WANI SHIRIN BAN TSORO ZAI HAƊA WASU GWANAYE NA ƘASAR INDIYA


Wani Film Na Ban Tsoro (Horror film) Me Taken ‘Bhoot – Part One: The Haunted Ship’ Zai Hada Gwanaye Da Duk Sun Karbi Wannan Gagarumar Kyautar ta kasa wadda Ake Kira da NATIONAL AWARD Domin Wannan Film Zai Fito da Matashin Jarumi VICKY KHAUSHAL Wanda ya karbi "National Award best Actor" da Film din URI Inda Shine Zaija Ragamar Wannan Film Yanzu se Kuma Wani Gwani Wajen Kirkiran Sauti me ban tsoro Watau ANISH JOHN Wanda ya karbi "National Award in Best Audiography" Sannan Wannan Mutum Duk Shine Ya Hada Wani Sauti a Fina-Finan Bayan Nan Na ban tsoro Irin su Newton, Trapped da Pari.

Director na Wannan film Bhanu Pratap Singh Yayi Magana da Shafin ETimes Yace Ba Karamin Dace Bane Kayi Aiki da Wadanda A kowane Bangare Suna da Baiwar Abun.

Wannan Film dai Tuni Tallarsa ya Fita Kuma Film din Zai Fita ne 21, ga Wannan Wata na February 2020.

By #AbbaIndiaDala


Post a Comment (0)