SALLAR ISTIKHARA DA HUKUNCE-HUKUNCEN TA 01


*~ SALLAR ISTIHARA DA HUKUNCE-HUKUNCENTA~01*


Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya shar’anta wa bayinSa abin da zai amfane su a addininsu da duniyarsu da Lahirarsu. Tsira da amincin Allah su kara tabbata bisa mai karantar da mutane alheri, mai nuna musu hanyar da’a, bai bar wani al’amari da zai kusanta su zuwa ga Allah Madaukaki face ya shiryar da su gare shi, kuma babu wani al’amari da zai nesanta su daga Allah Madaukaki face ya tsoratar da su a kansa.


’Yan uwa Musulmi assalamu alaikum warahamatullah. Barkanmu da saduwa a wannan fili mai albarka. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya dubi halin da muke ciki Ya kawo mana dauki wajen fallasa mutanen da suke kokarin jefa al’ummar kasar nan a cikin yaki marar manufa da tushe. Allah Ka gaggauta tona asirin masu wannan mugun shirin don kubutar da jinin bayinKa salihai. Ba mu da wani karfi ko dabara face komawa gare Ka. Ka isar mana abin da ba za mu iya ba.

Bayan haka, a wannan karo za mu yi bayani ne kan Sallar Istihara, wadda daya ce daga cikin sallolin da Manzon Allah (SAW) ya sunnata wa mabiyansa domin mika wa Allah zabi kan kowane abu da suke nema ko ya bijiro musu. Kuma saboda muhimmancinta Manzon Allah (SAW) ya kasance yana koyar da sahabbai kanta kamar yadda yake koyar da su karatun Fatiha kamar yadda nassi ya tabbatar.

Sallar Istihara Sallah ce da bawa ke neman zabi da shawara daga Ubangijinsa, da ita yana tabbatar da ibada ga Allah Madaukaki, ya gina gaskiyar niyyarsa da yakininsa da amincinsa ga Ubangijinsa.

Sallah ce wadda take sadar ruhin bawa ga Mahaliccinsa, Sallah ce da ke ba mumini natsuwa, ta kara masa imani a kan imaninsa. Sallah ce da bisa kudirin Allah da iradarSa mai karfi ke gudana tare da tabbatar da Musulmi ka duga-dugansa yana mai yarda da mika wuya ga hukuncin Allah da kaddararSa.

Sai dai kash! Maimakon al’ummar Musulmi su mayar da hankali ga yin wannan Sallah mai daraja, a cikin duk al’amuran da suka bijiro mus, sai suka gwammace zuwa wurin bokaye da miyagun malamai suna tsafe-tsafe da tsubbace-tsubbace, ba tare da tunanin wadannan abubuwa alheri ne a gare su ko akasin haka ba.

Da wannan sai al’amuran al’umma ke ta ci gaba da lalacewa da balbalcewa da susucewa, har ta kai a yanzu mutane ba su ba Allah damar Ya zaba musu mafi alherin abin da suke nema, a’a duk abin da ransu ya darsa musu daidai ne. Sun dauka duk abin da suke so ko zuciyarsu ta kawata musu shi ne alheri ko shi ne mafi alheri. Kalla! Ba haka ba ne, a komai zabin Allah ne mafi dacewa ga kowane bawa, saboda kowane bawa mai rauni ne ga hangen abin da ka je ya zo, jahili ne ga abin da yake boye, mai kai-kawo da taraddadi ne a abubuwan da yake gudanarwa.

Don haka ne Allah Ya shar’anta wa bawa cewa idan wani abu ya bijiro masa ko aka bijiro masa da wani aiki ko wani muhimmin al’amari, to ya mika wa Allah zabi, ya shawarci Mahaliccinsa, Shi Madaukaki Shi ne Mafi sanin hakikanin al’amura, Shi Ya san natijarsu da amfaninsu da cutarwarsu da alherinsu da sharrinsu a duniya da Lahira, domin Shi ne Mafi sanin abin da ke boye.
“A wurinSa mabudan gaibi (abin da ke boye) suke, babu wanda ya sansu face Shi. kuma Ya san abin da ke cikin sararin duniya da abin da ke cikin (ruwan) teku. Babu abin da ke faduwa na daga ganye face Ya san shi, kuma babu wata kwayar halitta koda kamar komayya ce da ke cikin duffan kasa ko wani abu danye ko busasshe face (Allah Ya sanya shi) a cikin wani littafi mabayyani.”
Don haka idan bawa ya yi himmar yin wani abu ko aka bijiro masa da wani al’amari kamar aure ko aiki ko kasuwanci ko tsayawa takara ko duk wani abu, to wajibi ne ya mika wa Ubangijinsa zabi wanda shi ne ake kira Istihara kafin ya fara wannan abu, kuma hakan zai faru ne kamar haka:
Zamu chigaba da yardar Allah... 

Rubutawa:- Salihu Is’hak Makera
Gabatarwa:- Salis kura

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Post a Comment (0)