*HARAMCIN RUBUTA AYAR AL-KUR'ANI DA HARRUFANDA BANA LARABCI BA*
Wato *(Transliteration)*
.
✍
*Suleiman Yunusa Alkali*
.
Bayan godiya ga Allah da kuma salati ga Annabin mu Muhammad S.A.W, muna ķara godewa Allah da Ya bamu ikon haďuwa a wannan rubutu na biyu da mukayi alkawarin kawo kadan daga cikin ayoyinda Malluma suka kafa hujjah dasu wurin haramta yin *Transliteration* na ayoyin Al-Kur'ani.
.
1. إنا أنزلناه قرآنا عربيا لعلكم تعقلون. (سورة يوسف 2).
*Lallai Mun Sauke Al-kur'ani Da Yaren Larabci* (wanda idan kukabi karantarwarshi) *Tabbas zaku zamo cikin masu hankaltuwa* (Yusuf : 2).
2. نزل به الروح الأمين * على قلبك لتكون من المنذرين * بلسان عربي مبين. (الشعراء 193-195).
*Ruhi Amintacce* ( Mala'ika Jibrilu) *Ya Sauko dashi* (Alkur'ani), *A cikin zuciyarka* (Annabi Muhammad S.A.W) *Dan kazamo cikin Masu gargaďi* (Manzanni) *Da harshen larabci a bayyane* (Shu'ara'i 193-195).
.
3. إنا جعلناه قرآنا عربيا. (الزخرف 3).
*Lallai Mun Sanya Al'kur'ani* (ne) *a harshen larabci* (Zukhruf 3).
.
4. قرآنا عربيا غير ذي عوج... (الزمر 28).
*Abun karantawa ne* (Kur'ani) *Da larabci wanda ba ma'aboci karkata bane* (Zumar 28).
5. ولو جعلناه قرآنا أعجميا لقالوا لولا فصلت آياته...... (فصلت 44).
*Da Mun sanyashi* (Qur'ani) *Ya zamo abun karantawa ne da ajami* (Transliteration, ajami shine dukkan wani yare da ba larabci ba) *Wallahi da* (Kafirai da mubafukai) *sunce me yasa ba'a rarrabe ayoyin ba???* (Fussilat 44).
.
Waďannan sune kadan daga cikin ayoyinda suke nuna Allah aya saukar da Alkur'ani ne da larabci kuma dan a karanta shi a larabcen bada wani yaren na daban ba kamar yadda kowa yasan wannan.......
Da hakan ne Malluma suke ganin tabbas fa rubuta Alkur'ani da wata yaren daban ba wacce aka saukar da Littafin da itaba haramun ne saboda illoli masu yawan gaske wanda zamu kawo kadan daga cikinsu a rubuce-rubucen mu na gaba da izinin Allah amma ga misali;---
.
1. Babu yare me harafin ض kap duniya, to dan Allah wuraren da harafin yazo cikin Qur'ani me za'a saka a wurin yayi dedai da yadda Allah Ya saukar dashi???
A hausa dole (D) zaka saka wanda a larabce ze koma (د), kaga an bata ma'anar ayar kenan kai tsaye.
2. A larabce akwai qa'idojin tajweedi cikin karatun Alkur'ani kuma a hakan aka sauke littafin, to dan Allah a *Transliteration* yaya za'a rubuta su sautin *Idgami da Iqlabi da ikhfa'i* yaya za'ayi a gane su *Ra'un me zabi biyu da kuma hukunce-hukunce Naqal da Saktah da Imala???*.
Duk wannan baze yuwu ba, wanda kuma yake nuni akan cewa za'a karanta Qur'ani kenan da kurakurai waďanda zasu iya kai mutum ga halaka, garin niman lada yasamu zunubi.
Allah Ya kiyaye.
Anan zamu dasa aya sai rubutun mu nagaba zakuji mu ďauke da wasu hadisai da Malluman suka kafa hujjah dasu kuma akan haramcin yiwa Qur'ani *Transliteration*.
.
Allah Yasa Mudace Ya kuma bamu ikon zuwa koyan karatun Qur'ani dan mu karantashi yadda aka saukar dashi mu samu lad.