WACECE MACE BALLAGAZA MAI ARHA?


*_🧕 WACECE MACE BALLAGAZA (MAI ARHA)?! 🧕_*

بسم الله الرحمن الرحيم

_🧕 Wace Budurwa ce Ballagaza (mai arha)?! 🤔_

_🧕 *Mace ballagaza* itace Yarinyar da take Zaune a gidan Saurayinta take kwana bayan Sarauyin bai biya sadakinta ba, ba'a daura musu Aure ba, Danginta basu sani ba, amma kuma tana Zaune tare dashi 😕_

_🧕 *Budurwa ballagaza (Mai Arha)* itace Budurwar da take Saduwa (Zina) da Saurayinta, ta bada kanta, Ta bar Farjinta ya zama Condon shara kowa ya zuba Kazantarsa a ciki, Ko ta san su ko ba ta san su ba, babu Alkwarin Aure, babu wani Dalili babba, amma tana Zina da Samarinta saboda Kudin da take samu daga Gare su._ 

_🧕 *Mace Ballagaza (Mai Arha)* itace Budurwar da ta ke Tura hotunanta na Tsiraici ga Samarinta da sunan Soyayya._

_🧕 *Mace Ballagaza (mai Arha)* itace Yarinyar da ta ke Zubar da Ciki ba sau daya ba ba sau biyu ba, kuma take kan yi a koda yaushe, koda kuwa tana da Aure......_

_🧕 *Mace Ballagaza (Mai Arha)* itace Budurwar da take yin Shiga ta Fitar da Tsiraici da sunan Kwalliya, take bayyana surorin jikinta da gabbanta, Kana ganin komai nata, take Yawo akan Titi ko take yin Postings (yada) irin wadan nan Hotunan a Facebook, WhatsApp, instagram, Snap chart don ta sami likes 500 da comments 100 ana ce mata "Kai amma fa ke kyakkyawace" da makamantansu ita kuma tana yin Reply da "Nagode" 🙁_

_🧕 *Mace ballagaza (Mai Arha)* itace take alaka da Mazajen Aure, take Saduwa da su (Zina), take Zubar da ciki, ta amshi Kudin su, ta sa fitina acikin Aurensa ta lalata masa Aure don ta samu a Aure ta._

_🧕 *Mace ballagaza (Mai Arha)* itace wacce ta karanta wannan Rubutun sannan taji haushi ko ta Tsargu._

_🧕 Ku Tura wannan rubutu ga irin wadan nan matan masu Arha da sauqi 'Yan gwanjo a kasuwar mata, don su gani ko sa gyara._

_🧕 Mace Mai Tsada wacce tafi Gwal, Zinare, Azurfa, Dirhami, Dollar, Naira tsada itace Wacce *Ta Tsare Mutuncinta, ta Shige hijjabi da liqabi take boye kanta*_

03/04/1440
11/12/2018

Rubutawa:- Abdullah A Abdullah Abu Khadijat (أنصار السنة)*
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren *_📖MIFTAHUL ILMI📖_* (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren 🔑 _*MIFTAHUL ILMI*_🔑 a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)