TAMBAYA TA 034

Tambaya
:
Shin kamar waɗanne irin abubuwa ne suka Halatta da kuma waɗanda suka Haramta akan mace mai-Takaba tayisu??
:
Amsa:
:
To da farko dai hukuncin da ke kan mace Mai-Takaba shi ne, daga lokacin da taji labarin Mutuwar Mijinta za ta zauna tayi takaba ne a nan gidan da take zaune da Mijinta kafin ya rasu, kuma za tayi watanni huɗu da kwana goma ne, wato adadin kwanaki 130 kenan, kuma yin wannan Idda Wajibi ne, kamar yadda Allah(ﷻ) yafaɗa: acikin 
Al-Ƙur-āni Mai-Girma:
:
وَالَّذِينَ يُتَوَفَّوْنَ مِنكُمْ وَيَذَرُونَ أَزْوَاجًا يَتَرَبَّصْنَ بِأَنفُسِهِنَّ أَرْبَعَةَ أَشْهُرٍ وَعَشْرًاۖ....(سورة البقرة/234)
Ma'ana:
Waɗanda suka mutu daga cikinku (Muminai) kuma sukabar Matayensu, to (Matan) zasu zaunane dakansu (suyi takaba) tsawon watanni huɗu da kwana goma……
:
Amma idan Mai-Ciki ce to da ta haife abin da ke cikinta shikenan ta gama takabarta, sannan ana buƙatar Mai-Takaba ta nisanci dukkan wasu abubuwa da suke da alaƙa da kayan ado, wato kamar irin su:
:
①-Zobe,
②-Sarƙa,
③-Kwalli,
④-Turare,
⑤-Agogo,
⑥-Awar-waro,
⑦-Tufafin ado,
:
Da dai sauran kayan ado, sai dai ya halatta ga mai takaba ta aiwatar da wadansu abubuwa irin wadanda dole ta na buƙatuwa zuwa garesu kuma bata samu wanda zai ɗauke mata nauyinsu ba, kamar zuwa Kasuwa don sayen wasu abubuwa na buƙatunta, ko kuma zuwa wajen aiki don neman abinda za ta ci ita da 'ya'yanta, da dai Makamantan waɗannan, Amma ba a son mai takaba take fita da daddare sai in da wata larura mai ƙarfi sosai, kamar ace Ɓarayi su haura gidan da take ko kuma rushewar ginin gidan, ko kuma wuta ta kama agidan, da dai waɗansu abubuwa makamancin haka,
:
Sannan ana buƙatar Mace Mai-Takaba ta nisanci dukkan wani nau'i na kayan ado, Sannan ba za ta yi amfani da kowanne irin nau'i na turare ba, na ruwane ko kuma na hayaƙi, don ta sanya ajikinta ko atufafinta, sai dai idan tayi Al'āda to za ta iya amfani da irin turaren da Mata suke amfani da shi dan su tsaftace kansu, sannan mai takaba ba za ta chāɓa ado ba, kuma ba za ta riƙa yin wanka da irin sabulun nan mai ƙanshi sosai ba, ko kuma ta ke amfani da man-shafawa me ƙanshi sosai ba, amma zata iya yin wanka a kullum da normal sabulu, kuma za ta iya shafa normal man shafawa amma waɗanda ba masu ƙanshi sosai ba, kuma ta na da damar ta sanya duk irin kalar tufafin da take so ba wai sai baƙaƙen kaya kaɗai ba, domin kuwa sanya baƙaƙen kaya a duk lokacin da wani abin baƙin ciki ya faru hakan bashi da wani asali a Shari'a, kawai wasu Mutane ne suka ƙirƙiro (Bidi'ar hakan) suka ɗorawa kansu, danhaka ya halatta mai takaba tasa kowanne irin Nau'in Tufafi matuƙar dai ba ado zata chaɓa da su ba, Sannan ba a son mai-takaba ta fita waje don taje ta yiwa wasu jāje ko ta'aziyya a wani gidan,
:
Hakanan ya halatta ga Mai-Takaba tayi dukkan abin da yake dama asali halal ne a gareta ta yi su kafin ta shiga takaba, kamar yin magana da wasu maza waɗanda ya halatta tayi magana da su, ko kuma zuwa Asibiti don a duba lafiyar ta.
:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
              Daga Zaυren
             Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
           Mυѕтαρнα Uѕмαи
              08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/

Post a Comment (0)