*💎GWALAGWALEN KALMOMI ZUWA GA ƳAR UWATA MUSULMA 03💎*
Na farko: Zasu janye hankalinki ga barin abinda Allah ya halicceki ki akai na ki bauta masa. Suna amfani da ƙyaleƙyalen wannan duniyar: gwal, kuɗi, fashions (fitar tsiraici), da suka assasa a ƙasashen su, fito da sababbin abubuwa a koda yaushe (new models), yawan buri, yunwa wacce ba'a taɓa koshi da ita, tsere acikin rayuwa, da hanyoyi masu yawan gaske marasa ƙarewa na jin dadin duniya. Wanda Allah be halicce mu saboda hakan ba. Shiga cikin irin wannan harkokin ɓata lokaci ne da kudi, da sa sha'awar sai na fi wane a rayuwa.
Abu na biyu da suke amfani dashi shi ne: Suna halarta jinsin maza da mata, suna ganin cewa babu laifi ki gaisa da nimiji, ki rungume shi, ya sumbace ki, kiyi saurayi, ya ga tsiraicinki dss. A gurinsu wannan duk bakomai ba ne, sun dauki mace ba'a bakin komai ba, bata da kima balle wani mutunci a gurinsu! Suna cutar ku ta hanyar fakewa da su na nema muku 'yan ci.
Suna ikirarin cewa suna koyar da tarbiya alhalin rashin tarbiyya suke koyarwa, ta hanyar nunawa 'ya mace cewa tana da nata iko (right) akan kome, ta yiwa babanta rashin kunya, ta bar gidansu, ta bijirewa mijinta, ta yi yawo yadda take so, tayi abinda ta so da sunan (Right).
Wallahi ba kiranku suke zuwa ga adalci ba, ba kira su ke na a samu zaman lafiya da cigaba ba, ba 'yan ci suke nema muku ba, bakin ciki suke muku saboda sun ga Musulunci ya girmama ku ya baku 'yan ci mai girma. Suna Kira ne zuwa ga Zalunci, munafunci, tsana da rushe Alummar Musulmi.
*✍Rubutawa: Abdallah A Abdallah Abu Khadijat (أنصار السنة)*
15/05/1440.
21/01/2019.
Gabatarwa: *Abu Abdurrahman Ahmad Umar Rimi Assalafeey (Assalafeey Rimi)*
*- Zauren Macen Kwarai-*
*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a WhatsApp.*
