*_MIJINA BAYA GAMSAR DANI_*
~~~~~
*_TAMBAYA❓_*
----
*_Assalamu alaikum_*
_Tambayata a nan ita ce, ni mijina ba ya biya min bukata a shimfida. Ma’ana; ta wajen jima’I; mu na fara saduwa idan ya samu biyan bukatar kansa shikenan sai ya daga ni ko da kuwa ban ji dadi ba. Ba ruwansa da sha’awar da zan kasance a ciki kuma ba ruwansa da damuwar da zan yi. Shi kansa kawai ya sani. Haka ma gobe idan ya zo zai kuma yi. Abin nan ya na matukar damu na har yana neman jefani ga halaka shi kanshi hausinsa nake ji dan Allah mene mafita?._
```Sannan don Allah ku tayani da addu'a Allah ya tsareni da faɗawa halaka```
*_AMSA:_*
----
Haƙiƙa wannan matsalar ma'aurata da dama suna fama da ita musamman hausawa ko ince waɗanda basu gama fahimtar haƙƙoƙin aure ba wasu kuma rashin lafiya ce amma meyasa bazasu nemi magani ba...?
👉🏼
Ƴar uwa ya na daga ilimin da ya kamata a dinga sanar da mutanen da su ka mallaki hankalin kansu shi ne ilimin jima’i a Musulunci.
::
Manzon Allah (saw) ya ce, kada dayanku ya afka wa matarsa, kamar yadda jaki ya ke afkawa jaka. Idan dayanku zai je wa iyalinsa, ya kamata ya aika dan aike, wato ya kamata a ce kafin ya kwanta da matarsa su gabatar da duk wani wasa da zai motsa musu sha’awa, domin samun gamsuwar su kansu ma’auratan. Sannan idan mutum ya sadu da matarsa, bai kamata ya yi gaggawar fitar da gabansa daga cikin matucinta ba har sai wannan matar ta sami gamsuwa daga gare shi, saboda wata matar ba ta samun gamsuwa a daidai lokacin da shi mijin ya sami gansuwa, har sai ya jira ita ma matar ta sami tata gamsuwar.
..
Wani mutumin ba ruwansa; da zarar ya sami gamsuwa da matarsa koda a iya wasan da su ke yi ne, to fa shi ya gama, ba ruwansa da ita. Shi ba abinda ya yi ma sa zafi. Kun ga wannan shi ne karshen rashin adalci. Wata matar kuma ta na da doguwar sha’awa, saboda haka, idan mijinta bai yi wasa da ita ba, sannan bai jira ta samu gamsuwa daga gare shi ba, to maniyyin da ya ke jikinta ba zai sauko ya hadu da nasa ba, sai dai ya tsaya ma ta a mararta. Daga nan kuma sai
*ciwon mara,*
*ciwon ciki,*
*ciwon kai,*
*warin gaba*.
Daga nan sai mace ta dinga tsintar kanta da rashin kuzari da rashin walwala. Ta rasa abin da ya ke yi ma ta ɗaɗi, kuma wannan ke sa mace ta dinga jin haushin mijin da tsanar mijin. Sai ka ga mace ba ta girmama miji yadda ya kamata. A rasa dalili. Nan kuwa rashin ba ta hakkinta a shimfida ne ya jawo ma sa.
Wasu ma har sukai ga neman maza zuwa ga aikata zina Allah ya kiyaye Ameen
🔗
Sannan ya kamata mu sani cewar mata kala-kala ne kamar yadda maza su ke kala-kala. Akwai mai karfin sha’awa, wacce idan ba ta sami daidai ita ba, akwai damuwa. Sai dai ka ga auren ya na kai kawo. Karshe dai sai an rabu hankalinta zai kwanta. Ba yin ta ba ne; haka Allah Ya yi ta. Haka su ma mazan, wani idan ya sami wata matar, da kanta za ta gudu. A-yi-a-yi ta dawo, ba za ta dawo ba, amma wata ta na kokari ta sanar da ’yan gidansu cewar ya fi karfinta.
_*Shawara ga mata da mazan da ba sa iya biya wa junan bukata;*_
Su sani ba sai ta kai su ga rabuwa ba. Idan ka san ba ka da juriyar da za ka iya biya wa matar ka bukata a shimfida ba, to ka dinga wasanni da ita sosai kafin ka shige ta, kuma ka tabbatar ka gane guraren da idan ka tattaba ma ta ta ke jin dadi sosai yadda kafin ku zo saduwa ka gama tayar ma ta da sha’awarta, ta fara jin dadi sosai. Ka ga ka na shigar ta, kafin ka biya bukatarka, ta gama jin dadinta. Za ka ji ta sharkaf; komai ya yi daidai.
_*Shawara ta biyu;*,
ka kasance mai neman maganin karin karfin mazakuta da kuzari yadda matar taka za ta ji ka da karfinka.
Uwar gida idan mijinki ya na fama da rashin karfin mazakuta ko ba ya biya miki bukatarki a shimfida sai ki yi ma sa wannan hadin, ki samu:
👇🏼
*Namijin goro*
*Tsintsiyar maza*
*Tatarida*
*’Ya’yan Dabino*
*Citta mai yatsu*
*Masoro*
*Barkono*
,,
_A hade, a dake su a tankade lukwui a dinga zuba ma sa a farfesu ko gasashshen nama ya na ci ko ki tafasa ma sa ki sa zuma ya dinga sha kamar shayi to insha Allah komau zaiyi daidai._
# ```Dafatan wanda akai dominsu zasu amfana Ameen```
*,"""""""""""""""",*
*_ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.*_
*--------------------------*
*_•Ga mai sha'awar shiga Zauren 📚Al'mar'atus'salihat _*📚
_*Ta whatsApp sai yayi cikakkiyar sallama tare da suna da Address nasa zuwa⬇ ga lambar mu*_
_*+2347037943539*_
```✍Abu Abdurrahman