SALLAR ISTIKHARA DA HUKUNCE-HUKUNCEN TA 02

🔹 *ISTIHARA DA HUKUNCE~HUKUNCEN TA* 

 *_02_*
chigaba....
 
1. Ya kawo dukkan sharuddan Sallar Nafila, kuma su ne sharuddan Sallah in aka cire sharadin shigar lokaci.

2. Ya yi Sallah raka’a biyu na nafila da niyyar Sallar Istihara, kada ya furta komai bayan kabbara, domin niyya muhallinta zuciya ce, yin furuci da ita al’amari ne kirkirarre, Manzon Allah (SAW) bai aikata haka ba, haka sahabbansa ko wani daga cikin shugabannin Musulmi da ake koyi da su. Sannan ya fuskanci Allah da zuciyarsa – a cikin sallarsa- yana mai kankan da kai da tawali’u.

3. Ya yi addu’ar Istihara, wannan kuma a bayan idar da Sallar ce. Ga yadda addu’ar take:
“Allahumma inni astakhiruka bi ilimika, wa astakdiruka bi kudiratika, wa as’aluka min fadlikal azim. Fa innaka takdiru wa la akdiru, wa ta’alamu wa la a’alamu wa atna allamul guyub. Allahumma in kunta ta’alamu anna hazal amru – ya ambace shi ko ya fadi abin da yake so- khairul li fi dini wa ma’ashi wa akibatu amri, fa kadirhu li wa yassirhu li, summa barikli fihi. Wa in kunta ta’alamu anna hazal amru- ya ambace shi ko ya fadi abin da yake so- sharrun li fi dini wa ma’ashi wa akibatu amri fasrifhu anni, wasrifni anhu, wakdirlil khaira haisu kana, summa radini bihi.”

Ma’ana: “Ya Ubangiji! Lallai ni ina neman zabinKa bisa iliminKa, na mayar maKa damar Ka yi amfani da ikonKa, kuma ina rokonKa daga falalarKa mai girma. Kai ne Kake da iko, ni ba ni da wani iko, Kai ne Kake da sani, ni ba ni da sani, kuma Kai ne Mafi sanin abubuwan da suke boye. Ya Ubangiji! Idan Ka san wannan al’amari- ya ambace shi ko ya fadi abin da yake nufin yi- alheri ne gare ni a cikin addinina da rayuwata da karshen al’amarina, to Ka kaddara min (ka ba ni) shi, kuma Ka saukake min shi, sannan Ka yi min albarka a cikinsa. Idan kuma Ka san wannan al’amari- ya ambace shi ko ya fadi abin da yake nufin yi- sharri ne a gare ni a cikin addinina da rayuwata da karshen al’amarina, to Ka kawar da shi daga gare ni, kuma ka kawar da ni daga gare shi, Ka kaddara min alherin a duk inda yake, kuma Ka yarda min da shi.”

4. Ya kasance sikka wato amana ko yardarsa ga Allah babba ce, tawakkalinsa wato dogara ga Allah da yake da ita ta zamo ta gaskiya ce, kuma ya kasance yana da yakinin Allah zai shiryar da shi zuwa ga abin da ya fi zama alheri, sannan ya zamo mai sauraren a karba masa.

5. Ya kasance mai kaurace wa dukkan abubuwan da suke hana karbar addu’a.
Wani yana iya tambaya shin ita ma addu’a tana da abubuwan da suke kawo a ki karbarta ce?

Amsa ita ce lallai akwai abubuwan da suke sa Allah Ya ki karbar addu’a. wadannan abubuwa sukan kasance shamaki su hana a karbi addu’ar bawa. Kuma ita Istihara addu’a ce, don haka wajibi ne a kan Musulmi ya san sharuddan addu’a, ya lizimci ladubbanta, ya guji abubuwan da suke hana karbarta, domin a karba masa Istihararsa a biya masa bukatarsa.

Da yawa mutane sukan ce sun yi ta yin addu’a amma ba su ga biyan bukata ba, ma’ana ba akarba musu ba, to wannan yana faruwa ne saboda rashin bin sharuddanta da suke yi, ko aikata wasu abubuwa da suke hana karbarta, ko kuma Allah Ya jinkirta karbar saboda wata maslaha da Allah Ya lura da ita Ya jinkirta karbar zuwa wani lokaci ko sai a Lahira su ga amfanin hakan kamar yadda nassi ya nuna....

Rubutawa:- Salihu Is’hak Makera
Gabatarwa:- Salis kura 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```

Post a Comment (0)