TAMBAYA TA 71


*YA MATSAYIN KUDIN DA AKA TARA WA MARAR LAFIYA DON NEMAN MAGANI SAI YA RASU?*

*Tambaya*

Assalamu alaikum warahmatullahi Wa barakatuh. malam Dan Allah a warware mana wannan matsalar..mutum ne ba lafiya aka nema masa taimakon kudi domin dashen qoda,ana cikin haka ba'a kai ga gamawa ba sai yarasu,to wannan kudin nasa ne ma'ana yazama nashi zai shiga gadonshi?ko za'a iya taimakon wani mai tsananin buqata irin wannan larurar.?mun gode jazakumullahu khairan.

*Amsa*
Wa'alaykumussalam

Dukiyar da wani ya bayar don mamaci, kafin ko a bayan rasuwar sa ne, ita ma ta na cikin dukiyar gado.

A duba : [FATA'WAL LAJNATID DA'IMA; 16/473]

Wallahu A'alam

*Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)*

05/04/2020

Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*
Post a Comment (0)