SARKIN SARAKAI BOOK 2. 01
BAYAN SARKI sahibul hairi ya sami karayar zuci bisa burin dake gabansa na zama sarkin sarakai a cikin dakin maridai saiya sake bajewa a kasa yana mai cigaba da tunanin rayuwar daya tsinci kansa a ciki. Sahibul hairi ya tuno da irin bakaken maganganun da sauran sarakuna abokansa suke aiko masa dasu gamida habaici da gori akan cewa' ya talauce bashi da cin yau bare na gobe kuma bashi da lafiya tunda ya kasa aure. Ya sake tunowa da yadda ya baro kasarsa bayan ya baiyana sirrin abinda ya fito nema kuma kowa ya sani haka kuma ya tuno da irin wahalar da ya sha a cikin wadannan dakuna biyu dake karkashin kasa a cikin masarautar sarki barusa koda yazo nan a tunaninsa sai zuciyarsa ta kama tafarfasa nan take yaji wani irin kwarin gwiwa ya shigeshi dukkan tsoro da fargaba suka yaye daga cikin zuciyarsa kawai saiya mike tsaye ya tunkari kofar da zata shigar dashi izuwa daki na uku.
Cikin zafin nama ya banke kofar da karfin tsiya take kofar ta rufta ciki ta fadi kasa koda yayi arba da abindake cikin dakin saiya kame tamkar gunki saboda tsananin firgita ba wani abu bane sarki sahibul hairi yayi arba dashi a cikin wannan daki na uku ba face wata murtukekiyar macijiya mai kawuna dari da daya idan macijiyar ta bude bakunanta duka babu abinda mutum ke gani a ciki face kibiyoyin wuta haka kuma a cikin kowanne baki akwai wani irin zarkalelen harshe mai tsananin karfi tamkar zabira kowanne kai guda daya na macijiyar yakai kamu dari haka shima wannan haske dake cikin bakin. Sa adda macijiyar mai kawuna dari da dayataga sahibul hairi ya kame a gabanta tamkar gunki sai itama ta tsaya cak tana kallonsa kawai jira take yayi kyakkyawan motsi ta kaddamar dashi tsawon dakiku sittin dayansu bai motsa ba sarki sahibul hairi ya san cewa bai isa ya koma da baya ba haka kuma bai isa ya wuce gaba ba don haka ya tabbatar da cewa yana cikin TSAKA MAI WUYA domin gabansa tsinine bayansa kuma siyaki daga can sai wata zuciyar tace dashi'' Kai jarumi uban jarumai ita fa masifa kafin tazo ne ake gudunta amma idan ta riga tazo saidai a rungumeta ayi daya daga cikin biyu wato ko kai ko ita' koda gama wannan tunani sai sahibul hairi yayi kukan kura ya afkawa macijiyar da nufin ya dankara mata sara nan take ta mako masa kanta guda ya makashi da jikin bango saboda karfin dukan saida bangon dakin ya burma ya fitar da shatar gaba daya surar jikinsa ya manne a cikin ginin tsananin zafi da zugin da yaji kuwa sai da jiri ya debeshi yaga taurarin wuya a idonsa koda macijiyar taga ya manne a cikin garu saita jefa jelarta a karo na biyu ta fincikoshi da karfin tsiya sannan ta fara kanannade shi saita matse shita ragargaza kasusuwan jikinsa. Tun a farkon lokacinda macijiyar ta fara kanannadeshi sai yaji ya matsu ainun tamkar an daureshi da sarkar karfe murtukekiya nan fa hankalinsa ya dugunzuma domin ya tabbatar da cewa idan fa macijiyar nan ta gama kanannade shi mutuwa zaiyi don kashin dake jikinsa saiya karye hakika wata masifar na iya sa mutum ya yi abinda bai taba tsammanin cewa zai iya ba a dai dai lokacinda macijiyar ke daf da gama kanannade wuyan sahibul hairi ne kawai saiya takarkare iya karfinsa ya buda jikin macijiyar da karfin tsiya a wannan lokaci inda mutum na nan yaga yanda kwanjin sahibul hairi ya ciko da yadda jijiyoyin jikinsa suka tattashi sukayi burdin burdin sai yayi tsammanin cewa jikin dutse gareshi karfin buda jikin macijiyar ne yasa macijiyar taji kamar za a yagata ba shiri ta warware jikinta daga nasa ta sake shi amma kafin yayi wani yunkuri ta bude bakunanta duk ta fara watso masa kibiyoyin wuta bisa mamaki sai yaga duk kibiyar data sauka a jikinsa saita kasa hudashi ta fadi kasa kawai abinda bai sani ba shine wannan naman zakin da yaci a wancan dakin na farko shine ya bashi wannan kariya amma ba karfin sihirinsa ba lokacinda macijiyar taga cewa kibiyoyinta na wuta sun kasa yin tasiri a kan sahibul hairi saita kara fito da harsunanta guda dari da daya duka ta watso masa su da nufin ta daddatsashi gunduwa gunduwa duk harshein da ya bugi jikinsa sai kaji kal kamar karfe da karfe ne suka hadu amma ko kwarzane jikinsa baiyi ba nan fa aka ci gaba da masifaffen fada ya zamana cewa macijiyar na dukan jikin sahibul hairi da harsunanta shi kuma yana saran harsunan da takobin hannunsa sai da aka shafe sa'a guda ana wannan artabu amma dayansu bai sami nasara ba da kanta macijiyar taja da baya ta tsaya cak aka ci gaba da kallon kallo ita tana huci shikuma yana haki hakika wannan macijiyar tasan cewa yau ta hadu da iblishin bil adama domin a tarihin rayuwarta tunda aka ajiyeta acikin wannan daki fiye da shekaru talatin baya ko mutum dubu aka watso mata a cikin dakika guda take hallaka su gaba daya amma yau ga bil adama daya kwal ya gagareta lokaci guda suka sake afkowa juna wannan karon dai kokarin da macijiyar takeyi shine ta hadiye sarki sahibul hairi da daya daga cikin kawunan nata koda ya fuskanci manufarta saiyayi ta zulle da gocewa yana kai mata duka hannu da kafa gami da kai mata sara.......
Zan Cigaba Insha Allah
Very good
ReplyDelete