KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE 28TH FEBRUARY 2020


*KHUÆŠUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:*

04/RAJAB/1441-HJRY

28/FEBUARY/2020-MLDY

🎙️MAI GABATARWA Abubakar BN Mustafa Biu

♦️TOPIC {HUKUNCEN TA'AZIYYA} 

➖NA KASASHI GIDA 7
.
.
1️➖TA'ARIFIN TA'AZIYYA
TA'AZIYYA a luggance shine= lallashi ko Æ™arfafawa, 
TA'AZIYYA a shar'ance shine= umurni da yin haÆ™uri da juriya da tsoratarwa daga É—iban laifi don rashin haÆ™uri da adu'ar gafara ga mamaci da É—aure zuciyar wanda akayiwa rasuwan, 
.
.
2️➖HUKUNCIN TA'AZIYYA
◼️IBN TAIMIYYA yace= Mustahabbine yadda yake wurin TIRMIZY, [ALFATAWA] 
◼️NAWAWY yace= sunce Sunnace,
◼️Mustahabbine TA'AZIYYA ga dukkan dangin mamaci Æ™arami da babba, namiji da mace, [RAUDATUT ÆŠALIBEEN] 
.
.
3️➖Shin akwai ayyanannun lafuzzan TA'AZIYYA ne a SUNNA

 ANNABI SAW- yayinda jikarsa ke cikin magagi yaturawa mahaifitarta wannan kalmar (na ALLAH ne yabayar da abinda yakarba kowane abu da ajalinsa yi hakuri kinemi lada, 
◼️NAWAWY yace= wannan Hadisin shine mafi kyawun abinda za'ayi ta'aziyya dashi
◼️ALBANY yace= dukda yayi aanfani dashi ga wanda yakusa Mutuwa amma TA'AZIYYA dashi ga wanda yamutu shinema yafi dacewa, [AHKAMUL JANA'IZ]

Kuma ANNABI SAW a TA'AZIYYAR JA'AFAR R/A yayi amfani da kalmar (YA ALLAH kamaye gurbin Ja'afar a iyalansa.... sau 3, {AHMD & HKM}

Kuma ANNABI SAW cikin TA'AZIYYA wa UMMU SALAMAH yayi anfani da kalmar (ya ALLAH kagafartawa ABU SALAMAH kaÉ—aukaka darajarsa cikin shiryayyu kamaye gurbinsa cikin abinda yarage, kagafarta mana dashi YA RABBAL ALAMIN, kayalwata Æ™abarinsa kuma kahaskakashi) {MSLM} 

ANNABI SAW yayiwa wani TA'AZIYYA yace= (ALLAH yarahamceshi kaima yabaka lada) {IBN ABI SHAIBAH & BYHQ}
 
ANNABI SAW yaga tana kuka awurin Æ™abari sai yace (kiji tsoron ALLAH kiyi haÆ™uri) 
   Ba dole bane sai waÉ—annan lafuzan dukda su sukafi [AL-INSAF] 
◼️IMAM AHMD yayiwa wani TA'AZIYYA yace= mu da kai ALLAH bamu lada cikin wannan mutumin,
◼️kuma AHMD É—in ya amsawa wanida yayi masa TA'AZIYYA da cewa= ALLAH yakarbi adu'arka yayi mana rahama tareda kai, [MANARUS SABIL] 

SAMURA IBN JUNDUB yana faÉ—i a TA'AZIYYA (yi haÆ™uri da hukuncin UBANGIJINKA) 
.
.
4️➖FALALAR TA'AZIYYA DAGA ANNABI SAW

ANNABI SAW yace "duk wanda yayiwa É—an'uwansa Musulmi TA'AZIYYA ALLAH zai tufatar dashi da set na kwarran kayanda kowa ke marmarinsa a Æ™iyama, {ALBANY ya hassana} 
.
.
5️➖Shin yahalatta Musafaha yayin TA'AZIYYA 
◼️AHMD yace= ba'a karhantaba inkaso kayi inkason kabari, {IBN QUDAMAH} 
◼️ABDULWAHABUL WARRAQ ya karhanta◼️ABU HAFS ya karhanta a maÆ™abarta {IBN MUFLIH cikin AKFURU'I} 
.
.
6️➖HUKUNCIN TA'AZIYYA GA WANDA BA MUSULMIBA
◼️NAWAWY yace= ya halatta Musulmi yayiwa kafirin amana TA'AZIYYAR mutuwar Kafirin amana sai yace= <<ALLAH mayema gurbinsa kada yarage adadinka>> hikimar shine= don yawaita kuÉ—in jizya, (روضة الطالبين)
◼️IBN BAÆŠÆŠAH yace= ace <<ALLAH yabaka akan wannan musibar fiyayyen abinda yabawa ma'abuta addininka>> [ALMUGNI] 
◼️DAMYAÆŠY yace= Ja'izine Musulmi yayiwa kafiri TA'AZIYYA saidai bazaice ALLAH gafartawa mamacinkaba, don ALLAH baya gafartawa Kafiri, [إعانة الطالبين]
◼️NAWAWY yace= za'ayiwa Musulmi TA'AZIYYAR É—an uwansa kafiri da adu'a ga rayayyen, kuma za'ayiwa kafiri TA'AZIYYAR É—an'uwansa Musulmi da adu'a ga mamacin, [المجموع]
◼️MAWARDY yace= za'ayiwa musulmi TA'AZIYYAR mutuwar babansa kirista sai ace= ALLAH yagirmama ladanka kuma yamayema gurbi, [الحاوي الكبير]

7️➖SHIN YA HALATTANE DANGIN MAMACI SUYI ABINCIN CIYARDA MASU TA'AZIYYA
.
.
  Bai daceba don hakan ba sunna bane abinda SUNNA takarantar adafane akaiwa dangin mamaci ba su zasu dafa su bayarba, 

ANNABI SAW yafaɗa yayinda JA'AFAR yarasu "kuyiwa iyalan JA'AFAR abinci haƙiƙa abinda zai shagaltar dasu yazo musu" (Hadisin akwai matsala) amma hadisin AISHA R/A mai zuwa zai ƙarfafeshi
.
.
UMMUNA AISHA R/A- idan akayi mutuwa mutane suka watse sukabar ahlan mamaci kawai sai tadafa Talbeena da dambu sai tabawa waɗanda akayiwa mutuwan tace kuci domin ANNABI SAW yace "Talbeena tana danne zuciyar maras lafiya tana tafiyarda sashin baƙin ciki" {AHMD, BHR-5417, MSLM-2216, TRMZ-2039}
◼️DAMYAÆŠY yace= Mustahabbine maÆ™ota da bare suyi abincinda zai ishi ahlan mamaci dare da yini subasu kumasu matsa musu suci, 
◼️RAFI'E yace mustahabbine shiryawa ahlan mamaci abincin,[شرح الكبير]
◼️KAMAL ALHANAFY shima yafaÉ—i haka
◼️QARAFY ALMALIKY shima yafaÉ—i haka[الذخيرة]
◼️SHAUKANY yace TIRMIZY yafaÉ—i haka,[نيل الأوطار]
◼️Cikin [المبدع على شرح المقنع] yace= mustahabbine yin abinci abawa ahlan mamaci, amma idan ahlan mamacin su suka dafa da kansu suke bawa Mutane- Wasu Malamai sunce haramunne ◼️IMAN AHMD ya munana hakan Æ™warai◼️MIRWAZY yace hakan yada daga ayyukan Jahiliyya, 
.
.
ALLAH JIƘAN DUKKAN MAMATAN MUSULMAI YABAMU LAFIYA DA ZAMAN LAFIYA YARUGUZA DUKKAN 'YAN TA'ADDA ADUK INDA SUKE YATSARE AL'UMMAR MUSULMAI DAGA CUTAR CORONAVIRUS YASA MUCIKA DA IMANI
AMIN

_# Abubakar BN Mustafa Biu_

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Post a Comment (0)