Tatsuniyar Daskindaridi
Gata nan Gata nan Ku...
A wani gari da akwai wasu 'yan mata wanda suke zaune tare a gida daya. Da alkama, shinkafa, dawa, da kuma daddawa.
Sun tsani daddawa kamar me. Komai ba'a yi da ita. Sai watarana aka yi shela a gari cewa duk 'yan matan gari su hadu a wani fili za'a yi gasa. Ita wannan gasar za’a chanki sunan dan sarki ne! duk wanda ya chanka zai aure dan sarkin.
Su alkama, dawa, da suransu suke ta murna za'a tafi filin gasa. Ranar gasar ta zo duk 'yan matan suka ci kwaliyya banda daddawa saboda bata da abun sakawa! kuma sauran 'yan matan suna ta yi mata dariya.
Haka suka shirya suka tafi ba tare da daddawa ba. Abun tausayi daddawa ta saka 'yan kayanta wadanda take ji dasu ta kama hanyar filin gasa.
A hanya, sai 'yan matan nan suka hadu da wata tsohuwa tana wanka a rafi. Sai tsohuwar tace da Allah su taya ta wanke bayan ta sai yan matan suka ce lallai ma iya baki ganin na ci kwaliyya ki ce wani na wanke maki baya! sannu ma. Duk a cikin 'yan matan nan aka rasa me wanke wa tsohuwa baya!
Bayan 'yan matan sun wuce sai ga daddawa ta taho. 'Yar tsohuwa tace mata dan Allah 'yan mata wanke mun bayana. Daddawa tace to iya... tana cikin wanke wa 'yar tsohuwa baya sai kuwa bayan tsohuwa ya burme.
Daddawa ta rasa yadda zata yi! sai tace iya dan Allah yi hakuri bayanki ya burme. Tsohuwa tace me kika gani a ciki? tace wasu akwatuna guda biyu (babba da karami). Tsohuwa ta ce ta dauko karamin. Da ta bude akwatun sai taga kaya ne a ciki na alfarma. Tsohuwa tace mata ta saka kayan.
Daddawa ta saka kaya tayi kyau sosai. Sai tsohuwar ta tambayeta ko ta san sunan dan sarkin? sai tace aa... sai tsohuwa ta rada mata a kunnen ta sunan dan sarkin. Daddawa tayi godiya ta kama hanyar filin gasa.
A can kuma wajen gasar ana ta fafata da 'yan mata. Kowacce ta zo wajen dan sarkin sai ta gaya mashi sunan ta idan ya tambayeta sunan shi sai ta ce bata sani ba...shi kuma idan yaji haka sai yace koma da baya ki sha kuka...'yan mata sai kuka ake yi.
Ana cikin haka sai ga daddawa ta iso. 'Yan mata na ganinta sai aka fara zunden ta ana cewa ita kuma wannan daga ina? waya bata aron kaya? muma bamu san sunan shi ba bare ita? suna ta dai maganganu irin haka.
Ita dai daddawa bata ce komai ta karasa wajen rumfar da dan sarki yake.
Sai ndaddawa ta fara:
daddawa: “Assalaam salaam dan yaro, assalaam salaam”
dan sarki: “wacece nan take mana assalaam salaam”
daddawa: “daddawarka ce take maka assalaam salaam, me dadi a miya dan yaro, me dadi a miya”
dan sarki: “naji naki suna yarinya kawo nawa suna”
daddawa: “daskindaridi dan yaro, daskindaridi”
dan sarki: “bude ki shigo yarinya, bude ki shigo ki sha dadi.”
Daddawa ta bude labulen rumfar ta shiga ciki...sauran 'yan matan suna ta jin haushi suna mamakin yaya aka yi ma ta san sunan dan sarkin!!!
washe gari daddawa da daskindaridi suke yi auren su abin sha’awa.