AL'UMMAH TANA GINUWA DAGA GIDAJE
Kana son gina ma kanka gida na gari sannan gidan ka ya zama gidan tarbiyya da wasu zuri'a da zasu gina al'umma?
•"Ƙaunar juna da yin aure don neman yardan Allah.
•Yin na rige wajen aikata alkhairi wajibbai da nafilfili karanta Ƙur'ani Sallolin nafila kyauta Sadaka da guje ma cutukan zuciya, da yin na rige wajen kyautata ma junan ku, mai zaka yi ka faranta mata? mai zaki yi ki faranta masa?
•Tausayin juna da Rahma da jin ƙai, ba cuta ba almubazzaranci da ha'intar miji ko mata. Shi kuma ya tausaya mata idan tana da ciki, ya riƙa tuna dawainiyar da take gaban ta na kula da yara da hidindimun gida.
•Ma'aurata su zamo masu sauke haƙƙokin juna da taimakekeniya, (Miji) ka ciyar da mace ka tufatar da ita gwargwadan halinka da kuma Haƙƙin kwana tare da kyautatawa da sauran haƙkƙokin yaranka.
•Mata tasan cewa dole tayi ɗa'a wa miji. Ta yi hidindimu na gida (tsafta) tsaftar kanta da ta iyali. Ajje komai inda ya dace kome ya zama tsaf.
•Kowa yasan ina ya kamata ya tsaya, namiji shine shugaba. Ita kuwa abokiya ce. Tana da gudunmowa wajen shawara da tacewa. Sannan miji da mata abokan juna ne wajen wasa da nishadi da walwala dabin tsaka tsaki cikin ci ko sha.
•Sannan ma'aurata susan cewa sune makarantan farko wa 'ya'yansu, a wurin su zasu koyi sanya tufafi da magana da cin abinci da gaisuwa da zumunci da yanda ake idan farin ciki ya samu ko bakin ciki.
•Ma' aurata su rikaTattauna akan abubuwa masu muhimmanci na daga addini da rayuwar duniya da kokarin ƙirƙiro da abubuwa da zasu amfanar da mutane koda na unguwarsu ne
•Sannan mu sani ko da yaushe akwai farin ciki ko baƙin ciki kan iya zuwa, zamo masu godiya da haƙuri da juriya da bin al'amura a sannu da yanke hukunci cikin adalci"
# Zaurenfisabilillah
Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah