FASSARAR WAƘAR INDIAWAALE

FASSARAR WAƘAR INDIA WAALE 

Waƙa: India Waale

Shiri: Happy New Year 

Harshe: Hausa 

Shekara: 2014 

Sauti: Vishal-Shekhar

Rubutawa: Irshad Kamil

Kamfani: T-Series

Rerawa: Vishal Dadlani, KK, Shankar Mahadevan & Neeti Mohan
 
Fassarawa: Haiman Raees 

'. Ho… Maane Ya Koi Maane Na

Ko dai a yarda ko ma kada a yarda.

'. Yahaan Apni Bhi Thodi Ada Thoda Andaaz Hai

Mu ma ma fa muna da salo tare kuma da alheri. 

'. Aise Hain Chaahe Waise Hain

Ko da ace kuwa mun kasance haka ko haka. 

'. Arey Jo Bhi Hain Jaise Hain

Babu damuwa da ko ma yaya mu ke. 

'. Khud Pe Humein Naaz Hai…

Domin kuwa muna alfahari da kanmu. 

'. Jaane Na Humko Ye Zamaana…

Izuwa yanzu duniya ba ta san muhimmancin mu ba tukun. 

'. Chaaho To Humko Aazmaana

In kuna son ku sani, to gwada mu. 

'. Hum Yaar-Baaz, Hum Jaal-Saaz

Abokai ne mu da ba mu rabuwa, mu maƙayata ne. 

'. Hum Ishq-Baaz Dilwaale

Mu mahaukatan masoya ne. 

'. Kehte Hain Humko Pyaar Se Indiawaale

Cike da soyayya mutane ke kiran mu da... 'Yan Indiya. 

'. Chhu Lete Dil Ke Taar Se Indiawaale

Mu ne ma su taɓa kirtanin zukata, mu ne 'yan Indiya. 

'. Har Jeet Cheen Le Haar Se Indiawaale

Mu kan iya fizge nasara da ga rashin nasara, mu ne 'yan Indiya. 

'. Dushman Ke Chakke Chhuda De Hum Indiawaale… (x2)

Mu kan kada maƙiya babu sassauci, mu ne 'yan Indiya. 

'. Yun Toh Seedhe Bade

Mu ma su sauƙin sha'ani ne. 

'. Kabhi Chahein To Haathon Se Lete Laqeerein Chura

Amma idan mu ka so, mu kan iya sace zanen hannun mutum ma. 

'. O… Humko Parwaah Nahi…

Ba mu damu ba. 

'. Jo Bhi Kehta Hai, Kehne De Jag Ye Bhala Ya Bura

Da abinda duniya ke cewa game da mu, mai kyau ko maras kyau. 

'. Jaisi Bhi Marzi Ho Humari…

Duk abin da mu ke muradi.

'. Karte Hain Aisi Hoshiyaari…

Mu na yin sa ne kawai da ƙwarewar mu. 

'. Par Dil Se Yaar Jo Le Pukaar

Amma wa abokai da su ke kiran mu da ga zukatansu. 

'. To Jaan Nisaar Kar Daale

A shirye mu ke mu sadaukar da rayukan mu domin su. 

'. Kehte Hain Humko Pyaar Se Indiawaale

Cike da soyayya mutane ke kiran mu da... 'Yan Indiya. 

'. Chhu Lete Dil Ke Taar Se Indiawaale

Mu ne ma su taɓa kirtanin zukata, mu ne 'yan Indiya. 

'. Har Jeet Cheen Le Haar Se Indiawaale

Mu kan iya fizge nasara da ga rashin nasara, mu ne 'yan Indiya. 

'. Dushman Ke Chakke Chhuda De Hum Indiawaale…

Mu kan kada maƙiya babu sassauci, mu ne 'yan Indiya. 

'. Ungli Pe Sabko Nacha De Hum Indiawaale

Mu kan sa kowa ya yi rawa da kiɗan mu, mu ne 'yan Indiya. 
 
'. Aankhon Ki, Aankhon Ki Chaabi Se

Yin amfani da mabuɗin ido. 

'. Thoda Betaabi Se Chupke Se Khole Dilon Ke Taale…

Da ɗan ƙarancin hutu da kuma sirri, mu ke buɗe mabuɗan zukata. 

'. Haan... Jaan Dete, Usko Jahaan Dete, Apna Imaan Dete

Hakane, mun ba da rayukan mu, duniyar mu da kuma yardar mu. 

'. Jiski Bhi Baahein Gale Mein Daale

Ga wanda mu ka runguma. 

'. Duniya Se Humko Kya Le Jaana… O…

Ba ma buƙatar komai a wannan duniyar. 

'. Yaaron Ke Dil Mein Ho Thikaana

Abin da mu ke so kawai shi ne matsuguni a zukatan abokai. 

'. Humein Ek Baar Hota Hai Pyaar

Sau ɗaya kawai muke faɗawa soyayya a rayuwa.

'. Yeh Laakh Baar Kehla Le

Ko sau nawa za ka tambaya, amsar dai ɗaya ce. 

'. Kehte Hain Humko Pyaar Se Indiawaale

Cike da soyayya mutane ke kiran mu da... 'Yan Indiya. 

'. Chhu Lete Dil Ke Taar Se Indiawaale

Mu ne ma su taɓa kirtanin zukata, mu ne 'yan Indiya. 

'. Har Jeet Cheen Le Haar Se Indiawaale

Mu kan iya fizge nasara da ga rashin nasara, mu ne 'yan Indiya. 

'. Dushman Ke Chakke Chhuda De Hum Indiawaale… (x2)

Mu kan kada maƙiya babu sassauci, mu ne 'yan Indiya. 

'. Ungli Pe Sabko Nacha De Hum Indiawaale

Mu kan sa kowa ya yi rawa da kiɗan mu, mu ne 'yan Indiya.

'. Dushman Ke Chakke Chhuda De Hum Indiawaale… 

Mu kan kada maƙiya babu sassauci, mu ne 'yan Indiya.

<••••••••••••••••••••••••••••>
      Haiman Raees 
<••••••••••••••••••••••••••••>

        08185819176

Twitter: @HaimanRaees 

Instagram: Haimanraees 

Facebook: Haiman Raees 

Tumblr: Haimanraeesposts

Haimanraees@gmail.com 

Miyan Bhai Ki Daring 

Post a Comment (0)