ILLOLIN ZINA, LUWAƊI DA MAƊIGO 4


*04→ILLOLIN ZINA ,LUWADI DA MADIGO*

5. Zina tana kawo kiyayya da gaba a tsakanin masu yin ta da sauran mutane. Allah Madaukakin Sarki Yana cire kwarjininsu da girma daga idon mutane, saboda haka ne za ka ga karamin yaro yana fada da sa’an kakansa a wurin neman mata, saboda ba ya kaunarsa, ballantana ya girmama shi.

6. Zina tana jawo rashin amincewa da mai yin ta. Kowa yana yi masa kallon maha’inci, mayaudari.

7. Zina tana haifar da wari daga jikin mai yin ta. Ba wanda yake jin wannan wari sai mutanen kwarai.

8. Zina tana jawo azaba mai tsanani ga mai yin ta idan bai tuba ba a duniya da Lahira. A duniya jefewa ko bulala da bakuntarwa; a Lahira kuwa makomarsa wuta. Allah Ya kare mu.

9. Zina tana kawo rugujewar gida da daidaicewar iyali, sannan tana kawo lalacewar tarbiyya.

10. A cikin zina akwai tozartar da dangantaka da sanya cin dukiyar mutane ba da hakki ba, domin kuwa duk dan da aka samu ta hanyar zina, abin da zai gada ba hakkinsa ba ne.


Zamu kwana a nan, a dakacemu 

Rubutawa:- Dr, Muhammad Rabi’u Umar Rijiyar Lemo, 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Post a Comment (0)