Hanyoyin da za ki bi don gyara auren ki


*Hanyoyin Da Zakibi Don Gyara Aurenki*

1- Aurenki ya zama domin neman yardar ALLAh ki ka yi ba don tara abin duniya ba.

2- Kada ki zama mai kwadayi wajen zaben mijin Aure.

3- Ki zabawa ‘ya’yanki uba ta hanyar auren wanda ki ka yarda da addininsa da dabi’unsa har ma da dangantakarsa.

4- Ki zama mai riko da addini a gidan mijinki.

5- kada ki zama mai kauracewa shimfidar mijinki.

6- Ki zama mai hakuri da halayyar mijinki.

7- Ki zama mai matukar biyayya ga mijinki.

8- Ki zama kwararriya wajen iya kwalliya kala-kala.

9- Ki zama kwararriya wajen iya girki kala-kala.

10- Ki zama kin iya barkwancin magana wajen baiwa mijinki dariya.

11- Kada ki zama mai rainuwa a cikin duk abinda mijinki ya baki.


Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Abdurrahman Ahmad Umar Rimi Assalafeey (Assalafeey Rimi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a WhatsApp.*
Post a Comment (0)