SHARHIN FIM ƊIN DAMMU
Dammu, wani lokaci kuma a rubuta shi da Dhammu fim ɗin India ne da ya fita a cikin shekara ta 2012, fassarar Dammu dai shi ne Izza.
An fassara wannan fim a cikin harshen Tamil inda aka sa masa suna Singamagan, da aka fassara shi da Hindi a ka sa masa suna
Dhammu, a harshen Hausa kuma aka sa masa suna Izzar Mulki.
Umurni: Boyapati Srinu
Ɗaukar Nauyi: K. A. Vallabha
Sauti: M. M. Keeravani
Horas da 'Yan Wasa: Arthur A. Wilson
Tacewa: Anthony
Kamfanin Da Ya Shirya: Creative Commercials
Kamfanin Da Yayi Dillanci: Sri Venkateswara Film Distributors
(Nizam) & Ficus Inc.
(Overseas)
Ranar Fita: 27 April 2012
Tsawon shirin: mintuna 155
Ƙasa: India
Harshe: Telugu
LABARIN SHIRIN A TAƘAICE
Rama Chandra maraya ne da ke rayuwarsa a sannu tare da aminin sa, ana nan sai ya kamu da son wata 'yar masu kuɗi mai suna Sathya. Sathya sai ta bayyanawa Rama cewa, domin samun damar auren ta, tarihi, nasaba da kuma mutuncin gidansu abu ne mai muhimmanci. A daidai wannan lokacin ne kuma Rama ya fahimci cewa wani ahali na sarauta suna neman wanda za su ɗauka a matsayin "ɗa" domin ya zamo magaji a masarautar. Rama sai ya yi amfani da wannan dama, sai dai bayan da ya isa can, sai ya fahimci cewa yadda yake tunanin abun fa ba haka yake ba. Domin kuwa wannan ahali wannan ahali da ya sauka a ciki suna da daɗaɗɗiyar gaba a tsakanin su da wani ƙasurgumin ahalin masarauta da ke maƙwabtaka da su.
Kamar fa hakan bai isa ba, sai kuma ya fahimci cewa, dubban mutanen da ke ƙarƙashin masarautar da yake duk sun dogara ne da shi domin su rayu. Sannan kuma ya fahimci cewa lallai fa shi ne asalin magajin wannan masarauta. To shi dai Rama baya son tashin hankali, don haka yayi iya ƙoƙarinsa wajen ganin zaman lafiya ya wanzu, amma sai abu ya ci tura.
Da fa ya harzuƙa, ya rufa musu da duka har ya kusa kashe babban ɗan wancan basaraken, a ƙarshe dai an nuno cewa basaraken ya fahimci cewa abin da yake kai ba daidai bane kuma ya ba wa kowa haƙuri daga nan komai ya wuce inda kowa a tsakanin ƙauyukan ya yarda cewa Rama jarumi ne.
JARUMAN SHIRIN
Jr. NTR - Rama Chandra
Trisha - Sathya
Karthika Nair - Neelaveni
Brahmanandam - Jaanaki
Nassar - Chandravanshi King
Bhanupriya -
Venu Thottempudi -
Abhinaya -
Hari Teja -
Chitralekha -
Suman - Suryavanshi King/Raja Surya Pratap Singh
Kota Srinivasa Rao - Raja
Ahuti Prasad -
Sampath Raj -
Kishore -
Tanikella Bharani -
Rahul Dev -
Subhalekha Sudhakar
Snigdha
Kolla Ashok Kumar
Rahul Mahajan
Maryam Zakaria
Waƙoƙin Shirin
1. "Sound of Vel"
2. "O Lily"
3. "Ruler
4. "Raja Vasi Reddy"
5. "Vaastu Bagunde"
3
6. "Dhammu"
7. "Ruler (CD Version)"
<••••••••••••••••••••••••••••>
Haiman Raees
<••••••••••••••••••••••••••••>
08185819176
Twitter: @HaimanRaees
Instagram: Haimanraees
Facebook: Haiman Raees
Tumblr: Haimanraeesposts
Bakandamiya: Haiman Raees
Haimanraees@gmail.com
Miyan Bhai Ki Daring