HARAMCIN RUBUTA ALƘUR'ANI DA TRANSLITERATION


*HARAMCIN RUBUTA AYAR ALKUR'ANI DA HARRUFANDA BANA LARABCI BA*
      
Wato *(Transliteration)*

FITOWA NA (3).
*Suleiman Yunusa Alkali*

Muna kara godewa Allah da Ya bamu ikon haďuwa a wannan darasi da muka masa take da *Haramcin Transliteration*, muna wa Annabi S.A.W salati da Ãlayensa da sahabbansa, sannan muna rokon Allah Ya temakemu cikin wannan aiki da muka ďauka.
.
       *Hadisai da Malluma suka kafa hujjah dasu akan wannan hukuncin sun haďa da:-*

1. عن أم المؤمنين، عائشة رضي الله عنها قالت: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
ﺍﻟﺬﻱ ﻳَﻘْﺮَﺃُ ﺍﻟﻘُﺮْﺁﻥَ، ﻭﻫﻮ ﺣﺎﻓِﻆٌ ﻟﻪ ﻣﻊ ﺍﻟﺴَّﻔَﺮَﺓِ ﺍﻟﻜِﺮﺍﻡِ ﺍﻟﺒَﺮَﺭَﺓِ، ﻭﻣَﺜَﻞُ ﺍﻟﺬﻱ ﻳَﻘْﺮَﺃُ، ﻭﻫﻮ ﻳَﺘَﻌﺎﻫَﺪُﻩُ، ﻭﻫﻮ ﻋﻠﻴﻪ ﺷَﺪِﻳﺪٌ ﻓَﻠَﻪُ ﺃﺟْﺮﺍﻥِ .
 ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ: 4937)
 ﺻﺤﻴﺢ ‏ﻣﺴﻠﻢ ‏( 798 ‏).

Daga Nana Aisha (R.A) tace: Manzon Allah S.A.W yace:---
Wanda yake karanta Alkur'ani kuma ya kware yana tare da mala'iku masu daraja *wanda kuma yake karanta Alkur'ani Yana in'ina yana bashi wahala to yanada lada biyu* (ladan juriya ko hakurin karatun da ladan ko wani harafi da ya karanta dedai).

(Bukhari 4937, Muslim 798)...

        Akwai qa'ida ta Usool da take cewa *لا يجوز تأخير البيان عند الحاجة* (Baya halasta a jinkirta bayani daga lokacin bukata).
       Yanzu idan muka duba hadisin zamu ga cewa Annabi (S.A.W) be umurci me shan wahala wurin koyan Qur'ani da ya rubuta da yarenshi dan ya iya ba, cewa yayi yanada lada biyu, wanda ke nuni akan cewa me shan wahala wurin koyan Qur'ani a larabce yayi hakuri kenan ya cigaba da koya da larabcin bawai yace ze rubuta da yarensa ba dan samun sauķi, domin kiyaye wannan ladan da Annabi S.A.W ya ambata.
       Domin kuwa Annabi (S.A.W) a kullun sauķi yake kawo wa Al'ummarsa, kunga dâ rubuta Qur'ani ba da larabci ba ya halasta da kawai sai yace (duk wanda ke ganin baze iya da larabcin ba ya rubuta da yarensa) amma kuma beyi hakan ba.
       Saboda haka, ba hujjah bane mutum yace ai shi baya gane rubutun ne da larabci sai an masa *Transliteration* (wai gashinan dan boko). Dolene ka nemi Mallami ya koyamaka kuma zaka iya da izinin Allah tunda har ka koyi Transliteration ka iya, domin daman shi Qur'ani sai da Mallami.
     Saboda haka da wannan hadisin ma kadai ya isa mutum ya guji rubuta Qur'ani da yarenda bana Qur'ani (larabci) ba, base ma an ambata masa illar yin hakan ba.

2. ﻋﻦ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ رضي الله عنه : ﻗﺎﻝ ﻟﻲ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ صلى اللخ عليه وسلم:--
 ﺃﻟﻖ ﺍﻟﺪﻭﺍﺓ، ﻭﺣﺮﻑ ﺍﻟﻘﻠﻢ، ﻭﺍﻧﺼﺐ ﺍﻟﺒﺎﺀ، ﻭﻓﺮﻕ ﺍﻟﺴﻴﻦ ، ﻭﻻ ﺗﻌﻮﺭ ﺍﻟﻤﻴﻢ ، ﻭﺣﺴﻦ ﺍﻟﻠﻪ ، ﻭﻣﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ، ﻭﺟﻮﺩ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ........
Daga Mu'awiya (R.A) yace;
Manzon Allah S.A.W yacemun:---
*Ka saka gefen sufi cikin Tawada* (Hakan yana temakawa ne wurin ķawata rubutu da sauķin rubutun da kuma kiyaye bakin alkalami) *Kuma ka karkata alkalami* (daide yanda zaka yi rubutun yayi kyau) *Kuma ka kafa ب* (ta yanda zaka banbantashi daga waninsa) *Kuma ka rarraba س* (wato waďannan hakoran nashi saboda ka banbantashi daga wani harafin) *Karka rufe م* (ma'ana karkayi shi kamar ●) *Ka kayata sunan Allah, ka sakawa الرحمن madda sannan ka kyautata الرحيم* (wato duk waďannan suna gyara rubutu da kuma bin qa'idodi).

ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺪﻳﻠﻤﻲ ﻭﺭﻭﻯ ﺑﻌﻀﻪ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻭﺫﻛﺮﻩ ﺍﻟﻘﺎﺿﻲ ﻋﻴﺎﺽ ﻓﻲ ﺍﻟﺸﻔﺎ ﻛﻤﺎ ﺫﻛﺮﻩ ﺁﺧﺮﻭﻥ ﻛﺎﻟﻘﺮﻃﺒﻲ ﻭﺍﻵﻟﻮﺳﻲ ﻭﺍﻟﻤﺘﻘﻲ ﺍﻟﻬﻨﺪﻱ ﻭﺍﻟﺴﻴﻮﻃي ﻭﻧﻘﻠﻪ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺤﻲ ﺍﻟﻔﺮﻣﺎﻭﻱ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺑﻪ ﺭﺳﻢ ﺍﻟﻤﺼﺤﻒ ﻭﻧﻘﻄﻪ ﺹ 66 )"
Al-dailamy da Tirmizi da Alqadi iyad duk sun kawo hadisin kamar yadda Ďabry ya kawo da Alusy da Muttaqy da Suyudi kamar yadda shima Abdulhayyi Alfarmawy ya kawo a littafinsa me takenan *Rubutun Alkur'ani Da ďigonsa p66*
.
      Wannan hadisin duk da rauninsa yana nuna cewa Annabine da kansa ya koyar da rubutun Alkur'ani kenan da larabci, to meyasa bazamu tsaya mu koyi rubutu da karanta rubutunda Annabine ya koyar da kansa ba???
     Bamu da wata hujjah na saba wannan sunnar domin kuwa rubutu dakuma karatun ajami *(Transliteration)* koyanshi akeyi, ba'a haifan mutum dashi amma kuma wai baze tsaya ya koyi karatun Qur'ani ba, ko so yake a haifeshi dashi ne oho....
.
3. حديث العرباض بن سارية رضي الله عنه الذي فيه:---
فعليكم بسنتي وسنة الخلفاء الراشدين المهديين، عضوا عليها بالنواجذ.....
أبو داود 4607. الترمذي 2676.
ابن ماجه 42.
Hadisin Irbaad dan Sãriyah (R.A) wanda a ciki Manzon Allah (S.A.W) yake cewa:----
*Ina Umurtarku da bin Sunnah ta da Sunnan Khalifofina shiryayyu masu shiryarwa, ku damķeta da turamen hakoranku........*
Abu Dawuda 4607.
Tirmizi 2676.
Ibn Majah 42.
       Tabbas wannan hadisin yana cikin hadisanda yakamata mu lura dasu kan wannan matsala domin kuwa *Qur'ani da rubutun larabci gabaki_ďayanshi a wuri ďaya Uthman bin Affan ne ya haďa kuma ya yaďashi* kuma yana cikin waďanda akace mubi sunnarsu sau da ķafa, to meyasa zamu juyamusu baya?
        Magana akan haďa Alkur'ani kam wannan Malluma sun nuna mana cewa tun lokacin Annabi (S.A.W) Qur'anin yana rubuce amma akan fatu ne da ganyayyaki da ķasusuwa wanda daga ķarshe sahabbai suka haďashi wuri ďaya musamman a zamanin Uthmanu dan Affan har ya tura zuwa sauran birane (R.A) shiyasa ake rubuta *بالرسم العثماني* wato (Da Rubutun Uthman)...
         Kuma da wannan rubutun larabcin ne na Qur'ani Malluma sukayi ijma'i wanda kuma haramun ne sabawa ijma'in Malluma kamar yanda wannan a bayyane yake........
.
           Waďannan sune kadan daga cikin hadisanda Malluman suka kafa hujjah dasu, kuma da yardar Allah a rubutu na gaba zamu fara naqalto muku ra'ayoyin magabata Mallamai akan wannan lamarin da izinin Allah.
.
Allah Ya Ķaramana temako akan koyan karatun Alkur'ani yadda aka saukar dashi da aiki dashi dan samun rabo me girma a gobe ķiyama.
Post a Comment (0)