ADDU'A GA MAMACI 01


ADDU'A GA MAMACI 0⃣1⃣

Kafin kutsawa kai tsaye ga hukuncin yin add'ua ga mamaci, da kuma abubuwan da suke iya riskar mamaci bayan mutuwarsa na daga aikin bayi, zanso in danyi tsokaci akan wasu hukunce hukunce da suka shafi abubuwan da mara lafiyan da ya cire tsammani zaiyi da abunda masu jinyarsa zasuyi, dama sigar yadda ake ta'aziya da kalan addu'o'in da za'ayiwa mamaci, in sha Allah. Ina rokon Allah ya datar dani. 

📕 WANDA YAJI ALAMAR MUTUWA ME ZAIYI?? 
      Alokacin da mutum yaji alamu na cewa rayuwarsa tazo karshe ko kuma rashin lafiya ya tsananta masa takai ga har yafitar da rai, to yana wajaba akansa da yayiwa iyalansa wasiya da jin tsoron Allah da kuma riko da addinin Allah, da nisantar shirka kamar yadda Annabin Allah yaqub Alaihis salam yayi (Baqara 133).
Sannn yayi kokarin hanasu aikata duk wani abu na sabo da yake tinanin zasu iya aikatawa bayan mutuwarsa koma adalilin mutuwarsa. 
         Sannan bayan nan sai ya shagaltu da ambaton Allah, musamman Kalmar *LA ILAHA ILLALLAH* saboda fadin manzon Allah "duk Wanda ya kasance karshen zancensa La ilaha Illallah ne zai shiga Aljannah. 
Da kuma fadinsa sallallahu alaihi wa sallama "Mafi soyuwar aiki awurin Allah shine ka mutu alhali harshenka yana jike da ambaton Allah". 
    Daga cikin azkar din da akeso mutum ya yawaita fadi awannan lokacin akwai:
*لاإله إلا الله والله أكبر، لاإله إلا الله وحده، لاإله إلا الله لا شريك له، لاإله إلا الله له الملك وله الحمد، لاإله إلا الله ولا حول ولا قوة إلا بالله*

📒 LAQQANAWA MAMACI KALMAR SHAHADA. 
      Idan ya kasance majinyaci ya fita a hayyacinsa ko rashin lafiya tayimasa tsanani ta yadda bai iya hararo fadin Kalmar shahadar da kansa ba, to shari'a ta karantar da cewa wadanda suke tare dashi su lakkana masa, hanyar da akafiso wurin lakkanawar shine wani yana furtawa da karfi har Allah ya yassarewa mara lafiyan ya furta shima, amma babu laifi yana umartarsa da yafada, misali yace: kace la ilaha illallah, dukda dai wancan na farkon yafi kamar yadda malamai suka bayyana. Dalili kuma akan haka shine fadin manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama "ku laqqanawa mmatanku Kalmar la ilaha illallah". Da kuma fadinsa "Duk Wanda ya kasance karshen zancensa ya kasance la ilaha illallah zai shiga aljannah watan watarana koda kuwa wani abu ya sameshi".

📔 BA KOMAI AKE FADA BA AWURIN MARA LAFIYA. 
  Alokacin da aka ziyarci mara lafiya to ba'a bukatar mutum yasaki bakinsa yayita surutu Mai ma'ana da mara ma'ana, abunda akafiso shine yawaita yimasa addu'a, manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama yana cewa "Idan kuka ziyarci mara lafiya ko mamaci to ku fadi alkhairi domin mala'iku suna cewa amin akan duk abunda kuka fada". (Muslim).

📓 WANDA AKA MASA MUTUWA ME ZAICE?? 
     Mutuwar makusanci babu shakka musibace kuma jarrabawa ce babba, hakan yasa Allah yayi tanadin aljannah ga duk Wanda yayi hakurin rasa wani masoyinsa kamar yadda yazo ahadisi manzon Allah yace "lalle Allah yana yarda wa bawansa mumini alokacin da ya dauke masa wani masoyinsa daga cikin mutanen duniya sai yayi hakuri ya kuma nemi ladan hakurin da yasamu Aljannah". 
      Hakan yasa abunda ake bukata mutumin da aka masa mutuwa ya fada shine da fari ya godewa Allah sannan sai yayi istirja'i, yace: 
*إن لله وإن إليه راجعون، اللهم أجرني في مصيبتي وأخلف لي خيرا منها* 
Babu laifi dan idanunsa sun zubar da hawaye, wannan tausayine kamar yadda manzon Allah ya gayawa sayyidina umar bin khaddab lokacin rasuwar Ibrahim dan manzon Allah. Amma baya halasta daga sauti da kururuwa da ihu, da bugun jiki, duka wannan haramunne. 

📗 ADDU'A WA MAMACI ALOKACIN YIMASA SALLAH. 
   Ayayin yiwa mamaci sallah ana bukatar mutum ya yawaita addua ga wannan mamacin, ya kuma tsananta kasancewar shine yake cikin matsananciyar bukatar addu'ar, kuma saboda fadin manzon Allah "Idan zakuyiwa mamaci sallah to ku kebanceshi da addu'a". (Abu Dawud)
Addu'o'i da ake acikin sallah janaza abune da yake sananne Wanda babu bukatar kawoshi anan saboda gudun tsawaitawa. 

# zaurenfisabilillah
https://t.me/Fisabilillaaah
Post a Comment (0)