*FAHIMTAR SAHABBAI (MAGABATAN MU SALAF ) TA ZARCE FAHIMTAR DUKKAN AL UMMAH* !
_____________________________________________
_________________________________________
A cikin muhimmin littafin sa mai suna ﺍﻟﻄﺮﻕ ﺍﻟﺤﻜﻤﻴﺔ ﻓﻰ ﺍﻟﺴﻴﺎﺳﺔ ﺍﻟﺸﺮﻋﻴﺔ mujalladi 1 shafi 106 , lmām lbn Qayyīm al Jawziyyah (rahimahumāllāh) yazo mana da wasu jimloli wadanda ke nuna mana wājibcin riko da kuma fifita fahimtar Magabatan mu Salaf sama da fahimtar mu a cikin dukkan lamari na addīni da rayuwa.
Sai yake ce mana :
" ﺃﻓﻬﺎﻡ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻢ ﻓﻮﻕ ﺃﻓﻬﺎﻡ ﺟﻤﻴﻊ ﺍﻷﻣﺔ ﻭ ﻋﻠﻤﻬﻢ ﺑﻤﻘﺎﺻﺪ ﻧﺒﻴﻬﻢ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭ ﺳﻠﻢ ﻭ ﻗﻮﺍﻋﺪ ﺩﻳﻨﻪ ﻭ ﺷﺮﻋﻪ ، ﺃﺗﻢ ﻣﻦ ﻋﻠﻢ ﻛﻞ ﻣﻦ ﺟﺎﺀ ﺑﻌﺪﻫﻢ "
Ma'ana _______ " Fahimtar Sahabban Manzon Allāh (S) itace sama ga fahimtar dukkan wannan al Ummar. Hakanan ma ilimin dake gare su na sanin manufar Annbabin su (S) da sanin qā'idojin addīnin sa da Sharī'ar sa , sunfi cika (ta kamāla) fiye da ilimin wadanda suka zo bayan su " !
Wannan kamar yana kara fito da maganar al Qur'āni Mai Girma ce dangane da matsayin su Sahabban ne a cikin wannan al Ummar , inda Allāh Subhānahu wa Ta'ālā Yake cewa :
" ﻭﻣﻦ ﻳﺸﺎﻗﻖ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﻣﻦ ﺑﻌﺪ ﻣﺎ ﺗﺒﻴﻦ ﻟﻪ ﺍﻟﻬﺪﻯ ﻭﻳﺘﺒﻊ ﻏﻴﺮ ﺳﺒﻴﻞ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﻧﻮﻟﻪ ﻣﺎ ﺗﻮﻝ ﻭ ﻧﺼﻠﻪ ﺟﻬﻨﻢ ، ﻭﺳﺎﺀﺕ ﻣﺼﻴﺮﺍ "
Ma'ana ______ " Duk mutumin da ya sabawa Manzon Allāh bayan da shiriya ta bayyana a gare shi , sannan kuma sai yabi wata hanya wadda ba ta Mūminai ba , to zaMU kara dora shi bisa ga abinda ya zabarwa kansa ( na bata). Sannan a ranar tashin al Qiyāmah zaMU kona shi da wutar Jahannama , lallai ta munana a matsayin Makoma " !
Shiyasa akan wannan ne ma Shaikhul lslām lbn Taimiyyah (rahimahullāh) ya kawo maganar lmām as Shāfi'ī (rahimahullāh) a cikin litaffin sa ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ mujalladi 4 shafi 158 inda yake nuna fifikon ilimi da kuma fahimtar Sahabban Manzon Allāh (S) akan sauran al Ummah baki dayan ta.
Ga abinda yake cewa :
" ﻫﻢ ﻓﻮﻗﻨﺎ ﻓﻰ ﻛﻞ ﻋﻠﻢ ﻭ ﻋﻘﻞ ﻭ ﺩﻳﻦ ﻭ ﻓﻀﻞ ، ﻭﻛﻞ ﺳﺒﺐ ﻳﻨﺎﻝ ﺑﻪ ﻋﻠﻢ ﺃﻭ ﻳﺪﺭﻙ ﺑﻪ ﻫﺪﻯ . ﻭ ﺭﺃﻳﻬﻢ ﻟﻨﺎ ﺧﻴﺮ ﻣﻦ ﺭﺃﻳﻨﺎ ﻷﻧﻔﺴﻨﺎ
Ma'ana_______ " Suke sama akan mu a cikin dukkan ilimi da hankali da addīni da falala. Da kuma duk wata hanya wadda za'a iya samun ilimi daga gare ta ko kuma a iya riskar wata shiriya daga gare ta ( to sun fi mu dacewa da wannan hanyar) .
Hakanan ma ra'ayin su akan mu shi yafi zama alkhairi a gare mu fiye da ra'ayin mu akan kawunan mu " !
Kaji gaskiya , kuma kaji magana ta adalci da hangen nesa !
ABUBUWAN LURA A WANNAN DARASIN
_____________________________________________
_______________________________________
1______ Tafiya bisa fahimta da karantarwar Magabatan mu Salaf (Sahabban Manzon Allāh ) a cikin dukkan lamari na addīni da rayuwa wājibi akan dukkan musulmi _____ amma ba zabi ba ne !
2______ Bayyanar da gaba da kiyayya ga aqīdah da manhajin Magabatan mu Salaf (Sahabban Manzon Allāh S) alāmah ce ta kāfirci da munāfinci wadda zata iya shigar da mutum wutar Jahannama _______ kamar yanda al Qur'āni Mai Girma ya nuna.
Domin sune "Mūminan " da yake magana akai wadanda bayan mutum ya sabawa "Manzo " , sannan kuma sai ya saba masu _________ cewa mai yin wannan dan wutar Jahannama ne !
3______ Abinda duk Magabatan mu Salaf suka tafi akan sa na addīni , to shine addīni , shine kuma dai dai.
4______ Fahimtar da suka yiwa addīni , to itace fahimta sahihiya karbabbiya a Sharī'ah.
5______ ldan har manyan Magabata irin su lmām as Shāfi'ī (rahimahullāh) sun yi iqrāri da bakin su cewa ra'ayin Sahabban akan mu , shi yafi zama alkhairi fiye da ra'ayin mu akan kawunan mu , to ina gare mu mutanen yanzu ?
6______ Wannan yana kara tabbatar mana cewa da'awar SALAFIYYAH , watau da'awar Manzon Allāh (S) da Sahabban sa _______ itace kadai da'wah ma'sūmah wadda babu kuskure ko bata a cikin ta. Kuma ita ce haqiqanin musulunci tatacce wanda babu wata gurbata ko son zuciya a cikin sa.
7______ lta da'awar SALAFIYYAH ta gaskiya , babu ruwan ta da duk wata Kungiya ta addīni ko wace iri ce , domin ita dai ba Kungiya ba ce. A'a ita ce ma addīnin musulunci din baki dayan sa.
8______ Duk wata fahimta ko karantarwar da ta sabawa fahimta da karantarwar Magabatan mu Salaf , to wājibi ne akan dukkan musulmi yayi fatali da wannan fahimtar ko karantarwar.
Domin idan kuwa har ya doge akan wannan fahimtar tasa gurbatatta bayan da gaskiya ta bayyana a gare shi , to ko shakka babu cewa wannan mutumin ya zama batacce kuma dan bid'ah abin kaurace mawa , abun nisanta abun gudu !
9______ Babu lokacin da mutane suka fi tsananin bukatar aqīdah da fahimta (tare da ) karantarwar Magabatan mu Salaf (watau manhajin baki daya ) kamar a wannan lokacin da muke cikin sa.
Lokaci ne wanda yake cike da ra'ayoyi da aqidu fandararri na kāfirci da son zuciya wadanda matukar dai har mutum ya rayu kuma ya mutu akan su ( matukar dai har gaskiya ta bayyana a gare shi kuma ya fahimce ta amma yaki gyarawa ) , to lallai wannan yayi babbar asara ________ asara ta rayuwa ba ta dukiya ba !
Ubangiji Allāh Ya tsare mana īmānin mu Ya datar damu Ya kuma tabbatar damu akan wannan tafarkin mai albarka _______ tafarki ma'asūmi kubutacce daga dukkan aibi !
DAGA, MALAM MUHAMMAD KABIR HAIDARE.
📚📚📚📚📚📚📚📚📚📚📚📚
Ga masu bukatar shiga group
Email: jibwissocialmediaktlg@gmail.com
Facebook: Jibwis Katsina L.G
WhatsApp:
07062584992,
08038977817
0703074 7392,
07036879671,
08036958490
