MUN ZO WANI LOKACI YANZU WANDA MATA SAM BA SU DA KUNYA


*_MUNZO WANI LOKACI WANDA MATA SAM BASA YIN KUNYA!_*

بسم الله الرحمن الرحيم.

_▪Subhanallah! Astagfirullah 😔 Allah ka gafartamana ka Shiryar damu_

▪Yanzu mun zo wani zamani wanda akasarin 'yan matan mu basa jin kunya kuma basa yinta ko kadan! Mace bata jin kunyar yin hira da samarin da ba ta sani ba. Ta nan media abun ma yafi muni sosai a instagram ne ko facebook ko a wasu shafukan sada zumunta irinsu whatsapp, twitter, snap chat da sauransu, basa jin kunyar yin bidiyo chart da samari ko su kira su ko suyi musanyar hotuna wasu ma hotun nan batsa da fitsara.

▪Wasu ma a jahilcinsu suna tunanin cewa babu wani laifi wurin hira da maza, sai ma suka ce, idan bamuyi magana da samari ba, ta yaya zamu sami mijin aure? Ta yaya zamu gane cewa suna son mu?

▪Mace yarinya budurwa zaka sameta da tarin samari a media, kuma sam bata jin kunya daga kalamanta, mu'amalarta, halayyarta, dabi'unta, domin kuwa haka zaka ga tana sakin zance da sakin jiki a hurinsu. Itace tura hotunanta, yi musu video call, wata ma saboda asara tana bandaki tana yin video call da samari! 😕

▪Abun takaici shine mafi yawancin 'yan matan suna faɗawa tarko ne na wadancan samarin da suke nema. Don mafi yawansu mayaudara ne masu son cimma wata damarsu da amfani da raunin matan. Abin da ze fi baka dariya shine, wadannan 'yan matan sukan yi saukin faɗawa wadannan yaran wadanda suke yaudararsu da kalamansu, waɗanda suke yin alkawuran karya gare su, waɗanda suke yaudararsu da soyayyar karya, waɗanda suke yin da'awar cewa sun fi cancanta a gare su amma a zahirin gaskiya ba haka bane.

▪Abun takaici a zahiri ma haka avun yake, yarinya 'yar secondary school zaka sameta da yin alaqar Boyfriends 😕 tana da samari kala kala a shekarunta da basu fi 16, 17, 18 ba! Wayarta fal da numbobin maza, takan shige daki ta kwana tana yin yawa, a kalamanta sam babu kunya balle jin kunyar wanda take magana dashi. 

▪Kai abun takaici da bakin ciki shine, yanzu samari da 'yan mata sun mayar da soyayya iya rashin kunya, fitsara, da maganganun batsa. ☹ Mace zata zauna namiji katon banza yayi ta yi mata maganganun sha'awa da iskanci tana jin dadi wai ai son ta yake! Su na kirkin idan sunje sai ace basu iya hira ba! 

▪Wallahi فتربصوا! Mu jira! Indai alummar mu zata cigaba a haka! Iyaye suna kallo kuma sun sani, amma sun fake da cewa ai zamani ne! Alhaji da hajiya lokacin da Allah ya damƙe ku to zaku gane kuranku! Kafin a fara yi musu hisabi akanku ku za'a fara yiwa hisabi akansu. Kuma zakuyi nadama lokacin da kuka mutu suna aikata alfashar su amma baku da ikon hana su! 

*▪#SHAWARA* - ga dukkan 'yan uwana mata a musulunci da zasu karanta wannan rubutun, wallahi samarin nan da kuke biye musu da mganganun batsa suna yaudararku da soyayyarsu, wallahi baku kadai suke yiwa ba, suna da wasu 'yan matan a gefe. So ko da sun yaudare ku da zasu aure ku wallahi karya suke yi. So suke suci moriyar ganga su jefar! 

▪Ki Tsare mutuncinki da kimarki, karki sauko da darajarki ga almajiran gayun nan! Wallahi ba auranku zasuyi ba. Saboda haka ku zama wayayyu ku nisance su. Basu cancanci mace mai daraja irinki ba.


▪Ku dena tayar da hankalinku akan mazajen aure, wallahi Allah ya rubuta mazajenku tun kafin halittar duniyarsa. Kuma da sannu idan lokaci yazo zaku gansu.

▪Ki fara gyara kanki da alaqar ki ga Allah, idan kika zama mutuniyar kirki to in shaa Allahu Allah zai hadaki da mutumin kirki. 

▪Kuma don Allah ku dena ruduwa ga haduwar media da kukayi da wasu, akwai na kirkin amma fa na banzan suna da yawa suna yaudararku ne kawai. Allah yasa mu dace ya tsare mana mutuncinmu.

✍Rubutawa: *Abdullah A Abdullah Abou Khadeejat Assalafeey (أنصار السنة)*
05/03/1441.
02/11/2019.

+2348060027244

https://sirassalafeey.wordpress.com/munzo-wani-lokaci-wanda-mata-sam-basa-yin-kunya/
Post a Comment (0)