TAMBAYA TA 69


TAMBAYA
=========
👇
Slm malam Dan allah hankalina atashe yake narasa yazanyi kabani shawara Dan allah Dan annabi ni budurwace kuma tunda nake bantaba sanin namijiba inasan aure amman iyayena basaso nayi yanzu Wai sainayi deploma kouma haryanzu bangama secondary ba ina sss 2 haryanzu sai shekara maizuwa zangama masu nemana sunanan dayawa yanzu haka wallahi malam akwai Wanda yake nemana ko yau akace yafito zaizo ashirye yake kuma shi ma aikicine likitane shi babbane yanada gidansa duk abinda ake nema yanadashi amman iyayena sunce saina gama deploma nan da shekara hudu kenan Dan bangama secondary bama haka narasa yazanyi musamman mahaifiyata itace take wannan bain shikuma babana maganarta yakeji kawayena babu Wanda baiyi aureba wasuma suna da yara uku amman saitace kada naje gidansu Dan kada su zigani akan aure narasa yazanyi bansan yazanyiba.
  Malam Dan allah kataimkamin kabani shawara.


AMSA
=====
👇
 Ba ke Za'a Baiwa Shawara ba. Mahaifanki ya kamata baiwa Shawara akan ya kamata Suyi Miki Aure.
 Musamman ma Mahaifiyarki. Tinda Mahaifinki Shima sai yadda Akayi Dashi. 
  Sannan Kuma Bari In Gaya Miki. Aure a irin gidanku Yana da wahala. Sabida duk wanda yazo neman Aurenki, Za'a ce Masa ke 'yar Mace ce. Koda Kuwa Baki da Wata Matsala.
  Domin Auren 'yar Mace Matsala ne. Duk Wanda ya Auri Yar Mace. Ba Zaiyi Tinkaho Akan Yayi Aure ba. Domin DQ zarar An sami Matsalar da Za a Iya gyara ta a Cikin Kankanan Lokaci. Uwarta Zatace Masa CIWON 'YA MACE NA 'YA MACE NE.
  Kinga kenan Akwai Damuwa. Ko da kina son Mijinki Mahaifiyarki Zata Iya Rabaki Dashi. Sabida ba yadda za'ayi Mace tayi Hukunci Akan Aure Kuma Tayi Adalci Wannan sai Namiji. Sai Kuma Ko Taimakon Allah. Namiji Shine Wanda Allah ya Bauwa Wannan Damar ya yin Hukuncin Tana a hannunsa. Amma kuma gashi Mahaifiyarki ta karbe daga Gareshi, Tinda shi Bashi da Wani Katabus a Gidansa 
  A takaice dai. Bai Wuce Ince Miki sai dai Kiyi Hakuri ba. Ko Kuma ki Sami Wadanda Mahaifiyarki Zata ji Maganarsa ta Umarceta domin ta Aurar dake.
 To Jama'a Wannan fa ga Ishemu Izina. Yarinya bata Gama Secondary ba. Amma Aure ne a gabanta. Harma tana takura Sabida Rashin Aure. To ina ga wadda har ta Gama secondary ko ta gama Jami'ah ba Aure? 
 Akwai Matsala fa. A yanzu Matsakar Aure ka kadai Ta Ishi Wannan Zamanin Namu.

Allah shine Masani.

✍️
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08137783797
Post a Comment (0)