ILLOLIN ZINA, LUWAƊI DA MAƊIGO 1


*01→ILLOLIN ZINA ,LUWADI DA MADIGO*

Gabatarwa:--- 

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai.

 Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin Manzanni, Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallahu Alaihi Wasallam) tare da alayensa da sahabbansa.

 Bayan haka, wannan tsokaci ne a kan ma’ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncin kowanensu a karkashin shari’ar Musulunci da Dokta Muhammad Rabi’u Umar Rijiyar Lemo ya rubuto kuma muka ga ya dace a sanya a wannan Gida mai albarka ( *miftahul ilmi*) don amfanin jama’a. 

Ina rokon Allah Ya sa abin ya yi tasiri a kan kowane musulmi...

Shimfida

Ma’anar zina da hukuncinta:
Lafazin zina a shari’ance yana nufin saduwa da mace ba tare da an yi aure, ko an mallake ta a matsayin baiwa ba. Sai dai akan yi amfani da lafazin zina a kan abin da bai kai saduwa ba, kamar yadda ya zo a Hadisin Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ) ya ce, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “An rubuta wa dan Adam rabonsa na zina, babu makawa sai ya same shi, zinar idanu ita ce gani, zinar kunnuwa ita ce ji, zinar harshe ita ce magana, zinar hannu ita ce damka, zinar kafa ita ce taku, zuciya kuwa tana kwadayi tana fata, farji kuma shi yake gaskata haka ko ya karyata.” Muslim.


A cikin wannan Hadisi za mu ga yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya nuna cewa kowane dan Adam an rubuta masa rabonsa na zina, kuma zai samu wannan rabo babu makawa, sai dai ba za a kama shi da laifi ba, har sai idan ya gaskata abin da idonsa ko kunnensa ko hannunsa ko kafarsa suka jiyar da shi, ta hanyar yin amfani da farjinsa don biyan bukatar wadannan gabbai. Wannan shi ne ma’anar fadin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) a karshen Hadisin, “Farji shi yake gaskata haka ko ya karyata.” (Sharhin Sahih Muslim na Imam Nawawi Juz’i na 16, shafi na 216).



Zamu kwana a nan, a dakacemu 

Rubutawa:- Dr, Muhammad Rabi’u Umar Rijiyar Lemo, 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Post a Comment (0)