AZUMIN MATAFIYI


AZUMIN MATAFIYI

Yanayin matafiyi dangane azumi uku ne:
1. Mutumin da idan yayi azumi a halin tafiya zai samu matsala ta bangaren lafiyar sa, wannan wajibi ya ajiye azumi, bayan sallah sai ya rama/ranka.
2. Mutumin da yin azumi a halin tafiya ba zai zama sababin cutar da lafiyar sa ba, amma zai sha wahala, abunda yafi ga irin wannan mutumin shine ya ajiye azumin, shima bayan sallah sai ya biya.
3. Mutumin da yin azumi 
a halin tafiya ba zai cutar da lafiyar sa ba, kuma ba zai sha wahala ba, wannan yana da zaɓi, in yaso yayi azumi, in yaso yasha. Amma yin azumi ga haƙƙin sa shi yafi, kasantuwar yana dama da ikon sauke wannan nauyi, haka kuma domin gaggawa wurin aikata wajibin dake kan sa.

Wadannan su ne takaitattun abubuwan da su ke rajihi game da mas'alar azumin matafiyi.

Allaah Ya datar da mu.

Abdullahi Almadeeniy Kagarko.
25/Ramadan/1441
18th May, 2020.
Post a Comment (0)