INA SON AUREN USTAZIYA AMMA...

🧕🏻🧕🏻🧕🏻INA SON AUREN USTAZIYA, AMMA MATSALAR; SU BA SU IYA NUNA SOYAIYA DA KULAWA DA MIJI BA 🧕🏻🧕🏻🧕🏻!

_ Maza da dama suna fadin wannan maganar' magana ta gaskiya Inason Auren mace ustaziya amma matsala ta da su basu iya Soyayya ba sai kaje ka aure ta tayi ta sanya ma hijabi a cikin gida, ba ruwan ta da nuna Maka Soyayya ko tarairaya ka so kana bacci kana jin numfashin Matar ka a kusa da Kai Kaji ka kamar kana Aljannah ka samu nutsuwa da ni'ima ' amma ina sai ka juya sai kaganta can tana ta nafila da tasbihi alhali kai ma mijin ta hakkin ka na a kanta ko da ta sauke hakkin ubangijin ta matukar bata sauke naka ba to bata gama sauke hakkin ubangijin ta ba ! Ammä ina kana so ka samu nutsuwa Kaji ka kusa da ita ayi hira ayi dariya ayi bacci amma ina tana can tana ta nafila !

_Ka dawo gida ta kawo ma abinci tace ma Sannu da dawowa maimakon ta zauna kana ci tana taya ka zama ko ta baka koda loma biyu ne a baki ko uku' ko ma ta ciyar da Kai ' kokuwa ta zauna tayi kwalliya Mai fidda duk kyawun ta a fili kana kallon ta kana Cin abinci tana kara shiga maka rai' tayi kwalliya ta mulke jiki da Mai tayi ado ga Jan baki ga powder' kana kara jin tana shiga ranka kana kara sha'awar ta da son kasancewa da ita har abadan da marmarin ta tamkar ango da aka dawo da shi gida' Tana yima kallon soyayya da kyawawan idanuwan ta 'amma ina sai ta tashi ta fita waje ta kama wani aikin ko ta wuce daki taci gaba da karatu ko wani bincike baruwan ta ko taje ta kwanta shiru !

_Bayan kana da bukatar in ka dawo ayi maka Oyoyo da maganganun Soyayya masu dadi dasauran su' ko ma ba ayi maka Oyoyo ba a tare ka cikin fara'a da shagwaba a riki hannun ka ana yima fara'a ' amma baruwan ta ko da kuna da yara , yara yanzu basa hana Soyayya karfe biyu ka dawo yara sun tafi Islamiyya sai Kusha Soyayya ku amma baruwan ta sai kace rayuwar da bana aure ba !

_kana taba ta kuwa da wani maganar sai ta jawo maka aya ko hadisi, Kai kuma ka aure ta ne kana ganin irinta itace cikakkiyar mace tagari Aljannah duniya ga ta da karatun Al'qur ani gata da hadisi ga fiqhu gashi zata nuna ma Soyayya, amma ina sai tayi tama nuku nuku kazamo mai aure amma kamar Mara aure' sai kace baka da aure to Meye amfanin Auren in ba Soyayya da kulawa da tarairaya' ai in dai tuwo ne da ruwan zafi da Sannu da dawowa mama da qannen ka suna yi maka' ita ta hana ka jindadi ta hana kanta !

_Ya ke yar uwa ta mai daraja Kamila mumina ustaziya shin kin manta Annabi Muhammad (SAW) irin soyayyar da yake da matan sa, shin baki san cewa da zaki zamo kin sauke hakkin ubangijin ki gabadaya in har baki sauke namijin ki ba akwai kura a kanki baki gama sauke hakkin ubangijin ki ba ? Lallai in kina da irin halin da na ambata a saman rubutu na to lallai kiyi saurin canjawa ya ke ustaziya mace tagari Aljannah duniya !

_Shin Rasheedah Bintu Abeebakar ta Fadi gaskiya ?in akwai Mai niyyar bada Shawara Ku bada shawarwari ku !

_Mu hadu a rubutu na gabah ...............................!

✍Rasheedah Bintu Abeebakar Mubi (daughter of Islam)
Post a Comment (0)