TARIHIN JARUMI RAM CHARAN

°••°•°•°TARIHIN•JARUMAN•INDIA°•°•°••°
TARIHIN JARUMI "RAM CHARAN
•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•
Date:-Wed-30-Oct-2019
©opyRight By:-Najibkhan NB Srk
Daga:-ZAUREN INDIA™
•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•
[GUNDARIN TARIHINSA]
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Da Farko Sunan Sa Na Gaskiya "Konidela Ram Charan Tej",Wanda Akewa LaQabi Da "Cherry,Mega Power".Kamar Yanda Muka Sani 'Ram Charan' Nagartaccen Jarumi Ne Wanda Ya Shahara Tareda Ga Hurta A Fannoni Kala-Kala Acikin Fina-Finan Sa,Musamman Sashin Soyayya,Rawa,Fada Da Maka Mantan Su.Bisa Yanda Alkaliman Binciken Kan Nazarin Da Masana Kimiyyar Nazarta Yan Adam,Sun Bayyanawa Mujiyar Tamu Cewa:Jarumin Dogo Ne Yana Da K'iba Matsakai Ciya,Sannan Fasalin Launin Idon Sa Ruwan Kasa Ne Wato "Brown" Shi Kuma Gashin Sa Ya Kasanxe "Ruwan Kasa Mai Haske" Wanda A Yaren Bature Ake Kiran Launin Kalar Da "Light Brown".
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
[RANAR HAIHUWA]
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
Jarumi 'Ram Charan' An Haife Shi Ne A Ranar 27 Ga Watan "March" A Cikin Shekarar "Alif Dari Tara Da Tamanin Da Biyar" Wato 1985,Inda A Lissafin Namba Shekarun Sa Suka Kama Kimanin Shekara 34Yrs Da Zuwa Duniya.Garin "Chennai, Tamil Nadu, Sune Garuruwan Da Suka Zamto Mahaifar Sa.Inda Kuma A Yanzu Jarumin Yana Zaune A Yankin "Hyderabad, Telangana" Dake Qasar India.Babban Jarumi "Ram Charan" Kamar Yanda Mujallu Da Jaridu Suka Bayyana Su Nan Makarantar Da Ya Fara Kasancewa A Ciki Itace; "Padma Seshadri Bala Bhavan School" Wacce Take Cikin Yankin "Chennai",Sai Dai Kash Bisa Yanda Sakamakon Bincikin Mu Ya Nuna Ba'a Bayyana Mana Sunan "Kwaleji/College" Da Yayi Ba Saboda Na'uwar Ta Samana (College Not Known),Amma Abiyo Mu Nan Gaba Insha Allah Za'a Jimu Dauke Da Cikakken Bayani Kan Makarantun Da Yayi Baki Daya.Bari Kapcen Namu Yayi Durar Mikiya Kan Ahalinsa,To Da Farko Sunan Mahaifin "Chiranjeevi" Ya Kasance Babban Jarumi Wanda Sunan Sa Ya Zagaya Duniya Yayinda Ludayin Sa Yake Kan Ganiyar Sa Acikin "Kunu".Sannan Idan Ba'a Manta Ba Akwai Sabon Film Din Da Ya Fita Kwanan Nan Mai Suna "Syee Ra Narasimha Reddy" Film Ne Wanda Mahaifin 'Ram Charan' Ya JagOranta Inda Shi Kuma 'Dan Nasa Mai Suna "Cherry" Ya Dauki Nauyi Sa.Ita Kuma Mahaifiyar Sa Sunan Ta "Surekha Konidela".Sa'an Nan Yana Da Yan Uwa Mata Guda Biyu Akwai Yayar Sa Mai Suna "Sushmita" Sai Kuma Kanwarta Wacce Ake Mata Kafcen Atisayen LaQabi Da "Srija".Sannan Addinin "Hindu" Shi Ne Addinin Dayai Imani Da Shi Da Kuma Bada Dukkan Yardar Sa Akan Sa.
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
[ABUBUWAN DA YAFI SO]
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
Daga Cikin Al'amarin Da Jarumin Yafi So Nafarko Akwai Girki,Karatu,Tseren Doki.A Fannin Abinci Kuwa "Biriyani" Shi Ne Abinda Yafi Burge Shi.Sai Kuma A Jarumai Ya Bayyanawa Manema Labarai Cewa "Tom Hanks" Shi Ne Jarumin Dayafi Burge Shi,Inda A Jarumai Mata Yabada Sanarwar Cewa:Babbar Jarumar Nan Mai Suna "Sridevi" Itace Jaruma Mafi Soyuwa A Gurin Sa.Har'ila Yau Game Da Fina-Finan Da Sukafi Burge Shi Na Farko Shi Ne "Gladiator" Sai "Khaidi".Daga Karshe Kuma Jarumin Ya Kara Da Cewa Kasar "New Zealand" Itace Kasar Da Yafi Muradi Da Kuma Son Zuwa Akoda Yaushe,Sai Kuma Kasar 'London'.
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
[GAMEDA FIM DIN DAYA FARA]
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
Fim Din Da "Ram Charan" Yafara Yi Shi Ne “Chirutha” Wanda Masana'antar "Telugu Movie" Suka Ja Ragamar Shirya Masa Shi,Duk Da Fim Din Ya Zamto "Flop" Wanda Ya Fadi Hakan Be Ko Raunana Masa Zuciya Ba Ko Karayar Da Dagiyar Sa Ta Son Yin Fim Kuma Yasamu Karbuwa Tareda Tura Darasin Da Yake Muradi.Bayan Fim Din Sa Na Farko "Chirutha" Wanda Akayi Shi A Shekarar 2007 Sai Kuma Aka Shirya Masa Fim Mai Suna “Magadheera” Wanda Ya Zamto Fim Mafi Girma Da Shahara A Idon Duniya Da Kuma Kansa Shi Jarumin Saboda Zamu Iya Cewa Shi Ne Sanadin Nasarar Sa,Duba Da Yanda Ya Girgiza Al'umma Da Kuma Irin Salon Kafcen Daya Qunsa.Haka Zalika Shi Ne Fim Wanda Akai Kwanaki "757" Ana Haska Shi A Gidan Kallo Na Indiya Wato "Cinema".
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
[BAYANI AKAN DANGINSA]
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
Jarumi Ram Charan Yazo Ne A Matsayin Bangon Bayan Mahaifin Sa Ma'ana: Tamkar Magaji Ne Na Mahaifin Sa Idan Mukai La'akari Da Irin Gudun Mawar Da Kuma Jajurcewar Da Mahaifinsa "Chiranjeevi" Yayi A Lokacin Su Na Baya,Kuma Har Yanzu Ana Damawa Da Mahaifin Nasa A Duniyar Fina-Finan Indiya.Zamu Iya Fasalta Jarumi "Chiranjeevi" Da Jarumi "Jackie Shroof" Saboda Jarumai Ne Wadanda Sukai Suna Da Shara Kuma Yanzu Zamanin Su Yaja Baya Kuma Ya'yan Su Yanzu Sun Taso Sun Shiga Harkar Film Da Kafar Dama Harma Yanzu Suna Kokarin Kere Iyawar Su Wacce Da Ita Suka Kafa Tarihi A Zamanin Su,Yanzu Dai Ina Nufin Jarumi "Tiger Shrooop" Da "Ram Charan" Suna Cikin Sahun Ya'yan Jaruman Da Sukai Tashe Kuma Ga Ya'yan Su Suma Suna Kan Tashen Su Wajen Ganin Sunayen Su Sun Karad'a Duniya Fiye Da Na Iyayen Nasu.Hakan Ba Karamin Abun Alfahari Bane A Tarihin Jaruman India Wato Uba Yayi Tashe Da Suna Sannan 'Dan Sama Yayi Fiye Da Shi.Idan Kuma Mukai Waiwaye Zuwa Kan Mazan Jiya WatO Jarumi "Amitabh Bachchan" Yana Daya Daga Cikin Jaruman Da Suka Shiga Cikin Kundin Tarihin Da Baya Gushewa A Duniya Bisa Irin Jajurcewa Da Kokari Tareda Gudun Mawar Da Yabawa Masana'antar "Bollywood",Amma Zamu Ga Cewa: 'Dan Sa Mai Suna "Abhishek Bachchan" Ba Wani Farin Jini Da Kuma Kwarewa Yake Da Ita Ba Wacce Har Za'ai Kokarin Kwatantashi Da Mahaifin Nasa,Wannan Kawai Lamari Ne Na Ubangiji.Baya Da Haka Shi Kuma Mahaifin Ram-Charan Wato 'Chiranjeevi' Shi Ma Mahaifin Sa Mai Suna "Allu Rama" Yakasan Ce Jarumi Ne A Fagen Ban Dariya Wato "Comedian" San Nan Kuma Yana Daya Daga Cikin Masu Fafutukar Yakin Kwato Yanciwa Kasar Su A Lokacin Baya.Rahotan Ni Sun Bayyana Cewa: Babban Jarumin Nan "Pawan Kalyan" Kawun "Ram" Ne Shi Kuma "Stylish Star AA" Wato "Allu Arjun" Dan Uwan Sa Ne Wato "Cousin.San Nan Jarumi Ram Charan Shi Ne Mamallakin Qungiyar Nan Da Ake Kira Da Suna (Ram Charan Hyderabad Polo Riding Club) Tim Ne Wanda Ya Hada Na Tseren Dokuna.Idan Abaya Ba'a Manta Ba Matar Da Ya Aura "Upasana Kamineni" Na'ambata Cewa; Mataimakiyar Shugaban Kungiyar "Apollo Charity" Sannan Kuma Babbar "Edita/Editor' Ce A Kamfanin Jaridar Nan Da Ake Kira Da "B Positive magazine".Mahaifin Sa Chiranjeevi Babban Masoyin Jarumi "Amitabh Bachchan" Ne A Saboda Haka Ne Yabbayanawa Duniya Cewa Baya Gajiya Da Kallon Jarumin,Sannan Kuma Chiranjeevi A Yanzu Haka Yana Kwatanta 'Dan Sa Ram Charan A Matsayin Jarumin Da Zai Maye Gurbin Jarumin Nasa "Amintabh Bachchan".Jarumi "Ram Charan" Yana Da Aure A Inda Ya Auri Wata Mata Mai Suna "Upasana Kamineni" Wacce Ta Kasance Mataimakiyar Shugaban Kungiyar Nan Da Ake Kira Da Suna (Apollo Charity).
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
[KARIN BAYANAI GAMEDA RAM CHARAN]
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
Kamar Yanda Na Labaranta Cewa: Jarumi Ram Charan Jarumi Ne Wanda Ya Shiga Cikin Manyan Jaruman India Sannan Mai Daukan Nauyi Fim Ne Daga Wata Kusurwar Kuwa Dan Rawa Ne Mai Ban Mamaki Baya Dahaka Yana Daya Daga Cikin Ma'aikatan "Telugu Cinema".Har Ila Yau Yana Daya Daga Cikin Gahurtattun Jarumai Wadanda Ake Ji Da Kuma Alfahari Da Su A "Tollywood" Bugu Da Kari Sunan Sa Yana Cikin Kundin Tarihin Manyan Mutane 100 Da Aka Fitar Da Jadawalin Su A Shekarar 2013.Jarumi Charan Yasamu Damar Lashe Kyautittika Da Dama Cikin Su Hadda Kyautar Nan Ta "Filmfare Awards" Guda Biyu Da Kuma "Nandi Awards" Guda Biyu,Kai Harma Da "CineMAA Awards" Guda Biyu,Sai Kuma "Santosham Best Actor Awards" Itama Guda Biyu.Kuma Ram 'Da Ne Ga Jarumi "Chiranjeevi" Da "Surekha",Charan Yafara Fim Din Sa Ne Tun A Shekarar 2007 A Cikin Wani Kayataccen Fim Mai Suna "Chirutha" Wanda YazO Da Salon Kafcen Fada Wanda A Shi Ne Yasamu Kyautar "Filmfire Awards" A Matsayin Sabon Jarumin Da Yafi Kowanne Jarumi A Wannan Shekara Duk Da Wannan Film Nasa Faduwa Yayi A Kasuwar Duniya Wato "Flop" Ne.Jarumi Ram Charan Da Jaruma Kajal Aggarwal Su Ne Manyan Jagororin Jaruman Da Suka Tafida Ragamar Film Din "Magadheera" Wanda Akayi Shi A 2009 A Inda Babban Mai Bada Umarnin Nan "S.S.Rajamouli" Ya Shirya Shi,Wanda Takai Cewa Wannan Fim Din Yana Daya Daga Cikin Manyan Fina-Finan Da Matakin Su Yakai Makura A Masana'antar Kudancin Indiya Wato "Telugu Films".Sannan Shine Fim Na Biyu Da Jarumi Ram Ya Samu Kyautar "Filmfire Awards" A Matsayin Jarumin Jarumai Na Masana'antar Telugu,Kuma Shi Ne Sular Daukakar Sa A Duniya.A Cikin Shekarar 2016,Jarumi Charan Ya Gina Masana'antar Fim Ta Kansa Wacce Ake Kira Da "Konidela Production Company",Sannan Yana Da Qungiya Ta Gudanar Da Tseren Sukuwar Dokuna A Garin Hyderabad Sunan Tim Din Nasa "Ram Charan Hyderabad Polo Riding Club".
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
[AUREN SA DA UPASANA KAMINENI]
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
Ram Charan Anyi Masa Baiko Da Upasana Kamineni, A Ranar 1 Ga Watan "December" Shekara Ta "2011".Sannam An Daura Musu Aure Ne Da Ita A Ranar 14 Ga Watan "June" 2012,A Wani Kayataccen Guri Da'ake Kiran Sa Da "Temple Trees Farm House".
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
[JERIN FINA-FINANTA]
Jarumi "Ram Charan" Yayi Fina-finai Da Dama Wadanda Sukai MatuQar Girgiza Masana'antar Tollywood Wasu Sun Samu Nasara Gagaruma Wasu Kuma Sun Fadi,Ga Jerin Rukunan Fina-Finan Sa Daya Kafta Sune Kamar Haka:
1. Chirutha 2007
2. Magadheera Kala 2009
3. Orange 2010
4. Racha 2012
5. Naayak 2013
6. Zanjeer
7. Thoofan
8. Yevadu 2014
9. Bruce Lee 2015
10. Dhruva 2016
11. Rangasthalam 2018
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
[FINA-FINAN DAYA DAU NAUYI]
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
Fina-Finan Da Yadauki Nauyin Su Kuwa Ga Jerin Jadawalin Sunayen Su Kamar Haka:
°•1. Khaidi No. 150 2017
•°2. Sye Raa Narasimha Reddy 2019
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
[JERIN KYAUTITTIKAN SA]
Jarumi "A
Charan" Ya Lashe Kyaututtuka Da Dama Wadanda Ga Jerin Jimmilar Wasu Daga Ciki:
.
*Filmfire Awards South*
2008 Filmfare Awards South Best Male Debut – South Chirutha Won
2010 Best Actor – Telugu Magadheera Won
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
*Nandi Awards*
2008 Nandi Awards Special Jury Award Chirutha Won
2010 Special Jury Award Magadheera Won
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
*South Indian International Movie Awards*
2019 South Indian International Movie Awards Best Actor – Telugu Rangasthalam Won
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
*Santosham Film Awards*
2010 Santosham Film Awards Best Actor Magadheera Won
2015 Best Actor Govindudu Andarivadele Won
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
*Ritz Icon Awards*
2016 Ritz Icon Awards Most Admired Celebrity Icon Award — Won
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
*Asiavision Awards*
2016 Asiavision Awards Youth Icon Of India — Won
2014 TSR – TV9 National Film Awards Best Hero Naayak Won
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
*CineMAA Awards*
2016 Special Jury Best Actor Award Dhruva Won [40]
2010 CineMAA Awards Best Actor – Male Magadheera Won
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
*Zee Cinema Awards*
2019 Zee Cinema Awards Best Actor in Leading Role – Male Rangasthalam Won
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
Kashhh..... Duka-Duka Anan Nakawo Karshen Wannan Tarihi,Ku Tara Wani Lokacin Domin Jina Dauke Da Wani Sabon Tarihin Acikin Wannan Shiri Na "TARIHIN JARUMAN INDIA" Wanda Kai Tsaye Yake Zuwa Daga Wannan Dan-Dali Na "ZAUREN INDIA" Bissalam.
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
©-2019•By:-Malamin Kimiyya Da Kapce.
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••

Post a Comment (0)