TAMBAYA TA 70


Tambaya
:
Mene ne hukuncin sallar matar da ba ta rufe duga-duganta ba ko kuma wani sashe na jikinta ya bayyana ta na Sallah?
:
Amsa:
:
Abinda ya ke wājibi akan Mace idan zā ta yi Sallah shine, dōle ne ta rufe dukkan jikinta da tufāfi in banda fuskarta da kuma tāfukan hannāyenta, domin ita Mace dukkaninta al'aurace in banda wajen da aka tōgace, idan kuwa har wani ɓangare na jikinta ya bayyana kamar gāshin-kanta, Ƙwabrinta, ko wani sāshe na jikinta, to Sallarta ba ta inganta ba, domin kuwa Mαnzon Aʟʟāн(ﷺ) Yāce:
:
"لا يقبل الله صلاة حائض إلا بخمار"
MA'ANA
Aʟʟāн(ﷻ) bā ya karɓar sallar mātar da (ta balaga ta fāra) Haila sai (in tā lulluɓe kanta da jikinta) da mayāfi,
:
To amma dangane da abinda ya shāfi hukuncin fitowar dugā-dugan-Mace ko Ƙafāfunta acikin Sallāh anan Mālamai sunyi Saɓāni, Mazhabobin Mālikiyya, Shāfi'iyya, Hanābila da wani sāshe na Mazhabin Hanafiyya tāre da mafi yawa daga cikin Mālamai-Ma'abōta-Ilimi duk sun tafi ne akan cewa wājibi ne Mace ta suturce dugā-duganta idan zā tayi Sallāh, kuma sun kafa hujjarsu ne da Hadīsin Ummu-Salama wanda ta yi wa Annαвι(ﷺ) tambaya cewa:
:
"أتصلي المرأة في درع وخمار ليس عليها إزار؟ قال إذا كان الدرع سابغا يغطي ظهور قدميها"
MA'ANA
Shin Mace zā ta iya yin Sallah acikin mayāfi da doguwar riga ba tāre da tā ɗaura zane ba? Sai Annαвι(ﷺ) Yace eh idan ya kasance rigar yalwatacciyace za ta iya sauka har ƙasa ta lulluɓe bayyanar dugā-duganta:
:
Wato abin fahimta anan shine, kenan idan har tufāfin ba zai iya sauka har ƙasa ya lulluɓe dugā-duganta ba to Sallah ba ta yi ba kenan, saboda barin wancan Sharaɗin da a kayi,
:
Sai dai wani sāshe na Mazhabin Hanafiyya sun tafi akan cewa ba dole ba ne sai Mace ta rufe dugā-duganta a Sallah ba, sukace dugā-dugai ba al'aura ba ce, domin a bu ne da yake yawan bayyana a jikin Mace in tana cikin gida, sannan sukace bābu wani Hadisi da ya inganta daga Mαnzon Aʟʟāн(ﷺ) da yace dole sai Mace ta rufe dugā-duganta a Sallah, sukace wancan Hadisi da aka kafa hujja dashi akan wajabci, sukace Hadisi ne Mauƙūf, duk maruwaitansa sun tsaya ne akan Ummu-Salama ba su kai ga Annαвι(ﷺ) ba, danhaka sukace fuskar-mace da tāfukan-Hannayenta, da dugā-duganta duk ba al'aura ba ne a cikin Sallah, amma zā su iya zama al'aura idan ba a cikin Sallah ba ne,
:
To amma Sai dai magana mafi inganci kamar yadda mafi yawan Mālamai suka rinjāyar da ita shine, wājibi ne Mace ta lulluɓe ko ina a jikinta idan za ta yi Sallah, sai dai in ba ta sāmu tufāfin da za ta lulluɓe jikinta dashi ba, to anan sai ayi mata uzuri, domin kuwa akan iya yin Sallah tsirāra ma idan an rasa tufāfi, hakanan kuma idan Mace tā ɗauki lokaci mai tsawo tana Sallah ba tare da ta na lulluɓe dukkan jikinta ba sakamakon ba ta san cewa lulluɓe jiki a Sallah wajibi ba ne, wasu Mālaman suna ganin cewa dole ne sai ta rāma waɗancan sallolin, to amma magana mafi inganci ba zā ta rāmasu ba, domin itama anan za'a yimata uzuri ne da jāhilcinta, danhaka ba za ace dole sai tā rāmasu ba, sai dai tayi ƙoƙarin gyāra na gaba kawai,
:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
              Daga Zaυren
             Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
           Mυѕтαρнα Uѕмαи
              08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Post a Comment (0)