JAN HANKALI GA MAZA MASU KIRAN MATANSU DA ƘANWATA


Jan hankali ga Maza masu kiran matansu da Qanwata.
Imamus Sa'idy Yace: Anqi mutum yakira matarshi da sunan matar data haramta agareshi, kamar yace " Ya uwata", " Ya yar uwata" da makamancin haka, domin yin hakan yana kama da haramci. ( ma'ana kamar kana haramta matarka ne akanka). 
Duba تيسر الكريم الرحمن
Ma'anar Zihari: 
Shaikh Fauzan Yace: 
Zihari ana nufin mutum ya cewa matarshi idan yana son yadaina jin dadi da ita ke kamar Uwata kike ko yar uwata ko wadda taharamta agareshi saboda dangantaka ko sanadin shayarwa ko surkuntaka, duk lokacin da ya kamanta matarshi da wadda taharamta agareshi koda wani sashen nata, to yayi mata zihari.
Duba:
الملخص الفقهي
Barka da shan ruwa
Post a Comment (0)