AKWAI HATSARI SOSAI

FITOWA TA (SHIDA)


HATSARIN AMFANI DA HANKALI WAJEN RUSA ABUN DA YA TABBATA A ALQUR'ANI KO YA TABBATA A HADISAN ANNABI (S A W)

Bayan mun keto bayani mai tsawo a Kan illar amfani da hankali wajen rusa abun da ya tabbata a shari'a, da bayanin da malamai sukai a Kan haka, zamu Fahimci masu wannan mummunar Aqidar kawai kokari suke su rushe a salin Addinin musulunci , shi yasa suka fake da yin haka.

DAN TA MORE ya rusa HADISAI da yawa saboda Yana ganin sun sabawa GURBATACCEN hankalinsa, kamar hadisan ANAS BN MALIK (R A), da hadisan MUGIRAH BN SHUUBAH (R A) daya rawaito na Shafa a Kan (KUFFI), da hadisin da JABIR ya rawaito na العنبر babban kifin nan da Allah ya Bawa sahabban annabi (s a w) a lokacin da sukai tafiya.

Duk wadannan hadisan da ire iren su ya karya ta su, saboda kwakwalwarsa mai virus ta kasa karbar sakon da yazo a cikin wadannan HADISAI.

Ina ma da zai koma wajen MANYAN malamammu ya tambayesu bayanin wannan HADISAI da ya fi masa a bun da yake yi a yanzu na kokarin rusa su. 

Yana daga cikin soki burutsu da rudewar DAN TA MORE zaka ga Yana ta da jijiyar wuya da bayanai marasa amfani ta hanyar kafa hujja da HADISAI Wanda basu ingantaba,.

Ya kawo hadisi da ya nuna Wai Sayyidina ABUBAKAR( R A) ya tattara HADISAI 500 yasa an konasu.

Sai yace : to Amma daga baya ya akai aka samu hadisan Annabi (s a w) da yawa?

GA HADISIN DA YA KAWO

وقد نقل الحاكم فقال : حدثني بكر بن محمد الصيرفي بمرو أنا محمد بن موسى البربري أنا المفضل بن غسان أنا على بن صالح أنا موسى بن عبد الله بن حسن عن إبراهيم بن عمر بن عبيدالله التيمي حدثني القاسم بن محمد قالت عائشة : جمع أبي الحديث عن رسول الله صلى الله عليه وسلم وكانت خمسمائة حديث فبات ليلته يتقلب كثيرا قالت : فغمني فقلت أتتقلب لشكوى أو لشيء بلغك؟ فلما أصبح قال : أي بنية هلمي الأحاديث التي عندك فجئته بها فدعا بنا فحرقها فقلت : لم أحرقتها؟ قال : خشيت أن أموت وهي عندي فيكون فيها أحاديث عن رجل قد ائتمنته ووثقت ولم يكن كما حدثني فأكون قد نقلت ذاك.

Wannan ASAR din Bai tabbata ba, saboda a cikin sanadinsa a Kwai wadanda a ke magana a kansu cewa suna da rauni, kamar محمد بن موسى البربري DA على بن صالح, in ka duba littafin ميزان الاعتدال للذهبي، DA littafin لسان الميزان لابن حجر العسقلاني zaka samu bayani a kansu.

Duk mai San karin bayani a Kan wannan الأثر din Ya duba wadannan littattafai :-

1- تذكرة الحفاظ للإمام الذهبي.
 2- كنز العمال في سنن الأقوال و الأفعال لعلاء الدين على بن حسام الدين الهندي.
 3- الأنوار الكاشفة لعبد الرحمن بن يحيى بن علي المعلمي اليماني.

Imamuz zahbi da ya kawo shi acikin تذكرة الحفاظ sai yace : فهذا لا يصح.

Amma saboda cin Amana ta karatu lokacin da DAN TA MORE ya kawo shi bayyi bayanin abun da Imamuz zahaby yace ba, kawai Sai yai shiru, idan da AKWAI amana ta karantarwa Sai yace الذهبي yace : Bai ingantaba, Amma Bai fadaba. 

A takaice wannan hadisin Bai tabbata ba balle a Gina hukunci a kai.

Saboda haka HADISAI sunanan masu yawa da suka tabbata daga ANNABI (S A W), Wanda suke bayanin Ayoyin da suka zo acikin Alqur'ani.

قال الله تعالى : (وأنزلنا إليك الذكر لتبين للناس ما نزل إليهم ولعلهم يتفكرون). سورة النحل

ALLAH (s w t) yace : mun saukarma da ALQUR'ANI Dan ka bayyana WA mutane abun da aka saukar musu (Ana samun bayanin ma anar ALQUR'ANI ta hanyar hadisi tabbatacce), Dan suyi tuntuntini.

يقول النبي صلى الله عليه وسلم : "ألا و إني أوتيت القرآن ومثله معه ".

ANNABI (S A W) yace : ku SAURARA Ambani ALQUR'ANI da misalinsa tare da shi.

BA za ka taba Raba ALQUR'ANI da hadisan Annabi (s a w) ba, in ana son yin Addinin musulunci in gantacce Sai an hada ALQUR'ANI da hadisi a wje daya, ba tare da an Raba suba.  

GA ABUN DA DAYA DAGA CIKIN MASU GABATAR DA HANKALI A KAN ABUBUWAN SHARIA HAR YAKE KOREWA ALLAH SIFFOFINSA YAKE FADA, NA YIN NADAMA DA BAKIN CIKIN YADDA YA KARAR DA RAYUWAR SA A KAN HAKA

نهاية إقدام العقول عقال # وغاية سعي العالمين ضلال.
وأرواحنا في وحشة من جسومنا # وحاصل دنيانا أذى ووبال
ولم نستفد من بحثنا طول عمرنا # سوى أن جمعنا فيه قيل و قالوا.

A KARSHE MUNA YIN NASIHA GA SAURAN AL UMMAR MUSULMI SU NISANCI DUK WANDA ZAIZO DA SUNAN KARANTARWA AMMA A KARSHE YA FAKE DA ZAGI DA CIN MUTUNCIN BAYIN ALLAH SUNE SAHABBAI DA SAURAN MALAMAN ADDININ MUSULUNCI, DUK WANDA KU KAGA HAKA A TARE DA SHI INA TABBATAR MUKU BABU ALHERI TARE DASHI SAI SHARRI.

ALLAH YA KIYAYE IMANINMU YA TABBATAR DAMU AKAN TAFARKI MADAIDAICI (SHINE TAFARKIN ALQUR'ANI DA SUNNAH KARQASHIN FAHIMTAR SAHABBAI) YA KARBI RAYUWARMU MUNA MASU IMANI

A HUTA LAFIYA

MAHMOUD SANI YUSUF ASSALAFY

23/09/1441 = 16/05/2020
Post a Comment (0)