Tambaya ta 007


*HUKUNCIN SADUWA DA IYALI BAYAN DAUKEWAR JININ HAILA*

Tambaya 
Assalaamu alaikum.
Malam mijina zai iya kusantata bayan jinin haila na ya dauke Amma banyi wankaba

AMSA

Wa'alaikumussalaam Wa Rahmatullahi Wa Barakaatuh.
Mallamai sun yi maganganu uku karkashin wannan Mas'alar kamar haka:
(1) Imamu Malik da Imamu Shshafi'i da mafi yawan Mallamai (Allah Ya musu Rahama) sun tafi a kan baya halatta yayin da jinin hailar ya dauke ya kusance iyalin shi har sai ta yi wanka. Daga cikin dalilan su fadin Allah(SWT):
(ولا تقربوهن حتى يطهرن فإذا تطهرن فأتوهن من حيث أمركم الله)
Kuma kar ku kusance su har sai sun yi tsarki idan sunyi wanka sai ku je musu daga inda Allah Ya Umurce ku.
Sukace lafazin (يطهرن) yana nufin wanka ne kamar yadda kira'ar Imamu Hamza Da Imamul Kisaa'i da Khalaful'Ashir da riwayar Shu'ubatu
(الإمام حمزة ،الإمام الكسائي، خلف العاشر، رواية شعبة) su ke kara tabbatar da hakan, haka kuma sunkara kafa hujja da lafazin 
(فإذا تطهرن),
wanda ya zo cikin Ãyar yana nuna wanka ake nufi.
(2) Kashi na biyu na Mallamai su ne Abu Hanifah da daliban shi da wasu daga cikin mallamai (Allah Ya jikan su da Rahama) sun tafi akan ya halatta idan jinin yabdauke miji ya kusanci matar shi ko da ba tayi wanka ba in dai ta samu cikakken tsarki daga mafiyawancin kwanakin jinin haila [a wurin Abu Hanifah mafi yawan kwanakin jinin haila kwana goma (10)], dalilin shi shima Ãyar da muka anbata yace fadin Allah(SWT):
(ولا تقربوهن حتى يطهرن فإذا تطهرن فأتوهن من حيث أمركم الله) 
Abinda Ãyar ta ke nufi shi ne kar ku kusance su sai jinin ya dauke gaba daya idan ya dauke to kuje musu daga inda Allah(SWT) Ya umarce ku.
(3) Imamul Auzaa'i ( Allah Ya jikan shi da Rahmah) ya ce bayan daukewar jinin gaba daya, idan ta wanke gaban ta to yana halatta ya kusance ta, wato ba dole sai ta yi wanka ba, shima dai da waccan Ãyar ya kafa hujja ya ce abin da Allah (SWT) Ya ke nufi shi ne kar ku kusanci matayen ku yayin da jinin ya dauke gaba daya har sai sun wanke gaban su, idan sun wanke to ku je musu daga inda Allah ya umarce ku.

Fadakarwa mai muhimmanci
Karkashin maganganun Mallamai da muka yi bayani: Abin da ya fi dacewa shi ne idan jinin ya dauke anfi son ta yi wanka kafin mijin ya kusance ta.

والله تعالى أعلم.
DR NASIR YAHYA ABUBAKAR BIRNIN GWARI
18TH FEB. 2020

_________________________
→"Wanke hannu da ruwa Mai gudana tare da Shan ruwa akai-akai da bin dokokin Ma'aikatan lafiya na daga cikin matakan kariya daga daukar cutar corona virus kamar yadda ma'aikatan lafiya suka fada"←
_________________________

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Post a Comment (0)