SALLAR ISTIKHARA DA HUKUNCE-HUKUNCEN TA 03


🔹 *ISTIHARA DA HUKUNCE~HUKUNCEN TA* 

*03*
 
→Abubuwan da ke hana karbar addu’a ciki har da Istihara

1. Ya kasance mutum yana cin haram ta hanyar kwace ko danne hakkin wadansu ko mu’amala da riba, ko cin dukiyar mutane da karya da zalunci ko algushu ko rashin cika alkawari a fannin kasuwanci ko sana’a ko makamancin haka, ta yadda kudin haram zai shigo masa, ya ci ko ya sha ko ya yi sutura da su, Allah Yana kin karbar addu’a ko Istihara daga irin wannan mutum.



An karbo daga Abu Huraira (RA) ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ya ku mutane! Lallai Allah Mai tsarki ne, ba Ya karbar komai sai mai tsarki. Kuma lallai Allah Ya umarci muminai da abin da Ya umarci Manzanni, sai Ya ce: “Ya ku Manzanni! Ku ci daga tsarkakan abubuwa, kuma ku yi aiki nagari. Lallai ne Ni, game da abin da kuke aikatawa Masani ne.” Kuma Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku ci daga tsarkakan abubuwan da Muka azurta ku.” Sannan sai ya ambaci wani mutum mai doguwar tafiya, mai gizo mai kura, yana daga hannuwansa sama, (yana cewa) Ya Ubangiji! Ya Ubangiji! Alhali abincinsa haram ne, abin shansa haram ne, tufafinsa na haram ne da haram aka raine shi, ta yaya za a karba masa?”

2. Ya zamo Istiharar ko addu’ar an yi ta, don neman bukata ta sabo da zunubi ko aikata zalunci. Idan ya zamo haka ba za a karba wa mutum ba, kamar mutum ya yi Istihara a cikin abin da akwai cutarwa ga Musulmi ko jawo zalunci ga mumini.

An karbo daga Ubadatu dan Samit (RA) cewa, lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Babu wani Musulmi a bayan kasa da zai yi wata addu’a face Allah Ya ba shi ita, ko Ya kawar masa da wani mugun abu gwargwadon abin da ya roka, matukar dai bai yi addu’a kan zunubi ko yanke zumunta ba. (Sai wani mutum ya ce, don haka za mu yawaita -addu’a). Sai (Manzon Allah) ya ce, “Allah Ya fi yawaitawa.” Tirmizi ya ruwaito.

Ma’ana Allah Ya fi yawaita karbar addu’a daga bawa fiye da yawan addu’ar abin da ya nema komai yawansa.

3. Barin yin umarni da aikin alheri da hana abin ki.
Yana daga cikin abubuwan da ke hana karbar addu’a, Musulmi ya kaurace wa yin nasiha ga ’yan uwansa Musulmi, ba ya umartar su da aikin alheri ba, kuma bai haninsu daga abin ki ba.

Domin haka idan bawa na son Allah Ya karba masa addu’a, ya wajaba a kansa ya kasance mai istikama a halinsa, mai gaskiyar buri, mai umarni da alheri da hana abin ki. Umarni da alheri da hana munkari bai takaita ga wata kungiya ko jama’a ba, a’a yana daga cikin wajiban da ke kan kowane Musulmi a gidansa game da iyalansa da wadanda suke karkashinsa ko a cikin dukiyarsa da ’yan uwansa ko wadanda yake tare da su da sharadin ikon hakan, kuma yana da hikima, don gudun kada garin gyarar gira a rasa ido, wato ya zamo kada ya jawo barna mafi girma daga gyaran da yake son yi.

An karbo daga Huzaifa (RA) daga Annabi (SAW) ya ce: “Na rantse da wanda raina ke hannunSa, kodai ku yi umarni da alheri kuma ku hana abin ki, ko ya yi kusa Allah Ya aiko da ukuba a kanku, sannan ku yi ta rokonSa amma Ya ki amsa muku.” Ahmad da Tirmizi suka ruwaito.

4. Yin ta’adda (wuce iyaka) a cikin addu’a, kamar daga murya ko kirkirar bidi’a a cikinta ko yin shirki ga Allah a cikin addu’ar ko ya mayar da zuciyarsa zuwa ga wani daga cikin bayin Allah. Allah Madaukaki Ya ce: “Ku kira (roki) Ubangijinku kuna masu kankan da kai kuma a boye, lallai Shi ba Ya son ’yan ta’adda (masu wuce iyaka a addu’a).” Don haka duk wanda ya wuce iyaka a addu’a Allah ba Ya sonsa, kuma Allah ba zai karbi addu’a daga wanda ba Ya so ba.

Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce: “Da sannu za a samu wadansu mutane suna ta’adda (wuce iyaka) a cikin addu’a.” Ahmad da Abu Dawud suka ruwaito.

5. Ya kasance mai addu’ar gafalalle daga Allah, mai juya wa addini baya, mai mance umarce-umarcen Allah, mai hawan kawara ga hane-hanen Allah. Ya zamo yana sabon Allah a lokacin da yake cikin yalwa sai an shafe shi da wata musiba ya rika cewa: Ya Ubangiji! Ya Ubangiji! Ta yaya za a karba masa?

Duk wanda ya mance Allah a lokacin da yake cikin yalwa, Allah zai mance da shi a lokacin da ya shiga cikin tsanani. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Duk wanda ke farin cikin Allah Ya karbi addu’arsa a lokacin tsanani da bakin ciki, to, ya yawaita addu’a a lokacin da yake cikin yalwa.” Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ku roki Allah kuna masu yakinin za a karba muku. Ku sani Allah ba Ya karbar addu’a daga wanda zuciyarsa ta gafala ta wofinta daga Allah.” Timizi ya ruwaito Hadisan biyu

6. Saba wa wasu hukunce-hukuncen shari’a daga cikinsu akwai:
- Yin shiru daga miyagun halayen matar aure da kin sake ta 
- Bayar da bashin dukiya ba tare da kafa shaida ba.
- Bayar da dukiya ga wawaye koda sun kasance ’ya’ya da ’yan uwa ne.

Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mutum uku za su yi ta rokon Allah Mai girman daraja amma ba zai karba musu ba: mutumin da yake auren mace mai mugun hali amma ya ki sakinta da mutumin da yake bin wani bashi amma bai kafa shaida a kai ba da kuma mutumin da ya ba wawa dukiyarsa, alhali Allah Madaukaki Yana cewa: “Kada ku ba wawaye dukiyarku.” Hakim ya ruwaito shi ya inganta shi, sannan Zahabi da dahhawi da wadansu sun bi shi a kai, kuma Albani ya inganta shi a Silsila, Hadisi na 1850.

Zamu chigaba da yardar Allah ....

Rubutawa:- Salihu Is’hak Makera
Gabatarwa:- Salis kura 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Post a Comment (0)