*Abubuwan Da Mata Suke Bukata A Zamantakewar Aure*
Da Yawa mata suna bukatar wasanni da maganganu masu dadi don kwantar da zuciya wanda zai sa su koda yaushe a cikin farin ciki da walwala, amma abin bakin ciki dayawa maza basu lura da wannan.
Ita mu'amala mai dadi itace zamantakewa, in kana so kaji dadin iyalinka to sai ka nuna mata kauna da janyowa a jiki.
Kalamai masu dadi da yabonta yana daga cikin abin da mata suke jin dadinsa, musammam in aka zo wajen gabatarwar ibadar aure domin haka zai motsar da sha’awarsu, hakan kuma zai sa ku samu gamsar da juna, rashin wadannan wasanni da kalamai da nuna kauna na iya haifar da rashin gamsuwa a tsakaninku a lokacin ibadar aure, kuma hakan ma yana iya haifar da kunci a aurenku.
Don haka sahihin maganin wannan matsala ga wasu matan shine sai mazan aurensu su runka daurewa wajen daukar lokaci mai tsawo suna masu wasanni da kalaman kauna ta yadda sha’awarsu za ta motsa sosai har a samu buyan bukatan aure.
Wabillahi Taufiq.
Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
Gabatarwa: *Abu Abdurrahman Ahmad Umar Rimi Assalafeey (Assalafeey Rimi)*
*- Zauren Macen Kwarai-*
*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a WhatsApp.*
