DUK ZANCE NE KAWAI


Daga
*Dr. Mansur Sokoto*

DUK ZANCE NE KI ZAUNA A GIDA KINA BURIN ‘DAN SANATA KO GWAMNA KO KUMA SHAHARARREN ATTAJIRI KUMA DAGA ANYI MAGANA SAI KICE BABU MIJIN AURE A GARI.

Akwai mazaje ma ba miji ba, suna can buhu-buhu a gidan kallon ball. Saboda irin burin da mata suka ci ne yasa samarin suka fita harkarsu suka koma kallon ball tukuru.

Masu mutuwar zuciya daga cikin mazan suka koma neman auren-jari. Kun ga anyi ‘balance’ kenan. Don haka kowa sai yaci wuya. Shi babu mata, ke kuma babu miji saboda kowa ya dauko “dala da gammo”.

A shekarun baya, mata sun wahalar da maza a fannin soyayya. Sai a samu mace daya tana wasan-kura da samari goma kuma kowa a cikinsu so yake tace shi take so ya aureta. Ita kuma tana ta wajigasu kamar kwallon ludo.

Ita dama duniya rawar ‘yan mata ce, yau kana gaba, gobe sai ka dawo baya. Ba zan manta ba, akwai wacce na sani har lissafa sunayen motocin da ake zuwa wajenta dasu wajenta take yi saboda buri da karya. Yadda ta dama, haka samarin suka dinga sha amma a karshe qauye muka kaita.

Duk irin misalan da suke a doron qasa basa zama izina a wajen matan yanzu. Yawancin masu cewa sun rasa miji dinnan sun samu damar aure suka yi wasa da ita saboda buri.

Ita dama yar talaka ta shiga uku idan tace buri ke a suwa kuma bayan kin san rayuwa a gidanku. To suma ‘ya’yan masu kudin jikinsu gaya musu yake balle kuma ke. Mai karatu tafi cikin GRA ko Abuja ka sha mamaki, sai ka samu mace ta kai shekara 40 a zaune, ta zama sanata a gidansu.

Allah na tuba, duk sanda mace ta kai 40 a gida kuma ta cigaba da jiran mai kudi ai ta samu matsalar kwakwalwa. Ahirr dinku ‘yan uwana mata, bahaushe yace “Da babu gwara ba dadi” Kuma idan hagu taqi sai a koma dama.

Wannan dalilin ne yasa kuke ta bushewa, kullum a rame, cikin tunani da rashin lafiya. Ga kuma uwa da yan uwa sun sako ki gaba da maganganu na neman kai da ke. Saboda kin tare mata hanya, ga qawayenki can sai haihuwa suke yi, saidai idan kun hadu su baki raino ki ‘dana rainon jariri. Allah ya aurar da kowa da alheri.
Post a Comment (0)