HANKAKA DA KURTATTAKI


 
Hankaka Da Kurtattaki
Wata rana kurtattaki na koto a gonar wani bakauye, suna tone shukar da ya yi suna cinyewa, sai ga hankaka ya zo zai wuce. Ya ce musu, “Na hore ku da ku tone abin da manomin nan ke shukawa duka ku cinye.”

Sai suka tambaye shi me yake shukawa. Hankaka ya amsa musu, “Irin rama.”

Kurtattaki suka kada fiffike suna yi wa hankaka dariya, “Me za mu yi da irin rama ga dawa da gero.”

Kwanci tashi rama ta fito har ta girma. Manomi ya cire ta ya kware bawon ya yi zare. Da zaren rama ya tufka raga wadda ya kafa tarko cikin gonarsa, kurtattakin nan duka suka fada cikin tarkon. Suna cikin kici-kicin yadda za su yi su kubuta sai ga hankaka. Ya dube su ya ce, “Ashe ban gaya muku ku tone irin ramar nan ba tun kafin ya fito? Ga abin da nake yi muku gudu nan!”

Manomi ya kama kurtattaki ya kashe, da ma sun addabe shi da barna. Hankaka ya wuce yana cewa, “KU KAWAR DA MUGUN IRI, KO YA GIRMA YA KAWAR DA KU!”

 
Post a Comment (0)