MURNAR SALLAH KAMAR ALGAITA

MURNAR SALLAH KAMAR ALGAITA

A wannan rana ta sallah na riga nayi baran-baran da tuwo sa Rangyam, hakan yasa ake kirana da ƊAN TAWAYE! Amma da yake ina sambaɗar taliya kamar yadda nake sambaɗan cin-cin, hakan Yasa ake kirana da Mai FUSKA BIYU. Tsakanina da naman Kaji akwai soyayya mai ƙarfin gaske, hakan yasa ake kirana da SARKIN SOYAYYA! Watau in dai soyayyen nama ne, da zarar mun haɗu to fa shi ya kaɗe kenan, hakan yasa na zama HATSABIBI a gare shi.

Kada ku taɓa damuwa da irin surutun da zaku ji Akuyoyi suna yi a kaina, tsabar cinye namansu da nake yi ne yasa suke kirana da AZZALUMI. Shi kuwa naman sa komai taurin sa hakanan zan yi amfani da IZZAR MULKI wajen ganin na taune shi ba tare da jinkiri ba. A taƙaice dai abokai, duk masu tsoron taurin nama ni kawai ina ɗaukar su ne a matsayin HAMAGAWA! Ko da yake nasan in suka zama HORARRU zasu iya tafi da kowane gagararren nama, amma domin cimma wannan mataki nasan cewa dole sai sun je makarantar NINJAN KISA tukunna. Domin Ita wannan makaranta tayi ƙaurin suna wajen sauya halayyar mutane, hakan ya faru ne tun bayan da ta canja DOLAYE UKU suka koma 'YAN UKU sannan suka rankaya HANYAR MADARAS domin zuwa shagalin bikin salla tare da MACASKALI.

To kun ga saboda haka, a wannan Sallar naga cewa ya kamata nima in ɗan yiwa wasu kaji KISAN GILLA domin samun Nishaɗi irin na BABBAN YARO tunda nima dai JIKINA DA JINI. Kun san cewa NAMIJIN ZAKI baya tsoron DAMISA, amma tun bayan da na zamewa tunkiyoyi MAI TAƁARGAZA sai duk suka koma kirana da SHUGABA saboda sun fahimci cewa YAƘI DA RASHIN ADALCI yana buƙatar MAI GASKIYA, su kuma basu da shi. Saboda haka, in dai a fagen ɗiban girki ne, to ni ake yi wa laƙabi da MAI SUBURBUƊA. Na riga n zamewa agawagi Inuwar mutuwa don har ma kiran suke da MAI ADDA. Tsabar shiƙar da nake yiwa raguna a kowace sallah in tazo ne yasa tuni aka ƙaƙaba min sunan MASHEƘI

MAZGA, MAKIRCI, haɗa TARKO ko yin amfani da barazanar kaini GIDAN KURKUKU ba zasu hanani amsa sunana na MASHAHURI a fagen shan jar miya ba. Wai don a hanani shan miyar yasa fa suka cika mata BARKONO, basu san cewa ni tuni na shiga cikin CAKWALKWALIN CAKWAKIYAr daɗi ba bana ma ko jin zafin. Sai dama an ce MAKASHIN MAZA... Kun dai gane domin kuwa a wancan sallar na kasa rabewa tsakanin SIYASA DA AƘIDA har sai da JAMI'IN TSARO ya kawo min ɗauki, a wannan lokaci kuwa tuni na daɗe da ɗaukar fasahar BOTORAMI. Na dai gane kuskure na tunda BABBAN YAYA yayi min Nasiha don haka babu ni babu MAKAUNIYAR SOYAYYA, shi yasa a wannan Sallar na kauda kaina daga SOYAYYAR BEBAYE ko MAKAHON SO, na tsaya kawai a matsayin ƊAN BASAJA.

Dama can AKASI, aka samu na zama UBAN DABA LAMBA ƊAYA a soyayya saboda KADDARA ta riga fata, amma in zaka ji shawarata aboki, kada ka sake ka yi budurwa ranar sallah in kuwa ba haka ba to zaka shiga cikin TAWAGAR MAƘARYATA ba tare da ka ankara ba kuma daga baya azo ayi ta binka da SABABI! kai ni dai na gwammace in zama MAI MAZGA a wajen nama kamar yadda na zama MAI ZAFIN HANNU a wajen loma. Kai gara ma in zama MADAKIN ƘATTI ko SARKIN ASKA a fagen feɗe dabbobi daga fatun su. Don haka kowa ya saka ZOBEN SIHIRI, ya ɗauki MASHI don shirin TAFIYAR AJALI in yaso komai ta fanjama FANJAM. Amma kuyi hattara sa SANGAMI, GARUJE, TAƘADARI da kuma SOJA domin suna iya antayewa da ku zuwa BIRNIN TSAFI.

Nidai na Zama ZAKIN ZAKUNA mai cinye namuka.

<••••••••••••••••••••••••••••>
  ɧãımãŋ Kɧâŋ Řâééʂ  <••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter:  @HaimanRaees
Instagram: Haimanraees
Infohaiman999@gmail.com

Post a Comment (0)