SIRRIN SOYAYYA DA BAZAWARI


Mata, Ga Sirrin Soyayya Da Bazawari:

Ita ma macen da take soyayyar aure da bazawarin da yake da mata daya ko fiye a gidansa, macece datafi sauran matan da muka ambata a baya aiki tukuri domin ganin ta samu shiga wajen manemin nata har kuma tayi sa'a amincewarsa ta zama matarsa ta aure.

Duk da yake wasu mata na ganin cewa auren mace mai mata yana da matsala da kuma wuyar gaske, ni kuma anawa ra'ayin da kuma nazarin ba haka abun yake ba, matsalar da mata suke fiskanta dai kwai shine, basusan sirrin soyayya da mazan da suke da mata a lokacin da suka zo neman auren suba. Shi yasa 'yan mata da damar gaske suke daukar cewa maza masu mata basu da dadin soyayya kokuma rashin sanin yaddazaki tafiyar da shi yasa ki rasa shi.

Sirrin duk wani namijin da yake da mace a gida ko yake da mata kuma ya fito yana meman kara wani auren shine, yana da dalilin daya sanya yake sha'awar kara wannan auren kuma yace ke yakeso ki zama matar tasa dai zai kara, to yana da kyau kiyi kokarin sanin dalilinsa na sha'awar karawannan aure domin yin nazari ko dalilin nasa ya isa ya zama hujjar da zaki iya aurarsa.

Da akawai wasu dalilan da sukan sanya ma suyi tunanin kara aure, da akwai na rashin son matan da suka aura tun a farko, da kuma dalilin kazanta ko rashin iya kwalliya, wani ya soma ne da auren bazawara yana neman ya kara da budurwa, wani kuwa da budurwa ya soma zai kara da bazawara, da akwai mazan da suke son hada mata masu bambamcin kabila ko al'ada kokuma launi na fata, da kuma mazan da dazaran mace ta soma tsufa suna sha'awar auro wata matar. http://sirinrikemiji.blogspot.com/2018/07/mata-ga-sirrin-soyayya-da-bazawari.html#.XkTxyGTFT0w.whatsapp
Post a Comment (0)