KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE: 14/FEBRUARY/2020-MLDY

KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:

14/FEBRUARY/2020-MLDY

MAI TAKEN:-- *[[SALLA GINSHIKIN ZAMAN LAFIYA]]*

➖NA KASASHI GIDA 7
.
.
1️➖MUQADDIMA
   Yaku bayin ALLAH! kuji tsoron ALLAH kusani salla itace mafi karfin rukunnan musulunci bayan tauhidi,
ALLAH SW ya ambaci SALLA da sunan IMANI, [SRT BQR-143]
ALLAH SW yayiwa ANNABI ISA wasici da SALLA, [SRT MRYM-31]
.
.
2️➖KARKASUWAN MASU WASA DA SALLA
   Wasu baswa salla sam sam, wasu suna wasu suna barin wasu- dukkan biyun kafircine a fatawowin dayawa daga Malamai ciki harda Malaman SAUDIYYA na zamani irinsu BN BAZ da UTHAIMEEN, 
Wasa da jam'i kuma kuskurene da takaita lada, 
.
.
3️➖HUKUNCEN TARIKUS SALAT A DUNIYA
 
Mun tsakuro daga littafin SHEIKH UTHAIMEEN mai suna (رسالة في حكم تارك الصلاة) cewa= TARIKUS SALAT ba'a bashi aure ko walicci, ba'a cin yankarsa, ba gado tsakaninsa da 'yan uwansa musulmi, baza'a sallaci gawansaba baza'a roƙa masa gafara da rahamaba, baza'a bizneshi a maƙabartan Musulmai ba, baza'a ɗaukeshi ɗan'uwa a addiniba saidai ma a barranta daga gareshi. 
.
.
4️➖HUKUNCEN TARIKUS SALAT A LAHIRA
ALLAH SW yace <<bone ya tabbata ga masallata masu sha'afa daga barin salla>> [SRT MA'UN 4-5]
ALLAH SW yace <<masu tauye salla zasu haɗu da Gayya>> [SRT MRYM] IBN MAS'UD yace= kwarine a jahannama mai zurfi da mugunya da azaba, 
ALLAH SW zaice <<me yasaku cikin SAQAR? sai suce bamu kasance cikin masallataba>> [SRT MDTSR-42-43]
ANNABI SAW yagani a mafarki an kwantarda wani anata ruguza kansa da dutse yatambaya akace masa mai kwanciya barci baiyi sallar farillaba, {SAHIH BHR} 
.
.
5️➖DAGA KHUSU'IN SALAF A SALLA
Ance da AMIR IBN ABDULQAIS AL-ANVARY= kana zancen zuci cikin salla? sai yace= Eh, ina zancen zucin tsayuwata agaban ALLAH

ZAINUL ABIDEEN yana cikin salla agidansa yayi suja sai gobara yakama gidan har aka kashe gobaran bai dagoba, aka tambayeshi bayan ya idar sai yace= tunanin wutar lahirace ta mantar dani wutan duniya

An sace mayafin YAQUB IBN YAZEED ALBASRY yana salla aka dawo dashi duk bai saniba, 

IBRAHIM TAIMY in yayi sujada don nutsuwa yakan zanto tamkar sashin gini har tsuntsaye kan dira a gadon bayansa, bayanannan dubi littafin (نزهة الفضلاء تهذيب سير أعلام النبلاء) na MUHD IBN HASAN IBN AQEEL

6️➖SALLANE MAFI GIRMAN GINSHIƘIN ZAMAN LAFIYA DA KWANCIYAR HANKALI

ALLAH SW yace <<da anbaton ALLAH zuciya ke nuutsuwa>> [SRT RA'AD-28]

ALLAH SW yace <<katsaida salla don anbatona>> [SRT ƊAHA-10]

ALLAH SW yace <<wanda yakau dakai daga anbatona yanada rayuwa ta kunci>> [SRT ƊAHA-124]

ALLAH SW yace <<kunemi taimakon ALLAH da yin hakuri da kuma salla>> [SRT BQR-45]

Shiyasa ANNABI SAW ke cewa= tashi BILAL kahutarda zuciyarmu ta hanyar salla, {AHMD} 
ANNABI SAW yace "an sanya sanyin idona acikin salla" {NASA'I} 
HUZAIFA IBN YAMAN yace= Idan babban al'amari yatunkarowa ANNABI SAW sai yagaggauta yin salla, {AHMD} 
TSABIT yace= idan masifa yasaukowa ANNABAWA sukan gaggauta yin salla! 
(TAFSIR IBN KATSEER)

KAKARMU SARATU matar BABANMU IBRAHIM A/SLM yayinda tafada tarkon sarki azzalumi salla raka'a 2 tayi sai ALLAH SW yaturo MALA'IKA yayita doke sarkin
Mu fa ayau idan ance Bom ya tashi boko haram sun kai hari Masu garkuwa sun saci mutane➖madadin mu garzaya zuwa sallah raka'a 2 yadda ANNABI SAW keyi- bazamuyiba- kawai sai mu garzaya zuwa WAYAR SALULA- FACEBOOK- WHATSUP- HABAICI- ZAMBO- ZAGI
Madadin salla da akace muyi sai muka canza da abinda bashi ALLAH yaceba
Shin meyasa kafin kayi posting din abubuwannan bazakayi sallaba?
Yanar gizone zai share mana hawaye ba ALLAH ba?
Donme bazamu fara da salla kafin yanar gizoba?

SHEIKH ABDLH IBN SA'AD AL-FALIH cikin littafinsa (الصلاة أهميتها وفضلها) yace= Dan uwana- domin shi salla sadarwa tsakanin bawa da Ubangijinsa, ya dace ga Musulmi idan yafaɗa cikin damuwa- yanemi isarda sakon kukansa zuwaga ALLAH ta hanyar salla, domin a hannunsane cikakken mulkin sammai da kassai, shine ke cewa abu- kasance sai yakasance, shike amsawa mai damuwa da kuma yaye masifu, 
ALLAH SW yace= <<shin wa ke amsawa mabukaci in yarokeshi kuma yake yaye damuwa kuma yake sanyaku mamaya? Shin akwai wani ALLAH ne banda ALLAH? kaɗanne masu wa'azantuwa>> [SRT NML-62]
.
.
7️➖RUFEWA
IMAM AHMD cikin littafinsa (كتاب الصلاة) yace= Kasonka da matsayinka a Musulunci gorgodon matsayinka a salla. 
.
.
Sirrin zaman lafiyar SAUDIYYA musammanma harami 2 wato MAKKA da MADINA shine salla, 
Haba dan'uwana- gashican inda ake ninninka masa kowace sallarsa akan naka sau 100,000 baiyi sakaciba- to kai meyasa sakaci
.
.
YA ALLAH KAZAUNARDA JIHOHIN BORNO, YOBE, ZAMFARA, KATSINA, KADUNA, JIGAWA, SOKOTO da dukkan 9jry lafiya cikin aminci kuma kamurkushe duk wanda ya addabi al'umma yake kashesu ko sacesu yahanasu sakat
AMIN......
 _#Abubakar BN Mustafa Biu_

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 Ga masu sha'awar Shiga Zauren *MIFTAHUL ILMI* WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248

Post a Comment (0)