ILLOLIN ZINA, LUWAƊI DA MAƊIGO 3

*03→ILLOLIN ZINA ,LUWADI DA MADIGO*

*Illolin zina:*

Babu ko shakka duk mai hankali ya san cewa zina tana tattare da illoli masu yawa, wadanda suke shafar mazinacin ko mazinaciyar, ko su shafi al’umma gaba daya. Ga wasu daga cikin illolinta:


1. Zubar da mutunci da jawo wa kai kaskanci: Duk matar da ta yi zina, to ta jawo wa kanta da danginta da mijinta kaskanci, ta kuma zubar musu da mutumci a idon duniya. Idan har ta samu ciki ta haihu, sannan ta kashe dan, to ta hada laifi biyu, laifin zina da laifin kisan kai. In kuma ta bar shi, to kuma ta shigar wa mijinta ko danginta, wanda ba ya cikinsu. Idan kuwa mai zinar namiji ne, to ya lalata mace, ya jawo mata lalacewa da tabewa, wanda hakan lalata duniya ne gaba daya.


2. Zina ta hada dukkan sharri gaba daya: Saboda a cikin zina akwai rashin tsoron Allah; rashin kunya; rashin tsantseni; rashin cika alkawari; karya da butulci da sauransu. Duk kuwa wadannan munanan halaye ne a Musulunci.


3. Zina tana haifar da cututtuka da mutuwar zuciya da sanya zuciya ta zama baki-kirin da samun kai cikin damuwa da rashin kwanciyar hankali da nutsuwa a koyaushe. Bincike ya tabbatar da cewa cutar kanjamau ta fi yaduwa ta hanyar zina fiye da kowace hanya da ake iya daukar cutar daga gare ta, sannan ta hanyar cutar akan kamu da miyagun cututtuka masu mugun hadari. 


4. Zina tana haifar da talauci da musiba a bayan kasa, saboda da duk namijin da yake mazinaci, to ba ya iya tattali, kullum kudinsa suna wajen matan banza, duk abin da zai samu, ba zai amfanu da shi ba yadda ya dace, a banza zai tafi. Haka nan duk matar da take mazinaciya ce, duk abin da ta samu yana karewa ne wajen yadda za ta janyo hankalin maza zuwa gare ta, Allah kuma Zai zare wa dukiyarta albarka.

Zamu kwana a nan, a dakacemu 

Rubutawa:- Dr, Muhammad Rabi’u Umar Rijiyar Lemo, 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```

Post a Comment (0)