HARAMCIN RUBUTA ALƘUR'ANI DA TRANSLITERATION 05


*HARAMCIN RUBUTA AYAR ALĶUR'ANI DA HARRUFANDA BANA LARABCI BA*

Wato *(Translietration)*.

Fitowa (5) kuma na karshe.
.
*Suleiman Yunusa Alkali*

Bayan godiya ga Allah dangane da temakonSa da Yamana baiwa dashi a rubuce-rubce da suka gabata, muna kara wa Annabin mu salati da Âlayensa da Sahabbansa da waďanda suka kyautata ayyukansu har zuwa ranan sakamako. (Allah Yasa damu cikinsu).
       Wannan shine rubutu na ķarshe akan wannan matsalar, bayan waďamcan da muka ambaci ayoyi da hadisa da maganganu na magaba faqihai (Malluman Fiqhu) da muhaddithai (Malluman Hadithi), yanzu kuma zamu bijiro muku da jam'iyyu na musulunci da majalisu na ilimi da fatawa waďanda suka kulla ijma'i akan hakan duk da cewa sunayensu kawai zamu ambata.
.
1. *Majalisar Manyan Malluma Dake Cikin Saudiyyah* tace:----
 Tabbas bayan naxari akan wannan lamari na *Transliteration* mun tabbatar da haramcin hakansa ta fuskoki kamar haka;---
       (a). Alkur'ani an saukar dashi da yaren larabcine kamar yadda Allah Ya ambata cikin ayoyi da dama kuma shiyasa ake cemasa *Alkur'ani*, idan kuma aka chanzashi zuwa wani yaren babu yadda za'ayi a kirashi *Alkur'ani* kuma a ilimance.
       (b). Lallaine an riga anyi ittifaki akan wannan Alkur'anin a larabce tun lokacin saukarsa har lokacinda Abubakar ya haďashi har lokacin Umar da Uthmanu (R.A), saboda haka sabamasa sabawa Sunnah ne ta mutanen farko.
        (c). Tabbas Harrufan Larabci sun sabawa sauran yarukan domin kuwa akwai harrufanda bazaka samesu cikin ko wace yare ba sai larabcin irinsu ض, hakan ya nuna cewa idan har akayi *Translation* dolene karatun ya chanza yakoma ba inda Allah Ya saukar dashi ba, hakan kuma zunubine babba (Allah Ya kiyaye).
          (d). Idan aka bar *Transliteration* ya ciga, to dolene abokan gaban musulunci su samu ďaman bata Alkur'ani ta gefen karantawa domin kuwa harrifan sauran yararrukan suna canza kamar yadda ya bayyana mana.
        (e). Tabbas ne idan aka cigaba da yin *Transliteration* na Alkur'ani to anbuďe wa Jama'ah hanyar wasa da littafin Allah kenan, wanda hakan ba dedai bane.
       (f). Idan aka bawa kowa daman yayi Transliteration, tabbas mutane zasu shagala dangane da koyan larabci wanda hakan ze iya kawo musu cikas a cikin ibadunsu na yau da kullun domin da larabcin suke bautan Ubangijinsu, sannan zasu dena fahimtar Addininsu domin kuwa larabcin ne maķullin fahimtarsu ga addini.
          Wannan shine, kuma datarwa daga Allah yake.
Allah Yayi daďin tsira ga Annabi Muhammadu da Âlayensa da Sahabbansa da kuma Aminci.


To jama'ah, wannan itace ittifaki da musulman duniya sukayi.
     Wani zece meyasa kace duk duniya bayan Majalisar Manyan Mallamai ne suka faďa a saudiyyah???
       Ehhh tabbas na faďi hakan ne saboda;----
    ** Sune Majalisun mu na fatawar ta duniya.
    ** Basu kadaine ba, ga sunayen waďanda suma sunyi ittifaki akan hakan kamar haka:----
__________________
1. Majalisar Faqihai dake cikin garin makkah.
2. Gidan Fatawa na cikin ķasar Misrah.
3. Kwamittin fatawar ta Cairo, Misrah.
4. Kwamittin Malluman Misrah.
5. Majalisar Karatu na Siriya.
6. Da'irar fatawa ta ķasa wacce take ķasar Ordon.
7. Jami'ar Shari'ah dake kasar Qatar.
8. Majalisar ķasa ta fatawa na ķasar Kuwait.
9. Ofishin jami'ar Banu Umaiyah na Siriya.
10. Jam'iyyar Malluman Indiya ta kasar India.
11. Shugabancin Al'amuran addini ta ķasar Turkiyyah.
12. Majalisar Manyan Malluman Saudiyyah.
.
    Duk waďannan Majalisu na fatawar sunyi ittifaki akan haramcin yin transliteration na ayoyin Alkur'ani.
         Ga ķadan daga cikin manyan Mallumana wannan zamanin da suka tafi akan hakan;'----

1. Dr AbdulHameed Mahmud. (Shehin Jami'ar Cairo daya gabata).
2. Sheikh Muhammad Abdullahi Daraz. (Ďaya daga cikin Manyan-Manyan Mallaman Misrah).
3. Sheikh Muhammad Abdulazeem Al-zarqany (Mallami na ilimin Alkur'ani da Hadisi da jami'ar Azhar).
4. Sheikh Muhammad Shãkir (Yana daga cikin Manyan Malluman Misrah).
5. Shekh ILal Al-Afasy (Yana daga cikin Manyan Malluman Fãs, a kasar Magrib (Morocco).
6. Dr AbdulGaniy Al-Rãjihy (Yana daga cikin Manyan Malluman Misrah).
7. Sheikh Yusuf bin AbdulRahman Al-barqãwy (Ďan Kasar Ordon).
8. Sheikh AbdulHameed Ďuhmãzz (Mallamin Qur'ani da Tajweedi a Jami'ar Imam Muhammad bin Sa'ood na Riyad, Saudiyyah).
9. Sheikh Baddãh bin Albùsìrý (Me khutubah a babban masallacin Murtaniya).
10. Sheikh Abdullahi bin Ibrahim Al'ansãry (Yana daga cikin Manyan Malluman Qatar).
11. Sheikh Sayyid Sãbiq (Mallami a Jami'ar Ummul Qura ta cikin garin Makkah).
12. Sheikh Abubakar, Jabir Al'jaza'irý (Me wa'azi a masallacin Annabi S.A.W na madina).
13. Sheikh Muhammad Aliyyu Al-Sabùný (Mallamin Tafsiri a Jami'ar Ummul Qura ta garin Makkah).
14. Sheikh Muhammad Algazzaly (Babban me wa'azin musulunci na kasar Aljeriya).
15. Sheikh Manna'u Alqaďďan (Yana daga cikin Manyan Malluman garin riyad na saudiyyah).
16. Sheikh AbdulRahman Sãfy (Yana daga cikin Manyan Malluman Kuwait).
17. Sheikh Ďahir Ahmad Al'zãwý (Babban me fatawa na ķasar Libya).
18. Dr Muhammad Ahmad Farrãkh (Yana daga cikin Manyan Malluman Jiddah ta kasar Saudiyyah).
19. Sheikh Muhammad Ameen Badawy (Daga Maktabar Shehun Misrah).
20. Dr Ďaläl Umar Ba-Faqeeh (Shugaban Majalisar fiqhu na Makkah).
21. Dr Ibrahim bin Isma'il (Yana daga cikin Manyan Malluman Murtaniya).
22. Sheikh AbdulAzeez Al'Sabihain (Shugaban Majalisar kula da musabaqan Alkur'ani me girma a riyad, saudiyyah).
23. Dr Mani'i Al'Jahný (Shugaban matasan musulunci na Riyad, Saudiyyah).
24. Mujallar wa'azin musulunci ta Saudiyyah.
25. Sheikh Salih Aliyyu Al'Awd ((Yana daga cikin Manyan Malluman Paris, kasar Faransa).
26. Sheikhatu Zainab Algazzaly (Mallama me wa'azin musulunci a ķasar Misrah).

         Dukkan waďannan majalisu da Mallaman sunyi ittifaki akan haramcin yin transliteration, dogaro da waďannan hujjoji da muka ambata.......
Wanda kuma yakeson ķarin bayani ya nemi littafi me taken *تحريم كتابة القرآن بحروف غير عربية* rubutawan *Sheikh Salih Aliyyu Al'awd.*
       Saboda haka, kowa ya koyi alkur'ani a yanda aka saukar da ita kuma asa himma a koya da tajweedi domin kuwa shine qundin musulunci kuma abun alfahari ga ko wani musulmi na kwarai.
     Ku sani cewa Qur'ani shine:---
    * Mafi Alkhairin abunda zaka karanta ka samu lada.
     * Mafi Alkhairin abunda yakamata abuďe masa makarantu a koyar dashi kuma aje a koyan.
      * Mafi alkhairin abunda yakamata a kashe masa kuďi kuma akashewa ma'abocinsa kudi ako ta ina.
        * Mafi Alkhairin abunda yakamata mu mayar da hankali akansa.
         * Mafi alkhairin abunda yakamata mubashi lokacin mu.
          * Mafi alkhairin guzuri da zakaba yaronka kokuma duk wani na kusa dakai.
          * Mafi alkhairin abunda yakamata a haddace shi.
          Saboda haka, idan bazamu iya kasancewa cikin mahaddata ba, to meyasa bazamu je mu koyi yanda ake karantashi yanda aka saukar dashi dan mu karantashi mu samu lada ba????
.
        Allah Ya karamana temako, Yakuma bamu ikon koyan Alkur'ani da samun cetonsa ranan Alqiyama.
Post a Comment (0)