wata matsala a rayuwarta wacce zata addabeta amma in ta tuna wacece ita sai taji zuciyarta na kuna gami da suya, hawaye suka zirnano mata a hankali ta dauke su tana ajiyar zuciya.
"Khairiyya!".
 Hajiya Layla ta fadi da sauti a muryarta mai cike da rarrashi da karfafa mata gwiwa akan lamarin rayuwar da suke ciki a yanzu, kusa da ita ta karasa tana toshe bakinta jin tari na kokarin sarke ta, a hankali ta zauna tana mai yatsine fuska alamun akwai abin da ke damunta na rashin jindadi.
"Haba mana Khairiyya. bana so nake ganin ki cikin wannan yanayin gabadaya sai naji babu dadi, na rokeki ki mai da komai ba komai ba duba za kiyi da baya da irin rayuwar da mu kasance da kuma yanzu, ai abubuwa sun yi sauki kuma kisan ita rayuwa ba ko yaushe take zama daidai ba, kuma ba wani bawa a doron duniyar nan da zai ce miki ya dawwama a farinciki da kwanciyar hankali a rayuwa kowa da yarda Allah ya ke kunsa masa matsalarsa, sai dai ace ta wani bawan tafi ta wani".
Ta karashe tarin na kara sarke ta, da sauri Khairiyya ta dube ta cikin yanayi na tausayawa.
 "Maama kin sha maganinki kuwa?".
GyaÉ—a mata kai tayi gami da sakin murmushi kafun ta dafa kafaÉ—arta.
"Khairiyya Ina son mu sake zama na biyu dake, kuma ina so wannan zaman ya zama na karshe tsakanina dake, sannan ki sani ba zan tursasaki ba sannan ba zan yi miki dole b,a ni dai fata na kawai ki samu kwanciyar hankali ako ina kike shine BURINA sannan shi abin da na fi bukata a duniyar nan, Khairiyya so nake yi na zama sanadi na wanzuwar farin cikin ki har kashen numfashinmu a doron duniyar nan...".
 "Maamaa".
Khairiyya ta fadi da alamun rigima a muryarta, kafun ta juyo sosai ta fuskance ta tana bayyana wani kunshin murmushi, wanda ta san zai kara kwantarwa Hajiya Layla da hankali.
 "Ina jin ki faÉ—a mani menene zan anshe shi a duk yarda ya zo mani, zan yi AMANNA dashi BURINA a duniyar nan shine na faranta miki, kullum na ganki cikin farin ciki Maama kece farincikina kece komai a rayuwata kece kika zama tsanin ganin rayuwata ta gyaru...".
  Hawaye ne suka kwanranyo mata da sauri ta kau da kanta, tana jin yarda zuciyarta ke kara buÉ—ewa farinciki na kara samun gurbi a cikinta.
 "Maganar Alhaji Abdulwahaab Khairiyya ina muka kwana?".
Ta fadi tana saka idanuwanta cikin na Khairiyya, so take yi ta hango gaskiya, so take yi ta gano in da Khairiyyar ta dosa da batun, so take yi ta ga yanayin ta ko na sauyi a yarda ta dauki maganar a yanzu.
Numfashi taja gami da fesarwa kafun ta mike kan kafafuwanta, zuciyarta take ji tana kara buÉ—ewa kaunar da Hajiya Layla take nuna mata bata san da mai zata saka mata ba, ta nuna mata so ta nuna mata kauna tayi tattalinta ta bata duk wani lokacinta, sannan ta bata farincikin daidai iyawarta ya kamata ita ma ta nuna mata godiyarta sannan ta anshi duk wani abu da ta zo dashi, hakan zai kara tabbatar wa Hajiya Layla da cewa sun zama UWA DA 'YA.
 "Maama na lura dai so kike yi ki samu suruki".
  Ta fadi fuskarta da murmushi ita ma Hajiya Layla murmushi take yi kafun ta mike tana faÉ—ar.
 "Ba suruki kadai ba har da jikokina nake so na gani, kafun lokacina yayi so nake yi ni dake ki saman mana DANGI da zuri'a, zan yi alfahari da hakan sannan ko na mutu zan san nima ina da dangi".
Ta karashe da kwalla a idanuwanta.
 "ki anshe shi a matsayin miji na san Alhaji Abdulwahaab zai rike ki a yarda kike zai kula min dake, zai tattale ki zai zama MIJIN MARAINIYA a gareki, na san ba zaki taba kokawa ba duk da dai an san DAN ADAM ajizi ne, amma a zuciyata fata nake ke da Alhaji Abdulwahaab ku zamo abu daya har a gidan aljanna".
 "Shikenan Maama nifa wannan kukan naki ne bana so, Allah ki dai batun Alhaji Abdulwahaab kuma ai tuni labari ya sauya kawai fadi miki ne ban yi ba".
Zaro idanu Hajiya Layla tayi cikin alamun mamaki, kafun ta kai wa Khairiyya dukan wasa ta goce.
 "Ja'ira dama kallona kawai kike yi, ina kidina ina rawa ta ko? Allah ya shirya min ke ni nan na saki baki ina cewa sai na hada miki da tsayuwar dare ayi auren nan, ashe tuni kin mai dani wata kakarki to ai shikenan Allah yasa hakan shine yafi zama alheri a garemu ga baki daya, Allah yasa fatan da muke ya tabbata Allah ya kau da duk wata fitina da abin ki Allah ya kare miki rayuwa 'yata Allah ya kawo zuri'a tagari kiyi ta haifar mani tagwaye".
 Ta karashe tana goge hawayen da suke zubo mata ta jawo Khairiyya jikinta ta rungumeta sosai suke jin wata natsuwa da kwanciyar hankali na wanzuwa garesu.
 "Ameen Yaa Rabbi Maama na".
Khairiyya ta ansa muryarta na rawa.
******
Da Sallama ya shigo cikin gidan, yana bin duk wata kusurwa da kallo yarda gidan ya dawo tsaf! komai ya zama sabo zuciyarsa yake ji tana kara buÉ—ewa da farinciki gami da kwanciyar hankali, ba abin da zai ce sai godiya ga Allah da kuma Dr.Karami da ya zama sanadin samun waraka a rayuwarsu duban jikinsa yayi kafun ya sake duban gidan kwalla suka tarun masa kafun ya dauke su, a hankali ya shiga takawa yana isa dakin Umma, daga labulan yayi bakin sa da Sallama.
Zaune take gabanta da katuwar roba mai cike da CAKE tana lissafawa jin sallamar maigidan ne ya sanyata tsagaitawa, ta ansa sallama tana kokarin mikewa ta anso kayan hannunsa ya iso da sauri yana fadin.
 "Matar nan kin zama Hajiya fa Kasuwancin nan ya anshe ki sosai kin yiwa 'yata wayo ita da koya ke da karbe sana'ar".
Murmushi tayi kafun tace.
 "Yo da zaman banza ai gwanda aiki kishiya kuma ai bani nace ta bar mani ba kuma ko ma kace na anshe mata ai ba gida daya muke ba ita za ta iyayin nata a gidan auren ta kowa ya ci da rabon sa".
Zama yayi yana mai fadin.
 "To Allah ya dafa mana kin ga na shagon ma da kika kai shekaran jiya kusan karewa na lura Cake din nan yana karbuwa sosai wajan jama'a da mutum yaji cikin sa yana masa yaÆ™i sai ya zo ya hada da lemo sai ki ga ya dawo hayyacinsa".
Murmushi tayi batare da ta kara cewa komai ba, amma zuciyarta tana goÉ—ewa Allah tana shiwa Dr.Karami Albarka yarda ya fiddo dasu daga cikin kangin rayuwa ya baiwa mijinta jali ya buÉ—e shagon kayan bukata na rayuwa gashi ita ma sanadin karatun 'yarta ta samu sana'ar yi ba abin da zata cewa Allah sai godiya da fatan karin kwanciyar hankali daga gareshi.
 "Wai ina karya jali yake ne?".
Ya tambaya yana murmushi, dubansa tayi.
 "Au kai ma Mariya ta bar maka sara ko É—an nawa ne karya jali ai yanzu na uwarsa ne ko ya karya ba damuwa wata rana shi zai daura...yana can ya tafi Islamiyya".
Dakin ne ya dau shiru na dan lokaci, kafun Bello ya ja dogon numfashi ya dubi Umma.
 "kisan mi ina labarin yan matan nan da nace miki mun hadu da su wajan mutanan nan da suke garkuwa da mutane?".
Umma ta gyaÉ—a kai tana gyara zamanta ya cigaba da fadin.
 "Yanzu a shagon Alhaji Adamu mai bulawus na gan su an nuna a talabjin ashe lokacin da na bar su tana da juna biyu shugaban tawagar na su shi yayi mata a cikin sauran yan matan ma akwai masu juna biyu duk sun haihuwa yau na ga shari'ar da aka yi musu yau aka yanke musu zaman gidan kaso na rai da rai duk kan su su kuma yan matan gwamnati ta dauki nauyin rayuwarsu saboda kin san garin na su an kone duka sannan duk an kashe iyayen su ba su da kowa ba su da komai yanzu naji tausayin su sosai".
Umma ta dauke hawayen da suka zubo mata domin ta jima tana tuna wannan labarin na mutanan da suka kama mata miji sannan da yan matan da ya bata labari akan su.
 "Allah ya sa iyakar wahalar rayuwarsu kenan Allah ya jibanci lamarin su su kuma wadannan mutane Allah yayi mana tsari da irin su ya kare mana rayuwa da ta yan uwanmu daga fadawa hannun su".
 "Ameen Ya Rabbi".
Ya ansa jiki a sanyaye yana mikewa.
 "Ka duba Jin Goggo fa don Allah Malam bai kamata ace kana mata haka ba, ita ma uwa ce a gareka duk wani abu da tayi maka na cutarwa ina rokon Alfarma ka yafe mata, rayuwar duniyar nan ba komai bane...".
 "Naji kuma ai ni tuni na yafe mata, kowa dai yayi na gari dan kan sa".
 "Malam don Allah ka manta komai a rayuwarka da tayi maka, ita ma ai tayi nadama ko halin da take a ciki yanzu yaci ace ka tausaya mata".
Bai sake fadin komai ba ya fice daga cikin dakin, tsayawa yayi yana kallon dakin Goggo Marka kamar ba zai je ba, sai kuma ya taka a hankali ya isa kofar dakin daga labule yayi can karshen gado ya hangota gabadaya ta gama yankwanewa idanuwanta a buÉ—e tarwai sai dai ba su da amfanin komai kusan watanni hudu kenan cutar MAKANTA ta lokaci guda ta kama ta tun da akayi wata iska kura ta shigar mata idanu shikenan ta makance kuma dama gashi tana faman da cutar hawan jini da tayi mata mugun kamu har ta kashe mata É“arin jiki tashima bata iyayi daga kwanciya sai kwanciya...
 *Kamala Minna*😘😘😘
Post a Comment (0)