MATSAYIN ZAKKA A SHARI'ANCE 3


_*⚖️MATSAYIN ZAKKA A' SHARI'ANCE⚖️*_(3)

MA’ANAR ZAKKA:
DAKUMA DALILAN WAJABCINTA:

 Ma’anar Zakka a harshen Larabci shi ne Karuwa da tsarkaka.

Amma ma’anarta a shari’a kuwa, 

ita ce:
 Fitar da haKKin da ya wajaba daga dukiya yayin da ta kai nisabi ga wadanda suka cancanta.

 Zakka rukuni ce daga cikin rukunan Addinin Musulunci kamar yadda ya zo a Hadisi:

"بني الإسلام على خمس شهادة أن لا إلـه إلا الله وأن محمدا رسول الله وإقام الصلوة وإيتاء الزكاة وحج البيت وصوم رمضان" رواه البخاري ومسلم.

“An gina Musulunci a bisa abubuwa guda biyar; 
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, 
kuma Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah ne, 
da tsai da Salla da ba da Zakka 
da ziyartar Dakin Allah (Aikin Hajji) 
da azumtar watan Ramadan” 
(Bukhari da Muslim).

Zakka rukuni ne daga cikin rukunan Musulunci guda biyar.
Zakka ta kasu zuwa kaso biyu:

1-Zakka ta jiki (Wato zakkar fidda kai), bayaninta zai zo a nan gaba.

2-Zakkar dukiya.

DALILAN WAJABCINTA:

Zakka wajibi ce da nassin AlKur’ani, kamar yadda Allah (S.W.T.) Ya ce :

   "وآتوا الزكاة"" Ku bayar da Zakka" (Al Bakara :110).

A hadisi, Annabi (SAW) Ya ce wa Mu’azu a sanda ya tura shi Yemen:

"وأعلمهم أن الله افترض عليهم صدقة تؤخذ من أغنيائهم فترد في فقرائهم"متفق عليه 
 
Wato:"Ka sanar da su cewa Allah (SWT) Ya wajabta Zakka a kansu, 
wadda za a karba daga mawadatansu a bayar da ita ga matalautansu”
 (Bukari da Muslim suka rawaito )

Haka kuma musulmi gaba daya sun hadu a kan wajabcinta.

_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Sadiq Salihu Kabara*

Gabatarwa_
_*ALHUSEIN ABBAN SUMAYYA*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Post a Comment (0)