*HARAMCIN RUBUTA AYAR ALKUR'ANI DA HARRUFANDA BANA LARABCI BA*
Wato *(Transliteration)*
FITOWA NA (4).
✍
*Suleiman Yunusa Alkali*
.
Bayan godiya ga Allah da kuma salati ga Manzon Tsira, Annabi Muhammadu, muna ķara godewa Allah Da Ya kawomu kan wannan rubutu wanda a cikine zamu bayyana ra'ayoyin magabata akan haramcin yin *Transliteration* na ayoyin Alkur'ani.
.
1. *Al-Imamu Malik (R)*.
An tambayi Imamu Malik cewa;---
*Shin idan mutum ze rubuta Alkur'ani ya halasta ya rubuta da harrufan nan namu na yau???*
Sai yace;---
*Bana ganin hakan, saide ina ganin ya rubuta shi akan rubutu na farko* (ma'ana ya rubuta da harrufanda aka rubuta Qur'anin tun farko shine ra'ayin Imamu Malik).
Al-Imam Al-Sakhawy yace;--- *Abunda Maliku ya tafi akai shine gaskiyan magana*.
Abu Amru Al-Dâny yace:--- *Babu Mallaminda ya sabawa Malik a wannan fatawar cikin Malluma magabata.*
A duba littafi me take تحريم كتابة القرآن الكريم بحروف غير عربية. (Haramcin rubuta Alkur'ani me girma da harrufa da bana larabci ba shafi na 42).
.
2. *Al-Imamu Ahmadu Bin Hambal* yace;---
*Haramun ne a sabawa rubutun Alkur'ani da Uthman ya rubuta koda a wurin rubutun و ne ko أ ko ي kokuma waninsu.*
Kunga har harafi ďaya tak ma yace haramun ne ka chanza balantana kalma ďaya ko jumla ďaya ko aya ďaya kokuma sura ďaya kode Qur'anin ma sukutun-da-guda.
.
3. *Abu Hanifah* (Masu bin fiqhun Abu Hanifah sun faďa a wani littafi me suna المحيط البرهاني) cewa;--- *Be kamata ba mutum ya rubuta Alkur'ani bana rubutu irin na Uthmanu ba*.
.
4. *Al-Imamu Al-Shafi'i* (Masu bin mazhabar Shafi'i sun faďa a wani littafi me taken المنهاج في فقه الشافعية) cewa;----
(Rubutun Alkur'ani da Uthman yayi) *Sunnah ce abun bi* saboda haka, saba masa ba Sunnah bace kenan.
.
*MAGABATA MALLUMAN HADISI*
Suma Malluman hadisi basuyi shuru kan wannan lamarin ba sai da suka topa albarkacin bakinsu kamar haka;----
5. *Al-Imamu Al-Bayhaqy* yace:---
*Duk wanda yakeso ya rubuta ayar Qur'ani, to ya kiyaye* (ya rubutashi a) *rubutun farko kar ya yadda ya saba musu kuma kar ya canza wani abu daga cikin rubutunsu, domin kuwa sun fimu ilimi da zuciya da harshe masu kyau da Amana, saboda haka babu yanda zamu zatta mun fisu*.......
.
6. *Al-Imamu Al-Bagawy* yace:----
*Qur'ani da akayi ittifaki akai shine wanda Uthman ya tara ďinnan kuma duk wani rubutu wanda ba wannan ba an shafeshi saboda haka, baya yuwuwa ga wani ya kawo lafazi wacce ta fita daga irin rubutun farko*.
.
7. *Al-Faqihu, Abubakar Bin Al-Arabiy* yace:----
Tunda Allah yace ولو جعلناه قرآنا أعجميا لقالوا لولا فصلت آياته .. *Da mun saukar da Qur'ani da Ajami ne da sunce meyasa ba'a rarrabe ayoyinsa tsakanin Ajamin da larabci ba?*** (Suratu Fussilat 44).
Wannan ayar ta nuna cewa duk wata yare da ba larabci ba bata da rabo cikin *rubutun Alkur'ani* domin kuwa babu yadda zaka rubuta Qur'ani da yarenda Allah Ya koreta a cikin kur'anun, sannan kasani cewa idan ka chanza rubutun Qur'ani zuwa wata yaren daban bazamu kirashi Qur'ani kuma ba kuma baze bamu bayani da muke bukata ba........
.
8. *Al'Allãmah, Nizamu Al-Dini Al-Naisaboory* yace:----
*Abunda ya wajaba akan masu karatun Qur'ani da kuma Malluma da masu rubutun Alkur'ani shine subi wannan rubutun* (karsu qagi wani) *domin kuwa Zaidu bin Thãbit ne ya rubuta shikuma Amintaccene na Manzon Allah S.A.W kuma shi yake rubutawa Annabi wahayi*......
.
9. *Al-Imamu Ibn Al'Hãj, Al-Abdary* yace:----
*Abunda ya wajaba akan Marubuta Qur'ani shine su rubutashi da larabci ba da Ajami ba* (Transliteration) *Domin Allah Ya saukar da Qur'anin da Larabci ne ba da ajami* (Transliteration) *ba*.
.
10. *Al-Imamu Abu Ishaq Al-Shaďuby* yace:----
*Lallai Allah S.W.T Ya saukar da Qur'ani da larabcine ba da transliteration ba* (kamar yadda Ya faďa a wurare da dama cikin Alkur'anin kamar su Q12:2, Q26:193-195, Q39:28, Q41:44, Q43:3) *Kuma Annabinda aka sauko masa da Qur'anin Balarabe ne.....*
saboda haka abunda yake kamata shine a rubuta Qur'anin a yarenshi na larabci.
.
11. *Ibn Taymiyyah* yace:----
*Allah Ya saukar da wannan littafin ne da larabci kuma Ya aiko da Manzo me bayanin wannan littafin balarabe sannan Yasa mutanen farko da suka riķi wannan littafin larabawa ne saboda haka, larabci ya zamo abunda yake dole a kareshi yanzu a addini domin babu yadda za'ayi mu kare addinin yanzu sai mun kare wannan yaren na larabci......* saboda haka, a rubuta Qur'ani a yarensa na larabci domin shine yarenda Allah Ya saukar dashi akai kuma yarenda Annabin yayi amfani da ita wurin isar da saķon Alkur'ani tunda shine yarenda aka rubuta Qur'anin dashi........
.
Alhmdulillah.
Ana zamu dasa aya sai kun jimu a rubutu na gaba wanda ze kasance a dauke da fatawowin Malluman zamani da kuma Majalisu na fatawa na duniya da izinin Allah.
Muna rokon Allah Yabamu ikon koyan karatun Alkur'ani a yadda aka saukeshi Yakuma bamu ikon yin aiki dashi dan mu tsira gobe qiyama.