SHARHIN FIM ƊIN VIVA


SHARHIN FINA-FINAI (18)

Kamar yadda aka saba a kowacce ranar Asabar muna gabatar da sharhin fina-finan Indiya, a inda a kowane sati muke zaƙulo fim ɗaya muke gabatar da sharhi da kuma irin darasin da yake koyarwa. To a wannan satin ma dai munzo muku da wani ƙayataccen fim mai cike da ɗumbin tausayi, kyau da kuma nishaɗantarwa mai suna "VIVAH" wanda haɗaɗɗen jarumin nan wato Shahid Kapoor da kuma kyakkyawar jarumar nan mai suna Amrita Rao suka jagoranta.
     Kamar kullum da koda yaushe ni AUWAL IBRAHIM KJ (AIMAR) tare da taimakon ɗan uwa abokin aiki HAIMAN RAEES nake gabatarwa.

GABATARWA

Vivah fim ne na soyayya da akayi shi da yaren Hindi wanda ya fita a 2006, Sooraj Barjatya ne ya rubuta ya kuma bayar da umarni. Shahid Kapoor tare da Amrita Rao ne suka jagoranci fim ɗin yayin da Rajshri productions ne suke shirya suka kuma rarrabashi.
     Fim ɗin Vivah na bada labarin wasu mutane biyu, da kuma rayuwarsu tun daga baiko zuwa aurensu da kuma abinda ya biyo baya. Vivah shine fim na 4 wanda Shahid Kapoor da Amrita Rao suka fito tare. An fitar dashi a 10 ga Nuwamba 2006, an sami gagarumar nasara ta fuskar kasuwancinsa duk da cewa ya sami sharhi kala biyu daga wajen masu sharhi 6 domin wasu sun yaba sosai wasu kuma sun kushe tsarin labarin. Koma dai yayane an sami nasara sosai dashi. 

GUNDARIN LABARIN

Poonam matsakaiciyar yarinya ce da take zaune a wani ƙaramin gari dake Madhupur. Bayan rasuwar mahaifanta, a lokacin tana 'yar ƙarama, kawunta Krishnakant ya ɗauki nauyin maye gurbin mahaifinta a cikin rayuwarta. Saidai kuma matar kawun nata bata amsheta ba a matsayin' ya saboda tana kishin cewa tafi ɗiyarta mai suna Rajni kyau duba da ita Rajni ta kasance mai duhun fata da kuma kuma bata kai Poonam kyau ba. A ɗaya ɓangaren kuma, akwai wani sanannen ɗan kasuwa mai suna Harishchandra wanda yake a garin New Delhi, yana da 'ya' ya maza guda 2 : Sunil wanda ya auri mata mai suna Bhavna, sai kuma ɗayan mai suna Prem wanda yake shi mutum ne mai magana mai taushi da kuma ilimi.
     Sauƙin kai da kyakkyawan halin Poonam su suka burge Bhagatji, wanda yake harƙallar kayan ƙawa (jewelry) kuma aboki na kusa ga Krishnakant. Sai Bhagatji ya ɗauki maganar auren Poonam ya gabatar da ita domin Prem. Lokacin da Harishchandra ya faɗi ra'ayinsa gama da batun, da farko sai Prem ya ƙiya a cewa yayi yarinta da yin aure a yanzu saboda yana buƙatar maida hankali kan aikinsa tukuna. Sai Harishchandra yayi ƙoƙari ya shawo kan Prem akan ya fara samun Poonam kafin ya yanke hukuncin komai.
     Saboda girmamawa ga buƙatar mahaifin nasa, sai Prem ya amince da cewa zai je ya sami Poonam domin fahimtarta sosai daga nan sai ya yanke hukunci. Sun ziyarci dangin Krishnakant kuma sun bar Prem da Poonam su fahimci juna. Duk da cewa tattaunawar tasu ta farko mai wahala ce, amma daga baya sun amince da suyi aure saboda suna son junansu. Sai Prem da Poonam suka yi baiko sannan suka shirya yin aure nan da wata 6. Sai Krishnakant ya gayyaci dangin su Prem domin zuwa shaƙatawa a garin Somsarovar, dan haka Prem da Poonam sun sami damar da zasu fahimci juna sosai.
     Prem da Poonam sun kasance cikin tsananin soyayya a lokutan rayuwarsu. Duk da kasancewar sun zo daga mabanbantan tunaninnuka game da rayuwa amma suna son ganin alaƙar tasu tazo daidai ga juna. Kuma sun gano muhimmancin da zoben baiko wanda suka bawa junansu yake dashi da kuma dama ta musamman da suka samu kan juna sanadiyar hakan. Sun fara son junansu da kuma kasancewa a tare. Madallah da ɗawainiya da kuma kwantar da hankalin da 'yan uwansu suka dingi yi a gare su. Bayan wasu kwanaki sai Harishchandra da iyalansa suka koma gida domin halartar taron gaggawa game da kasuwancinsu, wanda ya bar Poonam da Prem zaɓin sadarwa ta hanyar waya da kuma wasiƙa. Sai Prem ya shiya cikin kasawancin ahalin kuma ya ɗauki wani muhimmin aiki a Japan. A yayin dawowa, ahalin sun taho da Poonam domin su bashi mamaki tare da murnar baikon su.
     Kwana biyu kafin ainihin auren, sai gobe ta tashi a gidan Krishnakant. Duk da cewa Poonam ta fice daga gidan akan lokaci, sai ta fahimci cewa Rajni da har yanzu tana cikin gidan sai ta koma cikin domin ceto ta. Poonam ta sami mummunar ƙuna a jikinta sanadiyar a sanadiyar hakan. Da aka kaita asibiti sai likitan yake sanar da mahaifin nata cewa a irin haka ne iyalai kanyi watsi da nasu. A take a wajen ya kira Prem cikin takaici a yayin dashi Prem ɗin ya baro Madhupur domin halartar bikin. A lokacin da yake ƙoƙarin saka hannu akan takardar yarjejeniya domin yi mata aiki, sai kawai ya fashe da kuka domin ba zai iya yin hakan ba. Sai ga Prem yazo da niyar ya auri Poonam duk da irin ciwukan da suke jikinta ya taho da ƙwararren likitoci daga Delhi. A take a wajen ya aure ta kafin ayi mata tiyatar. Tare da taimakon waɗannan likitocin na Delhi, asibitin yayi nasarar yin aikin wa Poonam. Bayan zaman wata 1 da rabi a asibitin, sai ga Rama (matar kawunta) tazo domin ɗaukar Poonam a matsayin 'yarta bayan ta fahimci irin sadaukarwar da Poonam ɗin tayi domin ceto 'yar tata.
     Daga baya, Poonam da Prem sunyi aure kamar yadda al'ada ta tanadar sannan suka wuce gida domin gudanar da sabuwar rayuwa. Fim ɗin ya ƙare ne a inda Poonam da Prem suke murnar daren farkon su a matsayin ma' aurata.

SHARHIN FIM ƊIN

Kamar yadda ragowar fina-finan kamfanin Rajshri productions ƙarƙashin Sooraj R. Barjatya suke nunawa tun daga kan fim ɗin "Maine pyaar kiya, Hum Aapke Hain koun, Hum Sath Sath Hain, Main Prem Ki Diwani Hoon" to shima dai Vivah ba a barshi a baya ba domin yabi sahunsu dangane da irin salon labarin shima yana magana ne akan ahali da irin matsolalin da ake samu daga wani ko wasu.
     A fim ɗin zamu ga cewa a can gidan Krishnakant matsala na faruwa saboda matarsa Rama taƙi yarda da cewa Poonam 'yar tace tana kishi da ita dan tafi 'yarta kyau da kuma haske gashi kuma ta sami miji mai inganci zata aura. A inda taci gaba da nuna adawarta ga Poonam har sai lokacin da tsautsayi ya abku na gobara ta ceto yarinyarta ita kuma ta sami ƙuna, sannan ta gane kurenta. To ina amfanin irin wannan da mutum baze gane muhimmancinka ba sai lokacin daka cutu a dalilin tseratar da nasa.
     Ta ɗaya ɓangaren kuma munga yadda Prem ya nunawa Poonam so na gaskiya bayan sun fahimci juna ya tsaya mata a lokacin da take tsananin buƙatar hakan, bai guje mata ba dan ganin cewa ta nakasa sai ma taimakawa da yayi wajen ganin anyi mata aiki mai kyau.
      Daga ƙarshe ina mai fata da addu'ar Allah ya haɗa mu da masoyan gaskiya waɗanda zasu zauna damu a kowane hali, ba wai sai muna dashi ko yanayi mai kyau shine suke tare da mu da zarar an sami akasin haka sai su juya mana baya. AMEEN YA ALLAH

TAURARIN SHIRIN

Shahid Kapoor - Prem
Amrita Rao - poonam
Anupam Kher - Harishchandra
Alok Nath - Krishnakant
Seema Biswas - Rama
Samir Soni - Sunil
Lata Sabharwal - Bhavna
Manoj Joshi - Bhagatji
Amrita Prakash - Rajni

By : AUWAL IBRAHIM KJ (AIMAR)
Post a Comment (0)